Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,254 words 0 views Progress saved
Download Book

son gani"? "Kwarai kuwa" Maddibo yafada fuskarshi a sake, Washe baki Walidi yayi yace"ai kuwa bata dade da dawowa daga kasuwa ba, wallahi ai yaya ta ce, bari in shiga in kira maka ita" Fuska a sake Maddibo yace"Ok nagode Abokina, kace"mata Yusuf ne" "E ai insha Allahu zan yi mata bayani" Walidi yafada gami da juyawa da sauri! Maddibo yace"jimana" Walidi ya dawo da sauri ya zube kasa bai sani ba, Maddibo yace mike tsaye mana Abokina" Cikin yake Walidi ya mike tsaye sam ya kasa hada ido da Maddibo sabuda tsabar kwarjin da yayi masa, Hannu ya zira cikin aljihu ya fito da kudi daurin "ya dari-dari guda uku ya mika masa, Hannu na kyarma Walidi ya karba yana ta zabga godiya, Gyaran murya yayi yace" ka dauki dauri daya ku raba da kai da abokanka, sauran dauri biyu ka bawa mutanan gida" Godiya kawai Walidi yake bakinshi yaki rufuwa,sauran matasan dake gurin suka sanya ihu!suka bi bayan Walidi da gudu, Shamsiyya ta dago kanta tana kallonsu har suka karaso gurin basu bar ihun murna ba, ranta a bace! tace"kai wannan wane irin iskanc......kafin ta karasa maganar tata Walidi yazo yayi fatali da kaskon suyar awarar wanda yake cike taf da mai gami da awara cikin kwai, da sauri! ta dauke kafafunta tana kurma ihu! sabuda yadda mai duk ya zuba a kafafunta, kafin ta dawo hayyacin ta Walidi ya daki! Katuwar rubar dake cike taf!da awara an soya ta gwanin sha'awa, duk ta watse a gurin cikin kasa da tarkacan kazanta, ihu! ta kurma ta mike da sauri tayi kan Walidi tana dura masa ashar! ba ta sani ba ta tsumbula kafarta cikin kaskon awarar wanda ke dauke da ragowar mai da bai karasa zubewa ba, durkushewa tayi a gurin tana rike kafarata sosai ta kone, a kafafun da hannunta guda. Cikin Ihu!da hargowa Walidi yq shiga gidan, sauran matasan dake biye dashi a baya suna tayashi, Lantana ta mike da sauri! har sai da zanin jikinta ya sabule ya fadi kasa tayi saura daga ita sai dan tofi, Cikin gigita tace"shikkenan Walidi ya jawo mana musiba ooo ni Lantana! Uwa! ma fitowa tayi daga dakinta kanta babu ko dankwali,gabanta yana mugun faduwa tace"kai Walidi menene kake mana ihu! ne"? Banza yayi musu ya nufi dakin Balaraba da gudu, yana fadin" Aunty Balaraba Gimbiya ta gidan sarki! ki fito kinyi babban kamu, daga yau nine zan zama yaronki, Allah ya yanke min wahala" Tana zaune kan dadduma hannuta rike da carbi idar da sallahr ta kenan, taji shi yafado mata daki yana mata sambatu, Jin abunda Walidi yake fada yasa Lantana, bankada labulen dakin Balaraba da sauri ta shiga har tana kokarin faduwa, tace"kai Walidu me kunne na yaji kana fada ne"? *Muje zuwa* *Comment* *Vote and Share* [03/07, 14:29] +234 808 996 5176: πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ† _*GIMBIYA BALARABA*_ βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ† πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*Zamani Writes Association*_🀝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rahim``` *πŸ…Ώ37* _*Almuminu,Almuhaiminu ya Allah*_ Wani kallo Walidi yayi wa Lantana irin nasu na marasa tarbiya yace"kinga Lantana duk wani zancan bakin ciki da hassada ya kare, ni daga yau wallahi na dai na biye muku ku cuce ni, Balaraba dai Allah ya rufa mata asiri,dan Sarkin garin nan shine yazo gurinta gashi can a waje" Lantana bata bari ta karasa jin zancan Walidi ba ta nufi hanyar waje tamkar zata kifa sabuda sauri, Iya ce tayi sauri ta tari gabanta tace"ina zakije haka Lantana dubi jikinki babu zani daka ke sai dan tofi" "So nake inje in ganewa idona zancan da Walidi yazo dashi" Lantana ta karashe maganar tamkar wata zautacciya Sadiya Matar Kawu tasa dariya tace"yanzu ke Lantana idan a kace ki futa haka sai ki futa,to in kin futa waje me zakiyi"? Iya ta riko hannuta ta dawo da ita tsakar gida ta zaunar da ita kan tabarmar ta,sannan ta leka dakin Balaraba tace"me kike yi baki futo ba kije kiga ni ko waye" A nutse tace"Iya babu inda zani ni domin ba muyi da wani zai zo gurina ba,sai dai idan wata Balarabar a ke nufi bani ba" Walidi kamar ya dora hannu a ka yace"dan girman Allah aunty Balaraba kizo kije ku gaisa,kin san dai bazan miki karya ba, wallahi da gaske nake" Shamsiyya ce ta shigo cikin gidan tana durawa Walidi zagi ta Uwa ta Uba, sai jan kafa takeyi, Mahaifiyar su ta gani tsaye bakin rijiya tayi shiru, kamar babu ita a gurin, cikin jin radadin zafin ciwo tace"Wallahi Uwa!yau sai nayiwa Walidi rashin mutumci, kinga yadda ya kona ni, yayi miki barna,gashi can duk ya zubar miki da awarar gaba daya" Wani uban zagi Uwa!ta kurma tana kwalawa Walidi kira wanda yake dakin Balaraba yana tw zabga mata magiya kan ta taje gurin Maddibo. "Wai me yake a cikin dakin waccan mutsiyaciyar ko tafara koya masa iskanci ne" Shamsiyya tafada tana daga muryar ta dan Balarabar ta ji ta. "Rabu da shashasha kwadayayye kawai,makarya cin banza da wofi wai dan Sarki ne yazo zance gurinta shine yazo yana yiwa mutane shirme" "Kan Ubancan"! Shamsiyya ta kurma wani uban zagi,ta cigaba da cewa" shine ya kona min jiki a kan waccan,wallahi bazan yadda ba,sai nayi musu wulakanci, wane dan Sarki kawai yace Farkanta ne ya biyo bayan ta meye ba mu sani ba" ta karashe maganar tana buga cinyar ta Lantada dake zaune kurum tun dazu bata ce uffan! ba tace"shiyasa ai nake so in futa in ci masa mutumci in koreshi, sabuda nasan babu wani mutum mai mutumci da zai zo gurin wannan lalatacciyar sai lalatacce, O ni Lantana,yanzu in da gaske ne dan Sarki ne yake son yarinyat nan ina zan sa kai na" ta karashe maganar har da rike haba! Sadiya matar Kawu tace"Ko wane irin miji Balaraba zata aura, duk mulkinsa da dukiyarsa gami da nasabar sa, Lantana baki isa ki hana abunda Ubangiji ya tsara a kan ta ba,Balaraba dai ta zama murucin kan dotse wallahi,bakin cikinku babu in da zashi a kanta" Kuka Lantana tasa har da fyace majina tace"Ni kikewa rashin kunya Sadiya har kina kokarin zagina tsofai-tsofai da ni" Uwa!ta tabe baki gami da cewa"muna furci dai dodo ya kanci meshi,ehe!! ai gashinan ke da kike daure mata gindi tana kokarin zaginki ,gaskiya naji dadin wannan abu" Sadiya matar Kawu dakinta ta shige tace"gaskiya ce ba kyaso Lantana dole in fada miki" Ganin Nacin! da Walidi yake mata ya ki karewa yasa ta mikewa tsaya har yanzu tana cikin hijab dinta har kasa ta kalleshi gami da cewa"muje shikkenan ai sai ka sakar min mara in sake" Walidi ya washe baki gami da cewa"Yawwa matar Manya,aike yanzu kin zama kadara a gidan nan, ba irinsu wadancan "yan iskan ba" Yana sane ya fada da karfi dan Shamsiyya taji,aiko ta ji shi, yana futowa ta dinga zaginsa, tana hadawa da Balarabar, shiru kawai Balaraba tayi mata,shi kuwa Walidi kallonta yayi shekeke!yace"mahaukaciya kawai a haka zaku shegu "yan iska, kawai" Da gudu Shamsiyya tabishi tana zaginsa, kamar wata "yar maguzawa, Balaraba tayi saurin kaucewa tabata hanya, tana mamakin ta tamkar wata dabba haka take ganin Shamsiyya sam!bata da nutsuwa balle kamun kai. Tuni Walidi ya fuce daga gidan, sai ta tsaya bakin kofar gidan tana kalloshi yana tsaye can

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108