Chapter 79
Chapter 79
yake nuna mata ta kalla, ita fa bataso tana had'a ido dashi domin. Idanunsa suna mutukar kashe mata jiki. Dakewa tayi tace"Duk maganar da zamuyi muyi ta anan da can da nan duk d'aya ne" Shiru yayi na minti biyu, yace"Na fi so ina kallon fuskarki maganar zata fi armashi" Tab'e baki tayi tana d'an hararsa, minti biyu da maganar tasa ta mike a nutse taje ta zauna kujerar da ya nuna mata, zama tayi irin Wanda ake Dora kafa d'aya kai d'aya. Kallonta yayi yana mamakin zaman k'asaitar da tayi, babu Wanda ya isa yayi irin Wannan zaman a gabansa, ba tare da ya karb'i hukunci ba, amma da yake ya san halinta sai ya share kawai ya gyara fuskarsa sosai idanunsa ya zuba mata babu wasa yace"Inaso ki yi min bayanin Asalinki dana mahaifiyar ki, domin inajin a jikina akwai wani al'amari a game dake, bazan b'oye miki ba, nafi k'arfin shekara goma shabiyar ina mafarki dake tare da wata mata da alama mahaifiyar ki CE,tunda kullum tare nake ganinku kuna zuwan min cikin mafarkina, wannan mafarkin babu Wanda yasan dashi sai ni sai ke, yanzu Dana fad'a miki" ****** ****** ****** A kori kura guda biyu aka cika da kayan masarufi, su Shatima suka nufi gidan su Balaraba inda suka samu rakiyar daga Bubu direba tunda shi kadai ne yasan gidan. Sosai Shahid yayi mamakin inda mahaifar Balaraba take,ashe dama 'yar talakawa ce tilis, Lallai so babu ruwanshi ko a mafarki bai tab'a tunanin zai iya zuwa irin wannan gurin ba, Soyayar da Moddibo yakewa Balaraba ta gaske CE. Tabbas yayi mamaki da ya kalli yanayin jikinta da fatar ta, idan zata kwana tana rantsuwar babu Wanda zai CE a cikin irin wannan guri take rayuwa. Yara ne suka fara taruwa a gurin suna tsale suna d'ane mota sai su ruga da gudu, hankalin Samar in dake can tsallake ya dawo Kansu da sauri suka k'araso gurin, Buba Direba ya bud'e mota da sauri ya futo ya bud'e wa su Shahid suka futo, ganinsu cikin kayan sarauta yasa yara zurawa da gudu zuwa gidajansu suna ihu! Suna fad'in ga sarki! Sarki ga sarki! Mutane suka fara lekowa daga gidajansu. Da sauri Shahid ya umarci matasan nan dake tsaye a gurin yace su fara d'ibar kayan nan suna shiga dashi, lungun su Balaraba, Buba yayi gaba, sukuma suka koma cikin motar saboda hayaniyar jama'a, yuuuuuu!! Jama'ar dake gurin yara da manya suka rufa musu baya domin ganin ina za a shiga da wannan uban kayan masarufi. Lantana ta sawo Kai kenan zata futo daga cikin gidan suka buga karo da Sauri ta koma da baya tana masifa! Abokin Walidi yace"Lantana ina zakije ne"? D'ago kai tayi a fusace za tayi masa masifa"Aik.. Idonta ya sauka kan k'aton buhun shinkafar dake kansa ta bud'e baki kenan za tayi magana, sai ta hango matasa hud'u kowanne kansa da buhun shinkafa irin na kan Abokin Walidi kuma da alama suma gidan zasu kaita,, Zanin jikinta ne ya sabule garin sauri ta buge da kyaure bata damu ba, da sauri ta tsugans ta dauki zaninta da ya fad'i k'asa tana tafiya tana d'aura wa gami da k'walawa Maburuka kira. ************ ************ ************* A nutse take kallonsa tace"Bangane kullum kana mafarkina ba, a ina kasan ni ka san uwata da har zaka dunga mafarkin mu"? Ta karashe maganar cikin mamaki. "Duk ba wannan na tambaye ki ba,duk wata maganar ki ki aje ta gefe guda ki fara bani amsa ta tunda nine na tambaye ki" Tab'e baki tayi yana wani murmushi irin na gefan baki nan, girgiza kai tayi ta dago kai tana kallonsa tace"Ni ba wata aba b'ace kamar yadda kake tunani hakanan kuma ni ba "yar kowa bace, Tunda nake da Moddibo bai tab'a turke ni yana tuhumata da dole sai ya San asalina ba,saboda yasan inda yaje ya d'auko ni" Hararata yayi k'asa-k'asa cikin muskilanci yace"Ni daban Moddibo daban, in zaki fad'a min ki fad'a min banason, bata lokaci" Ganin fuskarsa babu wasa yasa itama ta gyara tata fuskar ta fara magana kamar haka. *Sunana Balaraba Ayuba Tanko* Dago kansa yayi yana kallonta sai ya tuna da lokacin saukar al'kuranin ta. Basarwa yayi yace"B'angaran uwa fa"? Ranta ya soma b'aci, dakewa tayi tace"Sunan babata Hafasatu, kakata kuma Kaka Suwaiba gurin haihuwar babana ta mutu" "Allah sarki, Ubangiji Allah ya jikinta da rahama" Ya fad'a cikin jimami! "Uhumm"! Ina sauraron ki"? Yafad'a yana tsatsare ta da ido. Wasu hawaye ne suke k'okarin biyo kumatun ta, à kufule tace" Wai kai dolene sai kasan Asalina in baka aure na a haka ka fasa ai babu dole. Ni ban san asalin mahaifiya ta ba. Shikkenan Malam" mik'ewa tayi zata bar gurin tazo ta giftashi, kamar kububuwa Dan haushi sai nishi. Take, tana tuno Moddibon ta, duk tsawon lokacin da suka dauka suna soyaya dashi bai tab'a turke ta ba, sai wannan Dan rainin hankalin ai babu dole idan bazai aure ta ba sai ya fasa. Hannu ya rik'e sosai yana murzawa ta sha kunu! Tana fad'in 'sakar min hannuna" K'i yayi yanai mata wani irin kallo, me tattare da abubuwa kala-kala a zuciyarsa yace"Ashe dama wannan zafin kan nata yana nan. Ajiyar zuciya kawai take saukewa idan da tasan tambayar da zai mata kenan babu abunda zai sata ta tsaya ta saurare shi. Mintuna kusan biyar suna a haka bai sake ta ba. Hannusa a cikin nasa , muryarshi bata futa sosai yace"Naji na janye wancan maganar ta baya, tunda ba kyaso amma wannan dole ne ki amsa min ita, lokacin da kina sai da abunci cikin kasuwar sha tambaya maza nawa kika kula"? ************* ************** *************** Mabaruka ta futo daga cikin d'akinsu a sukwane jin irin kiran da Lantana take k'uga mata, fad'i take 'wannan tsohuwa da jaraba take wallahi. Lantana ta shigo gidan tana fad'in "Mabaruka kece me mutanan arzki masu kudi da naira, yau wani Dan sutturar daga cikin mutanen ki ya rufa mana asiri ga kayan arzkiki na......Kafun Lantana ta rufe bakinta Zaratan samari suka dunga shigowa da kayan masa rufi buhu-buhu. Uwa! Ta futo daga ita sai d'aurin kirji da wata daud'addiyar biriziya duk Tasha d'auri hannuta duk ya saki, kanta inda kasan kan jaka fuskar ta sai maiko takeyi,, wata irin gud'a ta rafka Ayurrrrrrrrrr!!! *Muje zuwa* 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿92* Uwa! sai zabga gud'a takeyi babu ji babu gani, sai da tayi me isarta sannan, ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya tace"Yau "yan bak'in ciki zasu mutu, nima lokacina yayi, haihuwa tayi min rana, Mabaruka farar aniya farar haihuwa,nasan wannan alkairin kece silar shi" Ta k'arashe maganar tata tana dafa kafad'ar Mabarukan. Ita kuwa tunani takeyi waye ya kawo mata wannan shatara ta arzkin domin basuyi da wani daga cikin samarin ta ba, wata zuciyar tace mata ko dai Alhaji Saminu ne, mutum da yake so yayi luwad'i da ita. Nan take ta yardar ma kanta cewa shi d'in ne. Bak'in ciki kamar ya kashe Shamsiyya domin suma a junansu hassada suke ma junansu. Shigo da kaya abunci
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108