Chapter 37
Chapter 37
yayi kad'an yace" ni narasa abunda yake damun wasu matan wallahi, kawai sai tace ka aure ta baka santa,baku taba mu'amala da ita ba, tayaya wannan abu zai faru" "Humm kai ne kake ganin haka, nasan yarinyar ciki da waje, domin waccan shekarar tare mukayi aikin hajji da ita, kuma wata uku da suka wuce da naje Umara mun had'u da ita, sosai ta nace min kullum tare muke tafiya masallaci, sai dare take kyaleni ta tafi ma saukin su, safiya nayi zata zo ta dame ni, shine dalilin da yasa ko sati daya ban cika ba na tattaro kaya na na gudo bata sani ba, sai dai ta shafa taji ba nanan, kai kanka kasan na tsani ta kura" Dariya Maddibo yasa yace"Wallahi baka da kirki "Yan mata suna sonka kai kana k'insu ko zaka fad'a min dalili" *Comment* *Vote and Share* [13/07, 20:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿48* Maddibo ya cigaba da cewa "yanzu me kace kai akan al'amarin"? " Kai ma kasan halin Baba Waziri,cewa nayi na amunce kawai,ba kaga yadda yake murna ba" "Ya zakayi da rigimar Halisa"? Tsaki! yaja yace" Halisa ba tafi karfi na ba,ina ruwana da rigimar ta tayi, ta gaji, ka manta cewa ba ni ne nace,ina son ta ba, ita wannan din da a ka k'akaba min, sam! ba tai min ba, Siririya ce, babu wani cikar arziki, ka san ba nason mace, haka, dukkanin su babu wacce tai min gwara-gwara ma Halisa tana da wasu abubuwan" Dariya Maddibo yake sosai yace"kana kiran Tafida, da mayen mata,to kai da wane suna za'a kira ka"? Shan kunu! yayi kamar ba shi ba yace"ai gaskiya ce, ganganci ne ka auri mace, wacca baza ka more ta ba,sai dai kai ta fama da kashi da jijiya, wallahi nake fad'a maka,wata macan ko me zaka bata, baza ta yi k'iba ba" Cikin dariya Maddibo yace"kana daga zaune sai zaro magana kake, wallahi matan ka sun shiga uku, kai dai" Tab'e baki yayi ya mik'e tsaye tsaye, yace"babu ruwana dasu a cikin su duk wacce tafi kyautata min itace taurarowa ta" Mikewa Maddibo yayi yace" Zanje fada mu gaisa da Maimarta ba, idan naga da sukuni zan shigar da maganar Balaraba" "Allah ya bada sa'a" Sarki yafada ya cigaba da cewa"nima wanka zan shiga zan futo yanzu" Lokacin da Maddibo ya isa fada, bata cika sosai ba, daga Sarki sai Waziri da Wambai sai Wasu fadawa su hud'u , Maimarta ba yana zaune kan kujerar shi, suna magana da Waziri, duk dai a kan Sarki! ne, Waziri yace"d'azu munyi magana dashi yace ya amunce, yanzu abunda zamuyi shine, zamu aika da takkada gayyata gare ta kan tazo su gaisa dashi, muna bukatar ta zauna tare damu, domin ta koyi irin al'adunmu sabuda kasancewar kowane gari da irin tasu sarautar" Jin maganar da Waziri yake tasa Maddibo faduwar gaba! kalubale na farko kenan, Cikin nutsuwa da dattako yayi sallama fadar kanshi a sunkuye ya zube! yana kwasar gaisuwa Da murmushi a fuskar Maimarta ba yake amsa wa yace"da alamu akwai magana a bakin Ubana, Maddibo d'an Maddibo kuma Uban Maddibo" Murumushi Maddibo yayi ya karasa gaban Maimarta ba kanshi a sunkuye,yace"Allah shi taimake ka, nazo muku da wata magana me muhimanchi ina fatan zaku karb'eta hannu biyu" "Masha Allahu" Maimarta ba yafada ya cigaba da cewa"nasan ko wace irin magana zats futo daga bakin ka mai muhumanchi ce Ubana,ina sauraron ka, tare da sauran iyayen naka" Yafada yana kallonsu Waziri dake zaune duk sunyi shiru Da sauri Wambai yace"kwarai kuwa Allah shi taimake ka, muna sauraron ka" Shiru Waziri yayi irin na kara, amma ya k'agara Maddibo ya fad'i irin maganar da yazo da ita cikin fada wacce ya kasa fad'a masa ita a matsayin sa na wanda ya haife shi, Cikin nutsuwa Maddibo yace"Allah shi taimake ka na samu matar aure insha Allahu, ina so a aika gidan su domin a tsayar da magana" Kafin Maimarta ba yace komai, Waziri yace" "yar wane Sarki ce a fad'in duniyar nan, ina fata bakaje kayi mana jajibe-jajiben " yayan bayin mu, ba wato talakawa" Shiru fada tayi, sabuda Waziri ya karya dokar fada,bai bari Maimarta ba yace komai ba, ya fara magana, daga baya da yage b'arnan da yayi, sai ya d'an runk'ufar da kanshi yace"Afuwa a gafarce ni ranka ya dade" Minti biyar Maimarta ba bai ce komai ba, daga bisani ya d'ago kai a nutse yana kallon Maddibo yace"kaje ka cigaba da neman yarinyar zamu sa a je ayi bunkice, babu ruwan mu, da cewar "yar talaka ce,ko " yar mai kudi ce, ko "yar sarauta ce, duk wannan basa gaban mu, nagarta da kyawawan halaye shi zamu duba, Allah yasa za'ayi damu" daga fadin haka,sai yayi shiru, amma fa fuskar shi babu walwala dalili Waziri ya b'ata masa rai, sam! ya tsani halayen dan Uwan nashi kwata-kwata baya kaunar talakawa, tun jiya yake tunanin maganar da yayi masa akan Sarki! da d'iyar Sarkin Yalwa, yasan da akwai wani abu a b'oye wanda shi Wazirin yake son cika wa, amma koma meye ya barwa Allah domin ya fisu sanin abunda yake lullub'e. Cikin farin ciki Maddibo ya mik'e yana godiya, Maimarta ba ya dakatar dashi da hannu, yace"ka zauna a fada na lura tunda ka dawo baka zauna ba,kai ma ka koyi d'abi'un d'an uwanka, yau in ya zauna a fada gobe ba zai zauna ba" Komawa yayi ya zauna gami da tankwashe kaf'a yace"Allah ya taimake ka" "Ko kana da wani Uzirin ne"? Maimarta ba yafada yana kallon shi " A'a babu wani uziri a yanzu, ranka ya d'ade" Shiru Maimarta ba yayi yak'i sakin fuskar sa,sabuda abunda Waziri yayi ya bashi haushi, nan Wambai ya fahimta yace"Waziri ya na neman afuwa ranka ya dad'e" A nutse yace"Ai ya nuna min bani ne uban d'anshi ba,tunda har ya kasa hakura in fad'i magana sai da ya fad'i tashi" "Tuba nake, a busa kuskure ne,ranka ya dade a gafarce ni" Waziri, yafada yana jin wani mugun bak'in ciki, a zuciyar sa, dole ne ma yasan yadda zai yi ya kawai da mutumin nan daga karagar mulki,tunda ba danshi kad'ai a ka hallice ta ba, shima yana da gadon sarauta kamar yadda yake da ita, babu yadda za'ayi ya dunga nuna masa mulki, amma babban abunda yake bashi mamaki da d'aure kai shine duk sanda yayi niyar aiwatar da wani abu a kansa,daga ya had'a ido dashi sai ya kasa, ya rasa wane irin kwarjini yake masa. Haka fada tai ta tafiya, har lokacin sallahr la'asar, Maimartaba ya mike a nutse domin shiga masallaci, Suna dawo wa fada Maimarta ya aika ai masa kiran Sarki! Lokacin yana wani k'ayataccan lambu wanda yake hutawa, yana kishin gid'e kan wani lallausan kafet,da wani tumto mai kyau da taushi,anyi masa ado irin na sarauta, gefe ga kayan marmari nan burjik, amma ko daya bai dauka yaci ba, yau baya buk'atar kowa ya rab'eshi shi kad'ai ya ke zaune a gurin, wata irin iska na kad'awa mai dad'i, wayar shi ca hannu shi ya kura mata ido ko k'iftawa baya yi, *Niko da san
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108