Chapter 82
Chapter 82
sai aikinsu suke, k'amshi suke ko ta ina Sarki yana cikin wata d'anyar Shadda gezner me mugun tsada anyi masa wani irin dinki babbar Riga da " yar ciki ita kanta hular dake kansa da da yankin shaddar aka had'a ta kafarshi sanye da wani takalmi rufaffe mai mugun kyau kalar kayan jikinsa sky blue yayi masifar kyau fysakarsa sai futar da annuri take, sajensa ya kwanta lif-lif a fuskarsa hannusa wani irin agogo ne, na zallahr azurfa, kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki da annushuwa, sai gaisawa yake da manyan mutane gwamnoni da "yan majslisa sanatoci da sauransu, " yan abokan arziki duk murna sukeyi da farin ciki. Wata kujera ya nufa wacce a ka k'wata ta da shimfud'u na alfarma yana tafe su Shatima na take masa baya, zama yayi cike da k'asaita, wasu nayi dake tsaye suna jiran zuwansa suka hau yimasa firfita, Shahid da Shatima suka zauna gefe da gefan sa. K'irari kawai kakeji da busa marok'a sun rud'e kowa da irin nashi rok'on kowa naso ace nashi yafi na d'an uwanshi. "Masha Sarki! Ya futo fasa taro Jimana na gaban Giwa, baka iya ba Allah ne zai yi maka, yaro me Halin dattako! Fari mai farar anya! Hak'ika matayen ka sun dace da samun nagartaccan miji jarumin jarumai,, Duk zaka iya dasu har da k'warl'wara ma, Sarki! Almasur kujerar mulki takace Allah ya yataka ruk'o jamuje Gami sha sassaka duk wani mak'iyinka sai da ya mutu!!!!!! faaaa!! Gurin d'aurin aure ya kai ya kawo jama'a d'aurin auran mataye uku ba wasa ba ne, Waziri Zayyanu na gefe guda shi da tawagar shi duk ransa a b'ace yake shi ba abun ya koma gida, wata zuciyar tana ce masa ya zauna kawai a k'arasa dashi, dole shine Waliyyin Ango kuma yayi rantsuwar bazai masa waliyi ba, Yana kallon Shige da fucen da Galadima yake shida Wambai, sam sunk'i su zauna kusa dashi,sun karkata gurin Sarki,yasan duk kalar munafurci ne, kujerar mulki sukewa yaga kuma yadda za'ayi a karb'eta a hannusa. Gaisawa kawai yake da jama'a ba dan ransa ya so ba, mutane sai zind'ansa suke suna nuna shi a matsayinsa na Sarki me rik'on k'warya. Sai da aka fara d'aura auranshi da Halisa kan sadaki dubu d'ari sannan aka d'aura da Azima itama sadaki dubu d'ari, sai Balaraba itama haka, Liman ne ya karb'i wakilcin Balaraba,saboda babu wakili Sallau ne kuma bai zo ba saboda tsabar bak'in ciki,shi kuma Maman baya gari yana can tafiya tafiyensa dake babbar motar d'aukar kaya yake ja,,, Kowa ce aka damk'awa Wakilinta sadakin ta, Liman ya rik'e na Balaraba a hannusa yace shi zai bata da hannusa. Bayan d'aurin. Aure guri ya hargitse da ciye-ciye na abunci nau'i nau'i ana futo dashi daga gida,, Masha Allah kowa yaci kuma yayi guziri guri bai watse ba sai dab da sallahr azahur sannan kowa ya nufi gida domin yin sallah. Mahaifin Azima ne suke keb'e da Waziri suna maganganu k'asa-k'asa karku manta da cewar dama tuntuni abokai ne Tun daga nesa Sarki! Ya Fahimci akwai maganganu da suke tattaunawa. Kuma da alama basu da gaskiya, suna ganin sun k'araso gurin Mahaifin Azima ya saki fuskarsa sosai yana fad'in "Dama ina cewa azo a nemo min kai muyi sallama yau zamu koma ni da tawaga ta, inai maka fatan alkairi da d'or ewar zaman lafiya kai da iyalinka, ga Azima nan nabaka amana,yanzu ma abunda nake kara jaddadawa abokina kenan gashi nan a tsaye" Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya mik'a masa hannu yana fad'in "Insha Allah karkadamu mungode sosai A sauka lafiya" Cire hannusa yayi ya mik'awa Waziri Zayyanu, kauda kai yayi ba tare da ya bashi hannusa ba, yace"Ka rik'e gaisuwarka ni bana buk'atarta, na fad'a maka tun wuri tsalle d'aya mutum yake ya fad'a rijiya, amma sai yayi dubu bai futo ba" Yana gama maganarsa ya wuce ya barsu tsaye a gurin, Sarki! Shahid Shatima Duk suka bishi da kallon mamaki. 👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿94* Sanin Hali yafi sanin kama,Sarki fuska yayi kawai ya wuce ba tare da ya tsaya ya k'ara sauraron wata magana daga bakin Mahaifin Azima ba wato me Martaba sarkin Yalwa, ganin ya wuce ne yasa su Shahid suma suka rufa masa baya suna cike da mamakin abunda Waziri Zayyanu ya aikata. Suna tafe suke maganar har suka isa shashen nasa Shatima ya zauna kan kujera yana fad'in "Sai yanzu gajiya ta fara damuna kuma" Shahid yace"Duk ba wannan ba, abunda wannan mutumin ya fad'a fa abun dubawa ne, Tsalle d'aya mutum yake ya fad'a rijiya,Wannan Kalmar a hausance meye ma'anarta"? Wani k'asaitaccan murmushi Sarki! Yayi yace"Ku rabu dashi don Allah inajin shine zai fad'a rijiyar ya kasa futowa" Shatima yace"magana ce me harshen damo kuma da gani akwai wani k'ulli Shahid yace"Nima na lura da haka wallahi tunda muka doso inda suke, suna magana k'asa-k'asa" Tab'e baki Sarki yayi yana kici-kicin cire babbar rigar dake jikinsa yace"Mugun k'ullinsa zai koma k'ansa ni ina tare da Allah" "Wannan magana haka take,duk mutumin da yake tare da Allah kuwa to babu abunda wani mutum zai masa ba tare da Allah ya tsare shi" Su Shatima ne suka fad'i wannan maganar. Zama yayi kusa da Shahid da gashi sai Singelt da dogwan wando na shaddar dake jikinsa, yana fad'in zafi nake ji wallahi ga yunwa kasan tun jiya da yamma rabona da cin abunci" Shahid yasa dariya yana fad'in ai zama da yunwa ya k'are me mata hud'u rigis" Gabansa ne ya fad'i kad'an shi kansa yana tunanin yarda za'ayi ya zauna dasu lokaci guda. Shatima yace"Mutumina ai jarumi ne, zai iya rik'e su, ni dai INA ja maka kunne da kayi adalci a tsakaninsu" Shatima ya k'arshe maganar yana dariya Hararasa yayi yana fad'in "Ank'i ayi adalci me yasa su baza ka fad'a musu suyi min adalci ba sai ni zaku ta damu da maganar adalci, duk wacce tafi kyauta ta min itace Gimbiya ta" Dariya suke masa,Shahid yace"Maganar haka take duk macan da take kaytata ma kafi jin ta aranka. Ammafa kowa ce mace da irin nata salon wata akwai iya salo da jawo hankalin me gida da iya kwanciya wata kuma iya girki da iya hira wata kuma iya kwalliya da tarairaya duk dai gasu man, idan Allah ya hore maka mace me ibadah fa duk wannan abubuwan Dana fad'a to kayi sa'a a rayuwarka" Shatima yace"Wannan maganar haka take" Shiru yayi musu suna ta zubah, mik'ewa yayi ya je ya k'aro k'arfin AC sosai yake jin zafi abunka da wanda be saba ba,ya shiga cikin jama'a ga rana da cukurkud'u kowa naso ya gaisa dashi, shiyasa ya daure ya dunga gaisawa da jama'a domin futa hakkinsu Shahid ne ya kalle shi yaga yana lumshe ido, yace"Ko a sa a kawo abunci ne" Bud'e ido yayi yana kallon daining, babu komai a kai, d'aga kai yayi ya mayar da idonsa ya lumshe. Shahid ya mike yana k'okarin futa, bud'e idonsa yayi a karo na biyu yace"Kasan me"? Shahid ya tsaya yana kallonsa, shi kuma yace"tea nake so
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108