Skip to content

Chapter 64

Chapter 64

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,260 words 0 views Progress saved
Download Book

k'ara yi min magana makamanciyar wannan, duk sanda kika k'ara ranki sai ya b'aci, sosai daka ke har "yayan naki da kike ganin kamar bani ne na haife su ba" Sunkuyar da kai tayi ranta yana suya sosai tace"Allah ya huci zuciyarka" Shiru yayi mata na minti biyu ya cigaba da cewa"Duk cikin "yayan naki wacece tazo tai min gaisuwar Moddibo, ko da yake ai ban isa ba,tunda bani da Iko dake dasu,sai abunda kika tsara musu shi zasuyi ai kun kyauta" Cikin sauri tace"Allah ya gafarta maka, duk babu wanda be zo ba a cikinsu,duk sunje sun yiwa Waziri gaisuwa,ko wacce ta tafi gidanta gudun fad'an ka" "Saboda haka kika tsara musu cewar Waziri ne Uban Yusuf bani bane shiyasa bani da matsayin da zasu zo su gaishe ni balle suyi min gaisuwa, sun kyauta" Ya karashe maganar cikin b'acin rai! "Allah ya huci zuciyar ka" Tafad'a muryarta na rawa ganin kwab'arta tana so tayi ruwa. Har ya wuce zai tafi yaja ya tsaya yana kallonta yace"Nasan duk akan wa kike wannan abun wanda har kike nema ki sheganta min "yayana, duk cikin " yayan da na haifa babu wanda na ware nace shi nafi so kowa ina sonshi tunda nine na haife shi, Almansur Sarki!shine d'ana namiji guda shine kuma magaji na insha Allahu,saboda haka in zaki kwantar da hankalin ki ki kwantar da hankalin ki" Yana gama fad'ar maganar shi ya futa a nutse. Hajiya Kulu zaman durshen tayi kan kilishin dake malale tsakiyar d'akin wasu zafafen hawaye yana zubo mata, wai me yasa bata haifi d'a namiji bane?wai me yasa duk "yayanta suka zamo " yaya mata,? Ita kad'ai take tambayar zuciyarta, yanzu ta tabbata kenan Mama Fulani tayi nasara a kanta,tunda har ta haifi d'a namiji kuma takasa nasara akansa da ita kanta Mama Fulani, wata wawar ajiyar zuciya ta sauke ta mik'e zumbur!tana surutai falonta ta futa inda Hadiman ta ke zaune,suna jiran futowar ta, daga bakin Kofa ta tsaya ta kira Jakadiyarta me suna Ladi, suka shiga d'aki tare, wani irin zama tayi kan wani tuntu tace"Ladi duk wani shiru da k'uli da mukayi shekara da shekaru ina ganin duk sun karye,dole ne yanzu mu sake sabon lale,me zafi!domin inaji ina gani zamu zama "yan kallo a gidan nan dani da " yayana" *Muje zuwa* *Comment Vote and Share* [13/08, 19:27] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` _Alhamdulilahi, Ina taya d'aukacin alummar musulmi murna za gayowar wannan wata me albarka,ina fatan Allah ya nuna mana na shekarun gaba, ubangiji Allah ya shafe mana zunuban mu_ _____________________________ *🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂BANI BANE🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂* _(Zargina ake_) ~BY: MAMA QUEEN~ *💫DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION*💫 *NOTE* Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark'akiya,rikitarwa dad'i sauransu..... _Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_ Whatsap numbar 07061553385 *Karku bari abaku labari* _________________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿72* Jakadiya Ladi ta gyara zama sosai gaban uwar gijiyarta cikin sigar munafurci da iya kitifi tace"Allah ya taimaki uwar d'akina,dama abunda nake taso ki gane kin kasa fahimta,ai tuntuni ni na riga nasan abunda kikayi ya daina tasiri kan me Martaba,amma yanzu ga shawara" Gyara zama Kulu tayi tace"Ina sauraranki tabbas nasan shawarar ki me kyau ce" K'asa-k'asa Ladi tace"Me zai hana yanzu mu dawo kan shi d'an nasa wanda ya k'wallafawa rai,tunda dai,asiri baya cin mahaifiyat tasa kuma baya cin me Martaba, ina ganin haka shine abunda ya dace muyi" Kulu ta sauke ajiyar zuciya tace "Wannan shawarar taki itace abunyi, ni in san samu ne ma dukaninsu inga basa motsi a duniyar nan,saboda basu da wani amfani" Jakadiya Ladi tayi wani munafukin murmushi tace"Wannan aiki naki da kika d'auko me girma ne uwar d'akina,amma duk bazai gagara ba, a kwai wani d'an bori dake can lakwaja,shi zanje in d'auko zai yi miki aiki sosai,amma gaskiya dole za'a bawa aljanunsa me k'afa biyu sannan aiki zai ci" Cikin gadara Kulu tace"Ko me k'afa hud'u suke so za'a nemo abashi indai bukata zata biya" Ladi tace"Allah ya taimake ki kin san me ake nufi da me k'afa biyu kuwa" Girgiza kai Kulu tayi cikin izgili! Jakadija Ladi tace"Me k'afa biyu yana nufin mutum kamar ni da ke" Babu wata fargaba Kulu tace"Ai shine nace miki ko k'afa hud'u suka nema ni zan basu domin buk'ata ta biya" Ladi tace"Allah ya taimake ki nasan zaki iya ai,gobe idan Allah ya kaimu zan tafi in zo miki dashi, saboda haka sai a ta nadar masa masauki" Kulu tace"Babu damuwa duk wannan tunda a kwai d'akuna nan b'angaran yanzu babban k'alubalen shine yadda za'ayi ya shigo gidan" "Ranki ya dad'e zan bashi tufafi irin na hadimai na gidan nan sai ya sanya kawai in ya shigo su saje" "Yawwa wannan shawarar taki tayi" Kulu tafad'a tana gyara zamanta. Nan suka zauna suna kullu yadda abun zai kasance . **** Lokacin da me Martaba ya shiga fada ta cika sosai abun mamaki Sarki! Ya gani zaune gefen Galadima yaji dad'i sosai d'aya gefen ya kalla yana laluben Waziri babu shi babu Alamarsa. [14/08, 14:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` *🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂BANI BANE🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂* _(Zargina ake_) ~BY: MAMA QUEEN~ *💫DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION*💫 *NOTE* Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark'akiya,rikitarwa dad'i sauransu..... _Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_ Whatsap numbar 07061553385 *Karku bari abaku labari* _*BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿73* Zama yayi kan kujerarsa, suka fara gaisawa da jama'ar dake zaune a fadar,bayan angama gaishe-gaishen ne, me Martaba ya umarci jakada ya je ya kira Waziri,cikin sauri ya tafi, wajan minti goma sai gashi ya dawo,ya zube gaban me Martaba kansa a sunkuye yana jin nauyin fad'a masa abunda Waziri yace"Sai da ya nisa tukkuna yace"Allah ya taimake ka yace"Ace maka bazai zo ba" Shiru na minti goma me Martaba be ce komai ba, kawai a kafara gudanar da al'amuran da suka dace, kwata-kwata Sarki! baya jin dad'in zaman fadar saboda b'acin rai da damuwa da yake ciki,gashi ya fuskanci mahaifin nasa ma yana cikin damuwa ko ga yanayin fuskarsa ma,ta nuna alamu, haka dai ya d'aure har lokacin sallah azuhar yayi kowa ya mik'e domin yin sallah, tare suka fito daga massalaci da me Martaba, kai tsaye Shashen Mama Fulani suka nufa, suna tattauna,wasu muhimin abu da ya shafesu. Mama Fulani na zaune a farlo ita da Jakadiya Shafa'atu, Sarkin k'ofa ne ya shigo ya sanar mata da shigowar me Martaba, kafin kace kwabo bayin dake gurin kowa yayi nasa guri,har Jakadiya Shafa'atu. A nutse suka shigo Mama Fulani ta gyara masa gurin zama tanai masa barka da shigowa zama yayi sosai da murmushi a fuskarsa suka gaisa,duk b'acin ran da yake ciki idan yazo gareta sai yaji wata sa'ida a ransa. Sarki!ya gaida mahaifiyar tasa a nutse, tace"Kai kuma sai yau ka shigo ko,

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108