Chapter 14
Chapter 14
kai in ci da "yayanka" Bai ce mata komai ba ,ya fizge rigarshi gami da gyara wuyanta in da ta yaga masa,ya sakai ya fice daga gidan babu abinda ya dameshi,can mahadarsu ya nufa,abokanshi na Zane suna ta faman karta! (Caca) nan ya zauna cikinsu a ka fara yi dashi. _ina so Ku fahimci ko wane marubuci da nasa salon,gaskiya ni babu yadda za'ayi in yi rubutu batare da na fadi jogon labari ba ,domin shine ginshin fara karatu, So dan Allah kuyi hakuri kuci gaba da bina a yadda nake za azo in da kuke so_ *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* [04/05, 03:17] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? 🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀ *🐾GIMBIYA BALARABA*🐾 🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀ *By* _BINTA UMAR_ *Maman Abdul Wahabu* _ZAMANI WRITES ASSOCIATION_ *🅿23* _Bissimillahi_ To haka rayuwa take, Ayuba ya yi ta fafutukar naman abinda zai rufawa kanshi,asiri ,yayin da "yan uwanshi suka tasa shi a gaba har sai dai suka ga ya kwanta, ba ya iyayin komai da kanshi sai dai ayi masa,gashi lokacin nauyi yayi masa yawa dalili kuwa yayarshi Atika mijinta ya rasu,sai ta dawo gidan ta zauna dakinsu na gado ita da "yan uwanta ,da suke can garinsu ,suna aure,a lokacin Balaraba na da shekara goma sha uku, sai kanwar ta ,wato sadiya, tana da shekara tara,sai qaramin kaninsu Usuman dan shekara bakwai. Sosai Ayuba yake ciwo an rasa gane kan ciwon anyi na asibitin har an hakura ,sai aka dawo yin na hausa,sabida yadda kafarsa guda ta kumbura take fitar da ruwa abin babu dadi , wani mai maganin hausa da yazo ya dubashi ,yace jifansa a kai (Asiri) sabida haka kar a kara yin maganin asibiti domin zai kara rikita ciwon,cikin ikon Allah ya hada magani ya bashi nasha da wanka gami da shafawa, a kafar,sai a ka fara samun saukin abun, domin wani lokacin yakan tashi da kan shi yafito waje yana dafa bango, Tunda yafara wannan ciwon tsakanin Sallau da Lantana da Uwa babu wanda yazo ya duba shi ballan tana yace dashi sannu ,gwara Mamman shi yazo dalilin tursasawar matarshi Halimatu, Lantana tace yadda uwarka ta tafi tabarka haka kai ma zaka tafi kabar naka "yayan gyyar tsiya arna a idi, kullum in zata fita yawon tallanta sai ta tsaya a tsakar gida tayi surutai ,sannan take tafiya ,tana fatan Allah yasa kafin ta dawo ta tarar ya mutu kowa ya huta Allah mai yadda yaso a sanda yaso ,an kwanta da Ayuba lafiya daran alamis ,domin kafin yayi bacci ma sun dade da matarshi da yayarshi Atika ,gami da "yayanshi suna hira,ashe ta bankwana ce, da asubah Hafsatu ta rika tashin sa taji shiru ,sabida ta saba duk asubar fari shi yake riga kowa tashi a gidan,shiyasa ta gigice ta fice daga dakin da sauri,tayi dakin Iya Atika,ta daga labulen ta ce"Iya fito kiga babansu Sadiya yaki tashi, Da sauri Iya ta mike daga kan dadduma ta fito tana salati a zuciyar ta domin dama jikinta ya bata ,tunda ta kwanta take munanan mafarkai, Ta shiga dakin gami da zama kusa da qanin nata ,tana kallon yadda idon shi suka kakkafe tasan lallai Ayuba ya amsa kiran Ubangiji, salati take tana sallallami ,Hafsatu tace "Iya ya mutu ko"? Iya Atika tarasa mai zata ce mata sai kawai ta kama hanya zata fita daga dakin tana sharar hawaye, Kafin ta daga labule,taji abu ya fadi, rigif!! wanda yayi dai-dai da farkawar *Balaraba* daga bacci a furgice! Iya ta dawo dakin da sauri tana Salati ganin yadda Hafsatu tafadi kan Ayuba dake kwance, Tana daga ta taga ta kwanta yaraf! alamun babu rai! a jikinta, *INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN* Abinda Iya tafada kenan, Balaraba ta mike tsaye a zabure tana kallon iyayen ta biyu a kwance ,dukkaninsu babu rai! tace"Iya mai nene Iya kar kice min babana ya mutu,! Iya ki tashi Umma na kin ga tafadi, a kasa, sai ta fita waje da gudu bata saurari abinda Iya take fada mata ba, *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* 08089965176 [04/05, 03:17] +234 808 996 5176: 🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀ *GIMBIYA BALARABA* 🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀🧝🏻♀ *By* _BINTA UMAR_ *MAMAN ABDUL WAHABU* _BISIMILLAHIR RAHAMANIR-RAHIM_ *Page* *24* Lantana dake tsugune bakin rijiya tana daura alwala,ta juyo da sauri ganin Balaraba ta fito da gudu daga dakinsu tana ihu,sai ta mike tsaye gami da sakin botar hannuta,tace"ke Balaraba kina hauka ne,dan ubanki ko Ayuba ne ya mutu abinda zakiyi kenan,shashasha mara hankal.... Kafin Lantana ta karasa maganar ,Iya ta tare ta ,da cewar "to ai zan ce ya kare Ayuba da Hafsatu ,sun koma ga Allah,wanda yake ganin zai zauna jiran duniyar gashinan ga tanan. Lantana ta zabura ,cikin rawar jiki tace "me kika ce Atika, kina nufin Ayuba ya mutu"? Iya tafashe da kukan da yake cin zuciyarta tun dazu,tace "ai ba'a wasa da mutuwa Lantana ,leqa ki gani, Jikinta na rawa ta nufi dakinsu Ayuba, Ai kuwa abinda ta gani ya daga mata hankali sosai ,babu Ayuba babu Hafsatu, Lantana ta furgita sosai ,sai ta fito da sauri,ta fasa wani ihu! da ya ta da mutan gidan gaba dayansu har da makota, Kankace kwabo gida ya cika da jama'a ana ta kokawa da wannan mutuwar mai abin mamaki. Balaraba kuwa ta dai na kuka sai dai na zuci idanun ta sunyi mici mici kallon kowa kawai take,takama kanne ta da ke kuka ta rungume itama tana kukan zucci. Uwa da Lantana kai har da Sallau , mutuwar nan ta gigitasu ta firgitasu,sosai jikinsu yayi sanyi,amma abin mamaki ana yin sadaqar uku ,shikkenan ,suka watsar,mussaman ,yanda suka ga irin mutanan Ayuba ,suna kawo taimako, sai Sallau yayi uwa yayi makarbiya yace"ai shine wakilin yaran, sai Iya tayi da gaske sannan yake barinta ta karbi sadakar,komai idonshi na kai,ita ko Balaraba ,in an bata ,sai ta mikawa Iya,Ashe Sallau duk yana lura,sai yaga babu idon Iya sai yayi ta zuga Balaraba wai ta karbi kudin ta tabashi ,ya aje mata sabida in tazo yin aure shi zai yi Mata kayan gado, Kwata kwata Balaraba bata sauraronshi,sabida tasan ko ta bashi kudin zuwa zai yi yayi caca dasu kamar yadda yayi ,da wa"yanda ya karba ,yamma nayi ya lura,an dai na zuwa sai ya yayi tafiyarshi,mahadarsu,ta "yan caca Rayuwa kenan Balaraba ,ita ce tazama uwa da uban Sadiya da Usuman ,tun bayan rasuwar iyayensu,ita ce cinsu ita ce shansu, kudin makarantarsu,da nata, Bayan rasuwar iyayensu da kwana arba'in ,Balaraba ta hada "yan kudin da suka samu ita da "yan uwanta, ta shiga kasuwa ,ta siyo kuloli da farantai ,hade da manyan tukwane, tazo ta dira abincin siyarwa, a lokacin shekarun ta basu wuce sha shida ba, dake yarinya ce mai girman jiki ,shiyasa in ka kalle ta zakayi tunanin ta zarta haka, Balaraba tana da kyau sosai ,tana da diri na jiki, fara ce tas! Dan idan tayi kwalliya ta fita baza ka taba cewa a wannan gidan take rayuwa ba,tana da kirki sosai abin ta bai rufe mata ido ba domin ko abinci tayi kafin ta fita dashi duk wanda ya kwana ya tashi a gidan takan zuba masa ,sannan yaran da suke fitar mata dashi su dauka a kura, su kai mata bakin kasuwar,(sha tambaya) anan take siyar da abincin ta,wanda da an fita dashi yake karewa,wani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108