Skip to content

Chapter 39

Chapter 39

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
Download Book

yana mata wani kallon irin na sha'awa hannu ya sanya ya fuzge mata mayafin ya jefar k'asa, a gigice ya kai hannusa jikinta, inda ita kuma Allah ya bata sa'a tayi nasarar fuzgo wata k'aramar wuk'a dake soke a k'ugunshi, hannushi ta daka! da ita cikin zafin nama! nan take Iro ya zube a gurin jini na futa a hannunshi sosai da sosai, saura kad'an d'an ya tsan shi k'arami ya guntule, ihu! yake kurmawa, wanda yasa mutanan Cikin gidan futowa da gudu suka nufi inda suke jiyo Ihun! Da Sauri Walidi ya bud'e k'ofar soran dalili shima yaji ihun, dama dawowar shi kenan,ya tsaya yana raba wasu yara fad'a wanda suka zo siyan a wara, Ihu! Iri yake sosai kamar wani k'aramin Yaro, ga Balaraba a tsaye, babu mayafi babu d'ankwali, ga hannunta rik'e da wuk'a Da yake a kwai sauran haske a garin bai duhu ba, yasa kowa ya fahimci abunda yake faruwa, Uwa! ce ta kurma wani uban ihu! gami da d'ora hannu a ka tana fad'in na shiga uku! na Lalace, ni Uwande! shikkenan zata kashe min yaro na wanda nake hutawa dashi, wallahi Balaraba sai na d'auki fansa a kanki" Kafin kowa ya ankara tayi kan Balaraba da gudu ta danne ta tana duka ko ita, da yake Uwa! irin matan nan ne masu k'iba, kowa ya kasa daga ta daga kan Balaraba sai duka take, Lantana ko tana gefe d'aya tana k'ara ingiza Uwa!,kan taci uban Balaraba, a cewar ta abunda Balaraba takeyi musu samun guri ne, A fusace!Walidi yayi kan mahaifiyar tasa wacce take k'okarin kwatar k'aramar wuk'ar dake hannun Balaraba wai lallai sai ta cire mata ya tsa kamar yadda tayi wa iro, Cikin tsawa! yace"Wallahi Uwa! in baki d'agata kin daina dukanta ba sai nayi miki aski da wannan askar dake, hannuna, kin san dai zan iya, ko, dan tsabar mugunta da kawai ki danne ta, kina duka, kamar baki san halin d'an iskan d'anki ba, saunawa nake kamashi ke kanki yana lek'a ki a band'aki in kina wanka, wallahi naji dad'in abunda Gimbiya tayi masa, shege dan iska" Ya karasa maganar yana dukan k'afar iro wanda yake kwance a k'asa rik'e da dan ya tsa yana jale-jale sura kad'an ya cire, amma sabuda tsabar son mata, yana can yana kallon jikin Balaraba, wanda Uwa! ta tattare mata zani, duk rabin cinyoyin ta a waje, ji yake kamar ya shafa jikin ko yaji sauk'in Sha'awar dake damunshi Ganin Walidi yana masifa yasa Lantana tayi k'us! da bakin ta, sabuda tana k'ula fucin d'ari biyun da yace zai bata gobe da safe, tasan tayi magana zai iya hana ta, Itama Uwa! mikewa tayi daga kan Balaraba, tana wani irin huci! sai zaginta take ta Uwa ta Uba, tana nema mata bala'i gami da jafa'i, Abunda yasa ta daina dukan Balaraba shine tasan tsaf! Walidi zai aikata abunda yace, shiyas ta d'agata badan ta hak'ura ba, Cikin borin kunya Iro ya mike tsaye yana nuna Walidi dan ya tsa yace"ban tab'a sanin kai shege bane sai yau, ina matsayin d'an uwanka, wannan tayi yunk'urin kasheni ka goyi da bayan ta, to bari kaji wallahi da kai da ita duk ban kyaleku ba, sai nasa an tsaga min ku gida biyu,zakaci uwarka! k'aryar daba!! kake tawa dabar!! tafi taka" A zafafe! Walidi yace"wa kake zagi! in ka isa kai wani ne k'ara zagina ka gani" Cikin gadara Iro yace"Uwarka!! Ehh gshi na zage ka me zaka iya ne"!! Da gudu Walidi yayi kanshi ya yar k'asa ya dinga dukanshi, Sai da yayi masa laga!laga sannan ya d'aga shi yana huci! ya tsaya kusa da Balaraba wacce ke tsaye kawai ta rasa ma wane irin tunani zataiyi wannan masifa har ina! Yace"in ka isa ka k'ara shiga hurimin Balaraba, sai dai Uwarka ta haifi wani, ya karasa maganar yana cije baki! Ihu! Uwa! take kurmawa tana tsinewa Walidi, Iro ta kallah wanda yake kwance bai san in da hankalin shi yake ba, jini ne kawai yake futa ta hancinsa da bakins, da gudu ta karasa gurin da Lantana take tsaye, tace"Lantana a gabanki za'ayi kisan kai, sabuda ke butulo ce wato kin manta alkairin da yaron nan yake miki,kullum ya dawo daga tafiya kin dinga k'arb'e masa kud'adan sa, babun abunda zance dake sai dai ince Allah ya isa tsakanina dake Lantana" tana gama fad'ar haka ta shige cikin gidan da gudu domin ta d'ebo ruwa wanda zata zubawa Iro da alama suma yayi Tana barin gurin Lantana tace"Yo ni me zan tsinana miki, kaji masharanciyar mace, ko zatai min sharri, yashe nake ganin Iro ma balle ya bani kud'i o ni Lantana Allah ya had'ani da suruka wacce bata k'auna ta" Banza Walidi yayi mata,hankalin sa na kan Balaraba yana tausar ta, kawai sai saukar mai soyayye yaji a k'afafun shi ya waiwaya a zabure! Shamsiyya a tsaye a bakin k'ofar shigowa hannuta rik'e da abunda take tsamo a wara, sai muzurai! take sam! bashi taso mai ya sama ba Balaraba tayi niyyar watsa wa sai ya sauka a k'afarshi. *Muje zuwa* *Comment* *Vote and Share* [15/07, 22:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿50* Da sauri Balaraba ta sunkuya tana duba k'afarta guda wacce soyyayan mai yayi nasarar zuba lokaci guda ya tsun kafarta suka tashi, sabuda nan mai ya zuba Walidi kuwa ko ta kan kafarshi bai yi ba, yayi kan Shamsiyya, da wani mahaukacin duka, da gudu tayi cikin gidan, domin tasan zai iya ji mata ciwo, Duk suna tsaye a tsakar gidan ta shigo a guje ta nufi d'akinsu ta kulle kof'a tana zagin Walidi tace"dan Uwarka, ka manta ranar da ka k'onani akanta, wallahi naso ita man ya sama shegiya mai sufar aljanu" K'wafa Walidi yayi kawai yace"sai dai in baza ki kara futowa ba amma billahillazi sai na k'one miki wannan bak'ar fuskar taki,wacce ta gaji da bilitin" d'akin Balaraba ya nufa yana k'okarin bude mata, Lokacin da ta shigo cikin gidan kai tsaye d'akin Iya ta nufa, duk mutan gidan babu mai kula da ita, gwara ma matar Kawu wato Sadiya,ita kuma, bata zama,kusan kullum tana hanyar gidansu, tana jinyar mahaifiyar ta, Iya na kwance kan wata ya mutsetstsiyar kafita jikinta a rufe,da zani sai rarar d'ari take, Sadiya da Usuman suna zaune sun zabga uban tagumi, suna tsoran su futa Lantana ta dakesu domin haka take musu kullum shiyasa in suka dawo daga makaranta, har indai yayarsu bata dawo ba, to sai suyi zamansu gurin Iya, jikinsu yayi sanyi da rashin lafiyar Iya. Shiga tayi d'akin cikin sallama Sadiya ta amsa, tace" Yayarmu sannu da zuwa" "Sannu Sadiya, kuna zaune ku kad'ai Iya bacci take ne"? " Yanzu ta tashi taje tayi alwala ko sallah batai ba ta koma ta kwanta" Sadiya tafad'a tana kallon yayar tata. " Yayarmu kin dawo lafiya"? Usuman yafada, hankalinshi na kan ta "Lafiya lou Usuman, kayi karatu a makaranta ko"? " Eh nayi yau ma an karb'i haddar da aka bamu" "To ka dage da karatu ni kuma nayi maka alk'awarin zan siya maka keken hawa" Murna yake sosai ya mik'e ya karaso inda take

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108