Chapter 75
Chapter 75
ki zuba musu ruwa, gawa ba a zuba mata ruwa" Ihu! Kulu ta kurma ta mik'e tsaye a zabure! tace"Au! Ashe da gaske sun mutu? Wayyo na shiga uku na lalace ni Hauwa Kulu" Waziri ya tsuguna yana duba gawar su Fiddausi cikin zuciyarsa yana tunanin shi kuma a cikin "yayansa ko suwa Aljani Mak'asudu zai tsotsewa jini oho. Ihu kawai kake ji a b'angaran Hajiya Kulu babu me salati a cikin mutanan ta, lokacin k'ank'ani mutuwar su Fiddausi ta watsu a gidan, Ihun da Hajiya Kulu take ne ya b'atawa Sarki! rai kawai sai ya fuce daga shashan cike da b'akin ciki da damuwa. Wannan al'amari ya tayarwa da kowa hankali, Mussaman Sarki!, Cike da damuwa a kai wa su Fiddausi suttura aka kaisu makwancin su, bayan an dawo daga makabarta Waziri ya shige fada ya zauna kan kujera tare da jama'rshi,, kafin kace kwabo "yan zaman makoki suka fara gulma,har da masu zuwa inda Sarki! Yake zaune suna fad'a masa ga Waziri can a fada bayan kuma Governor yace" Kujerar ta shi ce. Sarki! Yace"Suyi hakuri su kyaleshi tukkuna a kwana biyu komai zai dai-dai ta, dama shi Galadima baya goyan bayan Waziri shiyasa basa shiri sosai, yanzu ma yana kusa da Sarki! Suna karb'ar gaisuwa. Bayan sadakar uku Hajiya Kulu Duniya sabuwa saboda a yanzu kud'i baya yanke mata motsi kad'an zata sa a kira mata Sarki! Tace zata ciri kud'i dole ya bata, ko yak'i ko ya so, watarana in ta umarshi da yayi Abu baya sab'awa umarnin ta,, Mama Fulani kuwa duk dan a zauna lafiya take k'ara tursasahi idan ya bujirewa bukatar Kulu wataran. ******* Sati biyu da rasuwar su Fiddausi, su Latifa da Iklas sauran "yan matan dake gaban Kulu kenan,suka fara rigimar dole a raba musu gado suna so su fara kasuwanci,nan Hajiya Kulu tasa ai mata kiran Sarki! kan buk'atar " yayanta. Bayan Sarki! Ya gama sauraron maganganun Hajiya Kulu kan rabon gado,sai yace mata ta kwantar da hankalin ta insha Allah za'a raba a cikin satin nan, yayi mata sallama ya tafi, yarasa me yasa idan yana gabanta baya iyayin katab'us. Limamai da shedu ya Tara kan rabon gadon akayi shi cikin adalci inda Sarki! Ya tashi da kusan rabin dukiyar me Martaba had'e da kadarorinsa, a matsayinsa na Namiji matan ma aka basu abunda Allah ya sharanta,, bak'in ciki kamar ya kashe Hajiya Kulu dan haka a daran ranar ta nufi gurin Tsito domin ta nemi shawarar yaya za'ayi. Tana zuwa Tsito ya bushe da dariya yana fad'in dama nasan kina tafe ai" Kulu ta zauna tana sauke nuffashi tace"Dole inzo gurinka domin ka had'ani da Mak'asudu yanzu anyi rabon gado komai yaron nan ya kwashe mu mun tashi a tutar babu" Tsito ya kece da wata mahaukaciyar dariya yana fad'in gaskiya Hajiya kina dan son kud'i sosai, Mak'asudu na jin ki kuma yanzu zan had'aki dashi" Ai kuwa Kulu ta gyara zamanta Mak'asudu ya hauro ya fara magana kamar haka" Kinzo kan wannan yaron Wanda ya tsaya miki a zuciya ko"? Kulu ta d'aga kai, yace"Kije kawai zaki samu yanda kike so akansa ko yau kuka karar da dukiyarku, daga zarar kin tambaye shi kud'i zai baki jikinsa na rawa" Kulu ta dunga godiya sosai Aljani Mak'asudu yace"Ki kawo min k'wai d'anye goma sha d'aya yanzu zan sha" Kulu ta mik'e da niyar tafiya tana fad'in "Yawwa yanzu kuwa zan aiko Ladi dashi, godiya nake Ubana" ****** Ina labarin su Shamsiyya ne? Satin Shamsiyya d'aya a gurin Arrama kullum ta Allah zai bata wannan rubutu yace ta shafa jikinta, sai yaga ta b'ingire yazo ya kwashi gara, ya wani murmure saboda yana samun biyan buk'ata yadda ya kamata yanzu tunaninsa yaya za'ayi ya kafe Shamsiyya s gidan,Ku kuma ta dunga kawo kanta gurinsa dole sai yayi aiki a kanta. Shamsiyya duk ta rame ta figale sai uban nonowa da suka cika k'irji ta futo daga k'aramin d'akin cikin shirin tafiya tunda dama tun daran jiya yace aiki ya fara ci, saboda haka zai sallame ta amma ta dunga zuwa lokaci zuwa lokaci domin a dunga dubawa. Godiya sosai take masa, yace"Kinanan zaune zai zo gurinki yace ke yake son aura ba waccan ba" Cikin rashin dabara da wayo Shamsiyya taita zabga godiya tayi masa sallama ta tafi, tana cike da farin ciki ganin bukatat ta takusa biya ******* Lantana ce ta tafi mak'abarta da kanta Ta samo k'asar sabon kabari ta kawo aka had'a maganin kamar yadda Arrama ya bada umarni, suna sauraron dawowar Shamsiyya Shamsiyya ta dawo gida cike da farin ciki da annushuwa domin ta gazgata maganar Arrama gani take kamar ta auri Sarki! ta gama, Uwa! Taga duk ta rame ba kamar ranar da suka tafi ba, amma labarin da Shamsiyya ta bata na samun nasara yasa bata wani damu ba, suka cigaba da kulla yadda al'amarin zai kasance. Sun yanke shawarar cewar Lantana ce zataje can gidan me Martaba domin ta gabatar da aikin nata,, Shamsiyya tace" Ai naji dad'in mutuwar me Martab wallahi ko babu komai zan sake kuma ina sa ran zan auri Sarki! Domin na san d'anshi ne zai gaje shi" "Bari ke dai " yar nan, ai bake kad'ai ce kikayi farin ciki ba har damu mun kusa hutawa dai da talauci mutukar kika auri Sarki! Ai kakarmu ta yanke sak'a" Shamsiyya ta washe baki cike da farin ciki tace"Lantana ke zan fara kaiwa aikin hajji,domin ina ganin in bata dalilina ba,har ki mutu baza kije maka ba" Lantana tace"Aikuwa dai ni kaina nakan fad'i haka,wallahi wannan bak'in talaucin namu ya ishe ni" Dariya Shamsiyya tasa,, tana fad'in wai ina Babanmu ne"? Tab'e baki Uwa! Tayi tace"Gashi can a kwance yau da lafiya gobe babu, sai kace me cutar farfad'iya kullum fad'uwa miyau na zuba" Shamsiyya ta lek'a d'akin da Sallau yake kwance ta ganshi kan tabarma ko fulo babu,miyau sai dulala yake. Yana ganin ta ya d'ago mata hannu wai tazo,Shamsiyya ta mak'e kafad'a tana fad'in "Wallahi bazan zo ba Tabb! Ji wani zarni da d'akin yake,aini yau bazan kwana a d'akin nan ba, d'akin Wacan shegiyar zan bud'e in shiga in kwanciya ta" Uwa!tace"Yo ba dole kiji zarni ba idan iskancin sa ya tashi nan yake sakar min futsari ke har guntin kashi sai ki gani a jikin wandonsa sai kace wani k'aramin yaro,duk yabi ya sakwarkwace aikin banza kawai" Dariya sosai Shamsiyya take harda hawaye tana fad'in Lallai ba, tsufan ka da kallo tabdijam harka fara kashi da futsari aiko zan hayo masu jinya, domin ni bazan yi aikin kashi ba" Uwa! Taja tsaki tana watsawa Sallau harara yana cikin daki yana kallon ta yana kuma jin duk abunda suke cewa bakin ciki kamar ya kashe shi,Uwa! Ta cigaba da cewa"Ai na kunshi takaici wallahi. da kike ji daga ni ko a gado wancan uban naku babu abunda yake iya tsinana min sai dai inyi kid'ana inyi rawa ta, solob'iyo kawai,, in banda shan taba babu abunda yasa a gaba" Cikin dariya Shamsiyya tace"Tab!! Uwa! A lokacin ki kin tsula tsiyar ki. yarda kike so,ai daga ni babu sauk'i waiiii'' Uwa tayi shewa tana fad'in "Ke rabu dani dan ubanki, ko yanzu garau nake ji na,zan iya da d'an shekara goma sha bakwai ma" Shamsiyya ta zare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108