Chapter 29
Chapter 29
shi dade nace Allah yasa lafiya, ko wani abune ya faru a unguwar ne" "Lafiya kalau, nazo gurin wani abokina ne" "Masha Allah Yallabai dafatan ka same shi lafiya"? " Alhmdulilahi" Maddibo ya fada yana jin zuciyarsa babu dadi,Sarki! ya cuce shi, yanzu yaya zai yi ya shawon kan Balaraba, Yana zaune a ka tafaran Falonshi shi kadai kwal, in banda karar AC babu abunda kakeji, yana zaune a wata kujera me cin mutum daya daga shi sai wando 3Quetar kafarshi daya kan daya kana kallon irin zaman da yayi kasan na masu mulki ne, Sigari yake zuka yana lumshe ido,zuciyarsa in banda zafi da turiri babu abunda take,jira kawai yake Maddibo ya shigo suyi ko wacce-wacce,domin yana ji yana gani bazai bari ya auri yarinya kamar wannan mara tarbiya ba babu yadda za'ayi ta shigo ta bata musu zuri'a. *Comment* *Vote and Share* [07/07, 12:38] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ∆∆∆∆∆∆ _*GIMBIYA BALARABA*_ ∆∆∆∆∆∆ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*Zamani Writes Association*_🤝🏻 _*DEDICATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` *®REAL BINTU BATULA👄* *🅿40* ```Bisimillahir-rahamanir-rahim``` Maddibo ne ya shigo falon cikin sallama,amma kana kallon fuskarsa kasan yana cikin bacin rai, kujerar dake fuskantar sa ya zauna sosai ya murtuke fuskarsa, yace" yace "Yanzu abunda kayi mun ka kyauta kenan, haka mukayi da kai ? a kan zakaje ka bata min lamarina a gurin yarinyar nan" Hannu ya daga masa a fusace! ya mike zaune sosai ya gyara zamansa, yana kashe guntuwar tabar dake hannunshi cikin wani karamin plete wanda ke aje kan wani karamin teble dake gabanshi, a ya mutse yace "me nayi maka, zaka zo kana min wani shan kunu,ni ban yi magana ba,kai ne zakayi magana, haka kawai ina zama kazo ka dauke ni la kaini an ci mun mutunci, wannan bayi ba ne" Ya karashe maganar yana huci! Kasa Maddibo yayi da muryar shi ganin yadda Sarki! ya ke hayaniya, yasan halin bakar zuciyarsa yanzu sai ayi batacciya shi dashi,shiyasa ya kwantar da kai, dama kuma (Annabi muhammadu slw) yafada cewa idan mutum biyu na fada,to daya yayi saurin saukar da zuciyarsa gudun abunda zai je ya dawo,idan duk zucoyoyi biyu suka dauki zafi a lokaci guda,to shedan zai samu abunda yakeso,a kansu, Allah kasa mu dace "Yanzu a matsayin ka na namiji mai hankali a kanta ya kamata ka biye mata duk abunda tayi, wannan ni kawai ka ciwa mutumci wallahi" "Ok " Ok wato ni ba kaga abunda tayi min ba,yariya karama tana nema ta zageni, abunda babu wanda ya taba yimin shi a rayuwa ta ita tayi min sabuda samun gurin kazo ka nai min wata maganar banza, Ok zan dauki mataki akanta mai tsauri wallahi sai inga yadda za'ayi ka aureta" "Duk abunda zakace sai dai kace" auran yarinyar nan kamar nayi nagama,kuma duk abunda tayi maka kai ne ka jawo tayi maka, me ye ruwanka da sana'arta da har zaka dunga kiranta da "yar towo-towo wannan ai cin fuska ne, kuma a sanina da kai nasan wannan dabi'ar ba taka bace,kawai ka ara ka yafa ne" A harzuke! Yace"an kira ta da "yar towo-towo din karya akai mata ne, in tayi wasa ma da " yar tasha za'a kira ta watarana" Zare ido! Maddibo yayi cikin mamaki yace"wai me yake damunka ne, kai me yarinyar nan tayi maka da zafi haka"? Tsaki! yayi ya koma ya kwanta cikin kujera yana lumshe ido zuciyarsa sai zafi take Maddibo yace"dan Allah kafada min meye alakar ka da yarinyar nan Balaraba naga alama kun san juna,ganin yadda kuka shaida juna da wuri" Minti biyar bece komai ba,farlon yayi tsit! bakajin komai sai karar AC kadan-kadan, Cikin Ginshera yace"Babu wani abu da ya hadani da ita, hasali ma ban taba ganinta ba,sai ranar saukar su, wacce sukayi ta wattanin baya da suka wuce, wannan shine ganina da ita na farko, tun daga ranar ban kara dora idona a kanta ba sai yau" Cikin mamaki Maddibo yace"kana nufin kace min itace yarinyar da kake fada min dazu muna mota" "Kwarai kuwa" yafada idanunshi a lumshe, ya cigaba da cewa"tun ganina da ita na farko naji na tsaneta sabuda dabi'ointa na lura yarinyar tana da girman kai sosai, kai kanka kasan halina bana shiri mutum mai girman kai da nuna shi wani ne" Girgiza kai Maddibo yayi yana cigaba da sauraronsa Ya cigaba da cewa"babban abunda ya burgeni da ita shine, lokacin da aka kirata cikin jama'a a lokacin bukin saukar alkur'anin nasu, ta bude taro da addu'a, lokacin ta bani sha'awa sosai jin tana futar da kira'a sosai, hakan yasa, Maimartaba yayi mata kyauta nima nayi mata tawa" Shiru yayi yana jan numfashi tsawon minti biyu baice komai ba, yana dan girgiza kansa, yaja tsaki kadan ya bude idonsa sosai wanda suke lumshe yace"inda na kara tabbar da cewar yarinyar nan bata da kirki,lokacin da zata karbi kyautar daga hannuna, in kaga irin kallon da tayi min irin na wulakanci sai ka rike baki,kwata-kwata kanta na wani gefe bataso ta kalli fuskata, ina nan da hotonan in kana bukata zan dauko maka kagani kai ma zakayi mamaki" Shiru Maddibo yayi kawai yana sauraronsa Shi kuma ya cigaba da cewa"a lokacin abun ya bani mamaki, ganin lokacin dana futo daga gida itace ta farko gurin mikewa domin ta ganni, kamar yadda jama'a suke yi amma yanzu gata a gabana tana dauke kai, kawai na shareta amma abunda tayi mun ya bani mamaki, sosai, naje na zauna, Shahid ya nuna min irin hotonan da yayi mana ni da ita, a lokacin na kara ganin, wukantacan kallon da ta din ga yi min,shi kuma Shahid cewa yake wai mun dace da ita sabuda yana ganin kamar "yar wani ce a garim nan kuma yarinyar tana da kyau sabuda haka kawai in shi ga,raina ya baci sosai da maganar da yayi min, wannan shine dalilin batawar mu dashi,domin da muka shiga gida, ya dame ni da zancan ta, fada mukayi dashi sosai, shine dalilin da yasa kaga baka ganshi ba kwana biyu, to wannan shine,abunda ya hadani da ita, sabuda haka,naji bana kaunarta kai kasan halina,in naki mutum to nakishi har abada wallahi" A nutse Maddibo yace"ni dai yanzu hakuri nake baka, maganar nan ta wuce kai kayi laifi,itama tayi laifi, sabuda haka sai ayi hakuri a yafi juna,amma gaskiya banji dadin tofa mata miyau da kayi ba" "Ok yanzu hakuri kakeso inje in bata kome"? A'a ni bance ba,kawai ka kiyaye ko da nan gaba zaku hadu,tunda dai kasan babu abunda zai hanani auranta,sai dai idan mutuwa nayi" "Wannan kuma abunda ya shafe ka ne, wannan yarinyar bana fata in sake ganinta,har abada kai ma ina me baka shawara ka janye maganar auranta,zai fi maka alkairi,kanemi yariyar arziki domin samawa " yayan ka Uwa ta gari" Cikin Sanyi murya Maddibo yace"Addu'a kawai zaka taya ni dashi a kanta, amma maganar gaskiya Allah ya jarrabe ni da kaunar ta, kuma kai ne kake mata kallon mara tarbiya Balaraba yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, abunda yasa ake mata kallon mara tarbiya dalilin sana'ar ta ne kawai" "Ok me yasa baza ka hanata talla a cikin kasuwa, in dai da gaske kana sonta,sai ka hanata fita kawai ka killace ta guri guda,kai kanka kasan al'adar cikin gidan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108