Skip to content

Chapter 50

Chapter 50

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,241 words 0 views Progress saved
Download Book

lallai Moddibo yarinyar nan zata zautaka, sai me in anyi mata aure,? dama can Allah ya nufa ba matar ka bace" Cikin damuwa da b'acin rai Moddibo yace" ba nafad'a maka damuwa ta bane domin ka b'ata min rai ba, na fad'a maka ne domin ka nema min mafuta" "Ok toum yanzu me zanyi maka, dama ni bana son ka aureta sabuda haka babu wani mafuta da zan nema maka" A nutse Moddibo ya juyo yana kallonsa yace"alfarma d'aya nake nema a gurin shine ka amunce min in kawo Balaraba shashen ka in b'oyeta kafin ka gama bunkice a kanta, dan girman Allah kaga daga mungama bunkice a kanta sai muje mu samu me Martaba mu fad'a masa halin da ake ciki,amma yanzu in muka bari a ka daura mata aure rayuwarta tana cikin ha tsari, nima zaku iya rasani, domin zuciyata zata iya mutuwa" *Comment Vote and Share* [23/07, 16:23] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿58* Cikin mamaki yace"ban fahimci abunda kake nufi ba, kana nufin ka kawo min ita shashena ka aje, min kan wane dalili zaka had'ani da mace baliga irin wannan" Cikin kwantar da kai Moddibo yace" ai a k'asa zata zauna, kai kana sama, duk abunda kake buk'ata da a kwai a saman ka,nasan in ba neman magana ba babu abunda zai sakko da kai k'asa" "Shikkenan sabuda buk'atar ka sai in dai na zaman farlo sabuda ka aje " yar gwal,sai in takure kaina,kasan abunda bazai yi hu bane" Ya k'arashe maganar yana masa wani kallo a d'age! "Shikkenan to ka bata aron d'aki a saman mai d'auke da toilet, ni zan dinga kawo mata abunci,da komai na buk'ata,banaso ma ta futo balle masu yi maka hidima su ganta su zargi wani abun" Ganin yadda Moddibo ya wani sukurkuce yasa yace"shikkenan" sakin fuska Moddibo yayi yace"nagode d'an uwana,na baka amanar ta ka kula min da ita don Allah" Cikin shank'amshi yace"ban karb'i amana ba, gaskiya ga guri nan da ta zauna" "Shikkenan hakama nagode" Moddibo ya fad'a cikin farin ciki, ya cigaba da cewa yanzu, in mun dawo me zai hana mu tsaya a gidan nasu ko"? Girgiza kai yayi kawai yayi shiru, hakan ya nunawa Moddibo bai yadda ba, shiru yayi bai sake maganar ba yana jin tsoron kar ya botsare masa, yasan halin kayansa. **** Sai bayan sallahr la'asar suka dawo gida, Moddibo ko zama baiyi ba, ya k'ara futa shi kad'ai a mota, Balaraba suna zaune ita da Bushira suna jiran zuwan Moddibo domin yayi mata waya yace gashi nan kan hanya, "yan kayanta ta had'a a k'aramar a kwatu, ta had'a nasu Sadiya da Usuman tanayi tana kukan bakin ciki da halin damuwar da take ciki, Bushira sai tausar zuciyarta take, Lantana ce yi sallama ta shigo d'akin tayi musu wani irin kallo,na raini da wulak'anci tace" Au kuka kikeyi, dan mugun hali, in ceko "yan gulma sun fad'a miki d'aurin auran ki da d'an uwanki ne,shine kike koke-koke banza,to ko kukan jini zakiyi sai dai kiyi munafuka kawai,ai da wannan lalatar da kike gwara ayi miki aure kar ki jawo mana abun kunya a gari" Haka Lantana ta k'araci zage-zagenta ta futa, basu ce mata komai ba, suna jiyo shewarsu Uwa da "yayanta a tsakar gida, sai zaginta suke, Iro ne ya shigo shima ya zauna anayi dashi, Wayarta ce tayi k'ara Moddibo ne, ta d'aga wayar gami da karata a kunne, cikin sanyin murya tace" Yusuf, ka zo ne"? "Eh ina cikin unguwarku, na bari ay sallahr Magariba duhu yayi sai in zo" "Yawwa dama abunda nakeso ince kenan" tafad'a tana kokarin kashewar jin alamun za'a shigo d'akin, Iro ne ya shigo yana wani lasar baki, idonshi tar! a kan Balaraba, yace"amaryata ya akai ne"? K'okarin tsallake Bushira yake yi yaje kusa da Balaraba yw zauna, Bushira tayi saurin janye k'afarta hakan yasa ya fad'i k'asa kamar wani soko, dama ga jiki babu k'wari ya mik'e yana layi yace"ke tashi ki futa zani magana da amarya ta"Wari ne ya cika d'akin na tsamin hamta da warin ganye, zuciayarta taji tana wani irin tashi, Balaraba kuwa tuni ta toshe hancin ta, Bushira tace"kai in banda abunka Iro ai kamata yayi kai da zakazo gurin amaryar ka kaci kwalliya kazo kana k'amshi, ba wari ba, yanzu abunda za'ayi kaje kayi wanka kasa kaya masu kyau ka fesa turare in kanaso amaryar taka ta saurareka, jin abunda Bushira tace, yasa ya washe baki yana kallonta yace"kina nufin ta yanzu ta amunce dani"? "Sosai kuwa" Balaraba tanai masa murmushi kamar gaske Futa yayi daga d'akin yana fad'in yanzu zanje kuwa in shek'awa amaryata kwalliya" Yana futa suka fara dariya kasa-kasa Bushira tace"wannan ya kasance a mijinka ai ka shiga uku da wari da tsamin hammata" Cikin takaici da damuwa Balaraba tace"rabu da shashasha mahaukaci kawai" Dariya kawai Bushira take mata. Sai bayan sallahr isha'i sannan Moddibo yazo, yana zaune cikin mota yana tunani,sai yaga gilmawar Walidi, ya sauke glass d'in mota yana kiransa, dawowa Walidi yayi ya tsaya, ganin fuskar Moddibo yasa ya washe baki yace"yallabai barka da zuwa" "Barka kadai abokina" Moddibo ya fad'a ya cigaba da cewa" kaje ka kiramin Gimbiya" Da sauri Walidi ya tafi, lokacin duk sun watse a tsakar gidan babu kowa, sabuda haka da sauri ya shiga d'akin Balaraba tace"yawwa dama kai nake nema d'auki wannan a kwatun ka futa dashi, zakaga wani mutum da mota a bakin lungu" Walidi yace"ai shine ya aiko ni ma yanzu" "Ok yi sauri ka kai masa" hannu biyu yasa ya d'auka ya futa da sauri,su kuma suka mik'e suna yafa mayafansu, Bushira ta rik'e hannun Sadiya, Balaraba ta rik'e hannun Usuman a haka suka futa daga gidan, lokacin babu mutane sosai a waje, sai yara k'ananu, sabuda haka basu fuskanci komai ba, nan Walidi ya bud'e bayan motar ya zura jakar ya mayar ya rufe ya tsaya yana hangowar zuwansu Balaraba, Moddibo yana ganin tawowar su ya bude mata kofa, su Sadiya tafara sakawa, ta tsaya suna sallama da Bushira Moddibo ya zuro kanshi suna gaisawa da Bushira, kud'i ya ciro wanda bai san adadinsu ba, ya mik'a mata, ya k'ara ciro wasu ya mik'awa Walidi dake ta washe baki, yace "ina neman alfarma a gareku da ku rufe wannan abu a tsakanin mu, in kukayi haka kunyi jahadi,bayan komai ya lafa zan muku kyauta ta mussaman" Bushira tace"Babu komai Yallab'ai" Godiya yayi musu ya kunna motar cikin sauri yaja motar, su kuma suka bar gurin cikin mamaki kyautar kud'in da yayi musu. Shiru cikin motar babu wanda yace komai sai da suka hau titi sosai sannan Moddibo ya juyo fuskarasa d'auke da murmushi yace"Gimbiya wannan ce Sadiyar"? A hankali tace"Eh" "Kai masha Allah kuna kama da ita amma ba sosai ba" Murmushi tayi kad'an da damuwa a fuskarta tace"Yusuf ina ka shirya a jeni ne"? Fuskarshi ya gyara yana kallonta ta cikin mudubin motar,yace"gidan mu mana amma kina keb'antaccan guri,wanda babu wanda zai san dake a gurin" Ajiyar zuciya ta sauke hankalinta ya kwanta tace" nagode Yusuf Allah ya kara mana so da k'auna" "Ameen gimbiya ta" yafad'a yana kallon Usuman dake

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108