Skip to content

Chapter 54

Chapter 54

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,237 words 0 views Progress saved
Download Book

Magajin Sarki ni kad'ai nasan abuda yake damun raina fa, jiya kwana nayi ina murk'ususu ciwon cikina ya tashi, kasan yadda yake min in ya motsa min" Da sauri ya kalli fuskarsa yaga duk tayi zuru-zuru, tabbas da gaske yake, yace"kayiwa girman Allah ka rage k'ulafun yarinyar nan, kar kaje ka tayar mana da hankali, kafi kowa sanin in ciwon ka ya tashi, babu me zaman lafiya, da kwanciyar hankali, ba kai kad'ai ne kake shan wahala ba harda mu gaba daya " Girgiza kai Moddibo yayi yace"sam ba soyyayar da nakewa Balaraba bace zata tayar min da ciwon na ba sai dai rashin fahimtar dake tsakaninku da ita, Balaraba ba ta da kowa,a yanxu sai Ina so ka tayani sonta da kula da ita" "Shikkenan zanyi yadda kace, amma don Allah kar ka jawo mana tashin hankali, Indin saboda bana sakin jiki da Balaraba ne, yasa kake wannan tunanin na dai na daga yau insha Allah" Farin ciki ne ya kama Moddibo fuskarshi a sake suka shiga shashen Sarki! d'in zama yayi cikin kujera shi kuma Moddibo ya hau sama,d'akinsu Balaraba, tana zaune ta zanga tagumi cikin damuwa Sadiya da Usuman na zaune gefe-da gefen ta, yayi sallama ya shiga, dak'in dago kanta tayi cikin nutsuwa ta sauke a kansa har ya k'araso kusa da ita ya zauna da murmushi a fuskarshi, yace"barka da asubah sarauniyar zuciyar Yusuf Moddibo, zuciyata tana azabtuwa da so da k'aunarki Ina fatan kin tashi lafiya"? Fuskarta d'auke da k'ayataccan murmushi ta sauko k'asa gami da sunkuyar da kai, tace " lafiya kalau na tashi Ina fatan kai ma ka tashi lafiya"? "lafiya k'alau, ya kwanan bak'unta kuma"? Shuru tayi kawai har yanzu da murmushi a fuskarta, yace" sakko muje k'asa Ku gaisa da mutumin ki" B'ata fuska tayi, tace"ba Kaine kake gaba dashi ba,ai shine ya kamata yazo ya gaishe ni" "Duk da nine nake gaba dashi amma girman shi yafi nawa, kuma a matsayin ki na matata uwar " yayana ya kamata ki d'aukeshi a matsayan magaji na tunda shak'ik'ina neshi, duk ranar da bana nan,shine zai mar miki uwa uba" K'walla ce ta taro a idonta tace" wannan wace irin magana ce kake Yusufu ni dai ka daina min don Allah" Kamar zata fashe da kuka ta k'arashe maganar. Rarrashin ta ya fara yi cikin taushin murya har sai da yaga ta mayar da k'wallar sannan hankalinsa ya kwanta ya kalli su Sadiya gami da shafa kan Usuman yace"kun tashi lafiya"? Kai a sunkuye Sadiya tace"Yaya Yusuf Ina kwana"? Amsa yayi fuskarsa a sake, Usuman ma ya agaidashi a nutse ya amsa, Balaraba tace"Sadiya ai da zazzab'i ta kwana mybe ko b'akonta ne" Hankalin sa a tashe ya jawo yarinyar yana tambayar ta, jikin nata, tace" Yaya Yusuf naji sauk'i abokinka wannan me kyau d'in yana da kirki shine ya bani magani nasha cikin dare" Moddibo yace"sunanshi Sark! Ko ce masa Magajin Sarki! nasan zaiyi fiye da haka ma, saboda yana tausayi" Kicin-kicin da fuska Balaraba tayi tace"ka gafarce ni Yusuf, ko maganar da zanyi maka zata b'ata maka rai, gaskiya kayi masa magana jiya cikin dare ya shigo d'akin nan, gaskiya ni ban yadda ba" Wani iri yaji a zuciyar sa, jin abunda tace"me ya kawo Sarki! d'akin, ya san halin d'an uwanshi ba mane min mata bane,kuma bazai ci amanarsa ba, Sadiya tayi Sauri tace"A'a Yayarmu ya ganni a wajan d'akine shine ya bani magani nasha ya rakoni na kwanta yace kuma in daina futowa cikin dare" Moddibo yace"yanzu naji,zance, kiyi hakuri Gimbiya babu abunda zai faru sai alkairi ba halin Sarki! bane abunda kike nufi" d'an tab'e baki tayi kawai tayi shiru yace"Ku tashi mu sauka k'asa Ku gaisa sai Ku karya" M'ikewa sukayi duka suka nufi k'ofa. Karo sukaci dashi zai hau saman shima, ratse masa sukayi a baranda har ya k'arasa hawowa Mariya baiwarsa ce take bayansa da'alama gyare-gyare zatai masa Wanda takeyi kusan kullum duk safiya, murmushi ya sakarwa Sadiya, sam ! baki kalli inda Balaraba take tsaye ba, ciki-ciki tace"Ina kwana"? yaci albarkacin Yusuf Moddibo. A dak'ile ya amsa, ya mik'awa Sadiya hannu, yarinya mai sauk'in kai da wayewa sai ta sanya hannuta cikin nasa tana yar dariya tace" Magajin Sarki ina kwana"? Cikin mamaki yake kallonta sai kuma ya kalli Moddibo cikin tuhuma yasan shine zai fad'a mata wannan sunan, saboda ba kowa ne ya ke kiransa dashi ba, Murmushi Moddibo yayi, shi kuma ya tab'e baki kawai yaja hannun Sadiya suka nufi d'akinsa, Sakin baki Balaraba tayi kawai tana kallon ikon Allah, shi kuma yana sane ya sakarwa yarinyar fuska duk Dan ya muzgunawa zuciyarta, saboda yana bala'in jin ciwon zargin da take masa a kan yarinyar,baya ga haka ma, yarinyar ta kwanta masa,tana da hankali da nutsuwa ba kamar yayar ta ba. *Comments Vote and Share* 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ _*DEDIGATED*_ *_TO_* ```RAHAMA ALIYU``` ```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM``` *🅿62* K'asa suka sauka zuciyarta tana mata sak'e-sak'e kan zak'ewar da taga mutumin nata yayi kan Sadiya,sam bata yadda dashi ba, ganin yadda yake wa mutane wani irin kallo, kullum ido a lumshe kamar munafuki. Ko da suka sauka k'asa hadimai ne su wajan biyar maza biyu mata biyu suna aikin gyara falon,kowa da inda yake gyarawa, jikinsu sanye da wasu kaya iri d'aya masu kamar Uniform, wani k'amshi ne mai dad'i ya cika hancinta, wani ku-ku ne ya futo daga kchin hannusa dauke da wani tank'asheshan faranti cike da abubuwan ci, Balaraba tayi saurin kauda kanta domin bata so tayi k'auyanci irin na jiya, hannun Usuman ta kama suka ni bayan Moddibo,inda ya nufi Wani k'ebantaccan guri a falon, yace da Usuman ya zauna, yaron ya zauna cikin wata k'aramar kujera mai taushi, zama tayi itama tana bin gurin da kallo gaskiya k'ayatuwar gurin ya burgeta sosai dagani gurin hutawa ne, D'aya daga cikin hadiman dake aiki a gurin ne ya k'araso ya zube gaban Moddibo yace"ranka ya dad'e a kwai abunda za'ayi ne"? A nutse Moddibo yace"ka kawo abun kari na mutum hud'u" Cikin bin umarni ya mik'e daga gurin. Cikin nutsuwa ta kalli Moddibo tace"ya kamata fa ka kira Sadiya haka" " Yanzu zai sauko ai wanka ya hau yayi" Shiru tayi kawai tana d'an ya mutse fuskar ta, tace"tsarin gurin nan ya burgeni Yusuf ina so abu White coulor" Murmushi yayi yace"lallai tsarin ku d'aya da mutum min in kin lura ai duk adon falon nasa white ne" Shiru tayi tana da tasanin fad'ar maganar, minti biyu tsakani yace"zan shirya miki falon ki da wannan colour" "Nagode" Abunda tace kenan,tayi shiru kanta a kasa tana wasa da hannuta Tsura mata ido yayi,kurum yana kallo, ta d'ago kai tana kallonsa suka sakarwa juna murmushi, tace"wannan kallon fa,Yusuf"? Da murmushi a fuskar sa yace"kallon soyyaya ne Gimbiya zuciyata tana fad'a min akwai wani babban al'amari da zai faru a tsakanina dake" Itama Murmushin take,tace"babban al'amari ai bai wuce na aure na da kai ba, dama ina so in tambaye ka a wace matsaya muka tsaya,nifa zama anan kamar a kan k'aya nake" " Karki damu insha Allahu yanxu in na tashi daga nan gurin me Martaba zan wuce, za'ayi komai a gama cikin kwanciyar hankali"

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108