Skip to content

Chapter 88

Chapter 88

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

ya zauna gefan ta shima, ita kuwa sai wani mar-mar take da idonta ita gata wanda miji ya kwana da ita. Sarki tsabar haushin Halisa bai sa ya kalle ta ba, ya kalli Balaraba da fuska a had'e yace"Tsayuwar me kuke min anan ko kema kina da abunda zakice a kan hakan" Gabanta ya fad'i jin abunda yace, Yo ita me zatace don ya kwanta da matarshi ta sunna kiji d'an neman rigima ita wacce tayi masa bai sauke fushin nasa a kanta ba sai ita da bata ji ba bata gani ba" Babu yabo babu fallasa ta d'an risina ta rage tsawon ta tace"Ina kwana fatan ka tashi lafiya"? Sai da ya gama ya mutse ya mutsen shi sannan ya amsa ciki-ciki. A zuciyarta tace"Dube shi don Allah wai mu zai nad'ewa tabarmar kunya da hauka. Juyawa tayi da niyar tafiya ya kalle ta a fakaice ya d'auke kansa ganin yadda mazaunan ta suke juyawa gwanin ban sha'awa"Jimana" Zuciyarta ta tsinke tasan da ita yake inda yayi mata wannan kiran tasan wata tsirfar ce. Juyowa tayi tana kallonsa yayi saurin d'auke kansa, yace"Ke je ki had'ama abun kari, ita wannan babu lafiya" yana nuna Azima da baki Wannan hukuncin da ya yanke yayi mata tsauri da yawa ita kam bata ga inda aka tab'a haka ba, wacce ta kwana da miji daban me kula dashi daban,, zuba abunci kawai za'ace baza ta iya ba, Ba tace komai ba ta nufi daining area cikin yanayin tafiyarta,dama abunda yake so kenan kallo ya bita dashi babu ko kunyar su Halisa da Azima da take fafar tana tare dashi hankalinsa da tunaninsa nacan gurin kallon rausayar Balaraba da tsarin jiki me kyau da Allah ya hore mata, duk namijin da ya d'ora idonsa a kanta sai ya kyasa balle kuma mace "yar uwarta. Halisa ta k'ara cika tayi fam-fam tamkar ta fashe da kuka haka take jin zuciyarta ita a ganinta ita aka takewa hakkin ta. Yana sane yak'i kallon gurin da take tsaye domin ba k'aramin haushi ta bashi ba da kan maganar da tafad'a. Jiki a sanyaye ta je ta zauna kusa da shi suka sashi a tsakiya, Azima cikin barikan ci da iya duniyan ci, ta mak'e murya irin me jin jikin nan, tace" Barka da safiya Uwargidan mu" Ko kallonta ba tayi ba,, hankalinta na kansa Wanda ya d'auke kansa tamkar bai san akwai ta a gurin ba, Murya a sanyaye tace"Ina magana fa ka share ni" Kallonta yayi yace"Ki je ki koyo yanda ake magana tunda ke kin ki kiyi hankali har yanzu" K'walla ta taro a idonta Lallai yau bata futo a sa'a ba komai a kanta ya k'are gara ma wacan wahalalliyar ita ya kula ta, cikin rashin abun yi tace"Ina kwana Kallonta yayi kamar yasa dariya domin ta bashi ita sosai, wai Ina kwana, fuskarshi ya kara had'ewa yana fad'in"Bazan amsa ba, sai kinje kin koyo yanda ake lafazi" Azima burinta ya cika jin yadda ake dizga Halisa sai wani lumshe ido take na jin dad'i. Halisa hakurin ta ya soma zuwa k'arshe da Jan ido ta kalle shi tana fad'in "Wai me yasa kake min haka hubby naga dai ni dakai auran soyayya mukayi ba auran had'i ba, kuma ba wani ne ya mutu akayi maka madadi da ni ba, kana sona ina sonka,to me yasa zaka dunga wulakanta ni a gaban Wanda basu isa ba" Kowa yayi zagi yasan da wanda yake,, Ba Azima ba har Balaraba sun gane habaici Halisa take musu" Shi ko Sarki! Kallonta yake gwanin ban haushi har da goge hawaye, shi kam bai ga abunda yayi mata ba da har take kuka idan laifi ne itace tayi,dole ne kuwa ya koya mata zamantakewa domin baya son rashin zaman lafiya a gidan shi. Yace"Kin shigo kina kallonmu d'ai-d'ai ke ga Gimbiya matar Sarki, ko? Bayan nan kin zo kina min wata maganar banza da bata da tushe balle makama, Eh na kwanta da Azima jiya kwanciya ya aure laifi ne, ke me ya hana ki kawo kanki tunda kina tak'amar da cewa kece Uwar gida wacce a ka fara d'aura min aure da ita" shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa"Bari ki abunda baki sani ba, Dan an d'aura maka aure da mata uku ko hudu a rana to bai addini bane kace Lallai sai da wacce aka fara d'aura maka aure sannan zakayi tara da ita ba, alhalin basu tare ba, ita ta kawo kanta gurina sai me ai itama matata CE,don haka ya rage naku yanzu Ku tsara yaya zaku raba kwana kamar yadda addini ya tanadar" Sosai Halisa take kuka taji zalin fad'an da yayi mata ahalin yanzu babu wata kalma da zata kara futowa daga bakinta bayan ya gama wulakanta gaban kishiyoyin ta. 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿100* Tashi tayi jikinta a mugun sanyaye ta nufi k'ofar futa daga falon, ko kallo bata ishe shi ba balle ya hanata tafiya. Balaraba ma cikin k'warin jiki tayi saurin had'a duk abun buk'ata kan daining d'in ta jera komai gwanin sha'awa, cikin nutsuwa ta baro gurin, kanta a k'asa ta tsaya nesa dasu tace"An kammala komai" Yana jinta sarai ya share tamkar bai ji ta ba,, d'ago kai tayi suka had'a ido, gaskiya ta tsani kallo wallahi ta lura kuma kamar d'abi'arshi ce,abunda Balaraba bata sani ba kuwa kallon kurulla ba hallin Sarki! Bane mutuk'ar ya damu Abu da kallo to tabbas abun yayi masa kuma ya k'yatar dashi,, Kishin Balaraba kamar ya kashe Azima domin ita ma ta lura da irin kallon da yake mata. Gyaran murya yayi k'asa-k'asa yace"Sauran ki d'akina ki hau ki gyara min, ita wannan bata da lafiya " Ya k'ara maimaita mata maganar da yayi mata akaro na farko. Farko yace mata ta had'a musu abunci yanzu kuma yace mata ta gyara masa d'aki wato yana nufin ta gyara inda suka b'ata ko yana so ya nuna mata Lallai yayi rayuwar aure da Azima ita a ganinta ba sai ya nuna mata komai ta gane sarai, b'ata fuska tayi kamar tace baza tayi ba, kuma sai ta tuno karamcin Fulani a gareta, kai tsaya ta juya da niyar hawa saman bene inda d'akunan baccin sa yake. Wannan kallon dai ya bita dashi, yana sauke wata sihirtacciyar ajiyar zuciya,, Azima ta d'ago kanta dake jikinsa tana kallonsa sai taga kwata-kwata ma hankalinsa baya kanta, bak'in ciki kamar tayi yaya, murya a sanyaye tace"Yallab'ai ya kamata muje kaci abunci zan wuce b'angaran da na sauka a kwai "yan uwanmu nacan na jira na da yawa daga cikinsu yau zasu tafi" Babu abunda yace mata, ya mike a tsanake ya nufi daining mik'ewa tayi da kuzari ba kamar d'azu ba ta bi bayansa Balaraba na shiga d'akin ta tadda bed d'in duk a hargitse duk nauyin bedshirt d'in dake shimfid'e a bed d'in ya hautsine da alama ba k'amin dirama aka sha jiya ba, wani mugun b'acin rai ne ya turnuk'o mata zuciyarta tamkar ta tarwarshe haka take jin wani matsananci kishinsa yana damunta, wai

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108