Chapter 25
Chapter 25
kunyar yarinya kwanakin baya, da sukayi saukar al'kurani,makarantar tasu ta kawo saukar gaban sarki, Sunanta Balaraba, bazan taba mantawa da kallon banzan da tayi min ba, kai in ka gani sai kayi mamaki, lokacin kana can Swiziland, abun ya bani mamaki, sosai" Murmushi Maddibo yayi yace"nafada maka duk me wannan sunan ba karamar mace bace, mybe ka nuna mata halinka ne shiyasa ta nuna maka nasu halin" Tabe baki yayi yana dan sosa sumar kanshi wanda hakan ya zame masa jiki in dai zai yi magana sai yw sosa kanshi yace"me ya dameni da ita,kasan ni mata basa gabana,wallahi, kai ni fa zan iya kare rayuwata batare da wata mace ba" "Wannan kuma mahaukaci zaka fadawa wanda bai san wanene kai ba" Dariya yasa ya dan sosa kai yace"Wallahi nake gaya maka yarinyar nan wai a na cewa gani na fito, ita ta riga kowa tashi domin ta ganni ina lure da ita, daga baya kuma ta fara yimin kallon banza,sai kace wani sa'an ta" "Maddibo ya ce" ka ishemu da zan wata yarinya ko ka na ciki ne, dan ban taba ganin ka ka zauna zance wata ba,ko Halisa bata da wannan matsayin" "Kai me zanyi da wannan yarinyar" yafada yana gyara fuska ya cigaba da cewa"kawai dai inai maka kwatance da ita ne, Allah yasa taka Balarabar ba irin halinsu daya da waccan din ba" "Zamuje ka ganta ne ai sam tawa daban take da kowa" "Ok Shikkenan, Allah yasa" Nan suka cigaba da hira har suka karasa Unguwarsu Balaraba, Maddibo ya kalli Haladu Direba yace"yi parking dai-dai can" da sauri Haladu yayi parking din motar inda a ka umarce shi, A nutse ya dago kanshi yana bin unguwar da kallo, Kallon Maddibi yayi yace"wannan wace irin unguwa ce ka kawo mu, guri duk tarkace da kazanta, ko ina kango,da kwatoci, kasan bazan fito ba wallahi,kaje kasa a kira maka ita" Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke domin yasan dole za suyi haka dashi, yace"kake maganar kango duk gidajan jama'a ne, duk babu wani kango a cikin nan unguwar, wannan tarkacen kuma da kake gani yaran unguwar ne suke sana'ar gwan-gwan" Ya mutse fuska yayi yace"gaskiya Maddibo baka da kirki, yanzu da kasan a irin wannan unguwar budurwar taka take ka gayyoto ni,kamar baka san halayyata ba, kai yanzu ya dace"kazo ka nemi matar aure a irin wannan guri"? "Kaga bana son ka bata min rai dan Allah, kafito mu shiga ga lukon gidansu can,yanzu duhun dare ne babu wanda zai gane ka" "Billahillazi, babu inda zanje nayi iya yi na, in ka damu kai ka futa ka kurawo ta sai mu gaisa,amma bazan fita daga motar nan ba,haka kawai kwalabe su fasa min kafafu,kan wata shashashar budurwar ka wai ita Balaraba" ya karashe maganar yana gyara kwanciya cikin motar babu abunda ya dame shi. Sanin halin taurin kai irin na Sarki! yasa Maddibo jan tsaki ya bude motar ya fita sabuda yasab duk nacin da zai masa bazai fito ba kamar yadda ya fada Dariya Sarki! yasa bayan fitar Maddibo daga cikin motar yace"duk Abinda zakayi kayi amma bazan fita in cuci kai na ba" Haladu Direba ya fito ya tsaya a bakin motar yana kalle-kalle, ganin fitowar Maddibo, yasa ya karaso Maddibo yace"ka tsaya kawai zan fito zan shiga gurin can" "A fito lafiya yallabai" Haladu ya koma bakin mota ya tsaya, Ganin motar gidan Sarauta yasa yara suka fara, taruwa *Comment* *Vote and Share* [02/07, 14:47] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» ββββββ _*GIMBIYA BALARABA*_ ββββββ πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» _*Na*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani Writes Associationπ€π» ```Bisimillahir rahamanir rahim``` *π Ώ36* Kasancewar babu wutar nepa a unguwar shiyasa yara basu ankara ba sosai, dabi'ar yaran cikin gari kenan in suka ga bak'o cikin mota zasu zo su tsaitsaya suna kallo wasunsu kuwa har zuwa suke su dinga taba motar suna dariya suna rugawa gida da gudu,Sarki!yana kwance cikin motar yana bin unguwar da kallo, cikin zuciyarsa yace"yanzu haka jama'ar dake cikinta suke rayuwa, wasu gidajan gasu nan duk babu kofofi, wasunsu an sanya musu buhu an kare sabuda kar a gano cikin gidan, a fili yace"da gani gurin zai yi sauro sabuda tarin shirgi da datti da kazanta, dole a kawowa unguwar a gaji, Shi kadai yake wannan sake-saken cikin zuciyarsa, gefe guda kuma ya zaku yaga wannan yarinya da Maddibo ya makance a kanta. A nutse Maddibo ya kutsa kansa cikin lungun su Balaraba wanda yake dauke da tarkace iri-iri haka ya dinga tsallake kananun langa-langa da robibi har ya karasa kofar gidansu Balaraba,inda yara da matasa suke tsaye kan Shamsiyya wacce take ta faman soya awara da kwai, Gefe guda ya ja ya tsaya ya kira wani yaro wanda yake tsaye kan Shamsiyya yana jira ta sallame shi, "Kai Salmanu ungo awarar taka, in sallame ka in huta" Shamsiyya ce ta dago tana wa Salmanu magana,kawai sai ta ganshi ya nufi gurin wani mutum can gefe, fitilar wayarta ta kunna ta haske fuskar Maddibo tana wani ya mutse fuska tace"wancan wanene a tsaye a can ne" Da Sauri Walidi dake tsugune kusa da ita yana zukar wani abu a tsumma ya mike yana wani ciccije baki yace"yana ina ne yanzu in farde masa ciki"! "Gashi can naga ya kira Salmanu ko uban me zai yi masa oho! je ka gani" Walidi na tafiya yana hada hanya ya nufi inda Maddibo ke tsaye tare da Salmanu Matasan dake tsaye a gurin ne suka rufa masa baya suma cikin rashin tarbiya suke cewa"bari muje muga wane dan iska ne,yanzu mu kaddamar masa"! Maddibo yana hangen zuwansu gurinsa sai ya gyara tsayuwarsa, har suka karaso gurin,suka tare Salmanu, cikin tsageranci Walidi yace"kai ina zaka ne? me wancan guy yace maka"? Jiki na rawa Salmanu yace"Cewa yayi in kira masa Gimbiya ta gidanku" "Kai!! dan uwarka wacece Gimbiya a gidanmu"? Walidi yafada yana dukan kafadar yaron. " Balaraba fa yake nufi" Salmanu yafada jikinsa na rawa domin wani irin tsoran Walidi yake ji Cikin tsawa!Walidi yace "kai! kauce daga nan dan uwarka ko in yaga ka, yanzunan" Da gudu Salmanu ya bar gurin, Cikin wata irin tafiya Walidi ya karasa kusa da maddibo ya tsaya yana masa wani irin kallo, duk da cewa a kwai duhu a gurin bai hana shi ganin irin kallon da yake masa ba. "Kai waye ya baka izinin shigo mana lungu ehe,! mufa duk inda mukaga bakuwar fuska babu yadda, gurin wace Gimbiya kazo a lungun nan" Dariya ce taso takama Maddibo ganin yadda yaron yake wani ciccije baki yana wani tangadi tamkar zai kai masa duka, gashi sai warin ganye suke dukkaninsu, girgiza kai yayi gami da gyara tsayuwa yace"Sannuku "yan samari, ni bak'on alkairi ku kwantar da hankalin ku, Gurin Balaraba nazo" Walidi ya gyara tsayuwar gami da zira hannu cikin aljuhun wandonsa ya fito da wata wayarsa wacce duk ta sha dauri ka da kyaure sabuda tsabar ganin duniya,ya kunna fitar wayar cikin sigar rashin mutumci ya dallare fuskar Maddibo da ita, Sai wayar ta kusa faduwa sabuda razana da yayi, ganin Fuskar Sarki!Almansor da yayi, sabuda Maddibo suna dan yanayin kama da Sarki!amma ba sosai ba, sai dai duk inda jininka yake za'a ga kama ko yaya ne" Bakinshi na rawa yace"ranka ya dade, kace Balaraba kake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108