Chapter 42
Chapter 42
kud'ina, da ya fasa min banki jiya da daddare ya kwashe min" Sallau duk yayi tsuro-tsuro, gwanin tausayi Wani irin kallo yayi wa mahaifin nasa yace"Kai! ya akai ka fasa mata banki ka kwashe mata k'udi? wallahi baba zuciyarka ta mutu, eh! ka cuce mu daka haife mu, ina tur! da futowa ta tsatstson ka!! Kasa cewa komai Sallau yayi duk ya muzanta, jikinshi yayi sanyi k'alau sai ya sunkuyar da kai k'asa "Walidi" da sauri ya daga kai yana kallon inda yaji kiran Balaraba ce tsaye k'ofar d'akinsu, hannu ta d'aga masa alamun yazo inda take, da sauri ya nufi inda take, " ya akayi Gimbiya"? yafad'a yana murumshi, "Nawa ne k'udin? " Wane k'udin kike tambaya"? "Na Uwa! mana,sai a biya ta ta sakar masa wuya" tafad'a tana kallon inda suke tsaye, tana k'ara mamakin rashin mutumcin Uwa! Wata mahaukaciyar dariya Walidi ya kwashe da ita, yace"kinga Gimbiya kar kishiga wannan cakwakiyar babu ruwanki sunfi kusa, tunda ki kaga yayi shiru to ya aikata ne" "Ai ba cewa nayi zan shiga ba, a dai biya ta ta sake shi, tun misalin shida na safe suke abu d'aya yanzu har bakwai da rabi, yanzu kuma zaka ga yara sun fara shigowa siyan a wara, wannan ba mutumci ba ne" Tab'e baki yayi yace"dubu biyar ne" "Shikkenan zan futa yanzu, zanje banki zan ciro k'udi ka f'ada mata in nadawo zan bata magana ta wuce" "Shikkenan Gimbiya, tunda kince zakiyi amma ni da dan tani ne da kin rabu dasu, ai gwara da tayi masa haka,gaba bazai kara aikata wa ba" Lantana idonta a kansu, sai tab'e baki take tana cewa"munafukar banza da wofi kawai, kinibabbiya" kasa-kasa take maganar sabuda batason Walidi yaji "Ke Uwa! sake shi za'a biya ki" Walidi ya fad'a yana cije baki! Hannu daya ta mik'a masa tace"bani in rik'e a hannuna tukkuna" "Dallah! ki sake shi za'a baki an fad'a miki" yafad'a kamar zai kai mata duka, Sakin sa tayi ta matsa gefe tana huci! tace"ina kud'in suke, kai ma zan iya tsine maka akan k'udin wallahi" Dariya yake mata yace" Yo ke Uwa! ai ko kin tsine min tsiniwar ki baza ta kamani ba, sabuda kema, baki bi naki iyayen ba, duk abunda kai sai am maka,Hahahahahahaha! Ya karashe maganar yana wata dariya kamar shashasha. Ya cigaba da cewa, "Gimbiya zata bayar a baki an jima" Jin yace Balaraba zata bayar a bata yasa ta kwantar da hankalin ta ta wuce d'aki tana huci! Sallau kuwa tunda ya samu ta sakeshi sai ya sulale ya futa daga gidan kafin kowa ya ankara,haka ya futa baiyi sallah ba. Shamsiyya da Mabaruka har a ka gama masifar suna bacci sai da Uwa! ta shiga d'akin tana kwashe sauran kud'in tanayi tana zage-zage sannan ne suka tashi, Shamsiyya tace"wai menene ina bacci ina jin hayaniya a gidan sama-sama, na d'auka ma mafarki nake" Nan Uwa! ta kwashe komai ta fad'a musu, suka had'u da ita suna zagin Baban na su. Balaraba kuwa wanka tayi a gurguje ta sanya doguwar riga ta atamfa, me kalar blue da yellow mayafi mai girma ta yafa ta sanya takalmi plate mai a don duwatsu, tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ta kuzo a gani ba, su Sadiya sun shirya tsaf cikin uniporm dinsu na makaranta, ta hada musu shayi mai kauri ta basu sannan ta dafa musu indomee cikin kula, tare suka futo ta kulle d'akin ta nufi d'akin Iya, tana kwance kan katifa, da alamar ta fara samun saukin jikin ta, suka gaisa cikin mutumci Balaraba tace"Iya jiki yayi sauk'i ko" "Alhamdulilahi jiki yayi sauk'i Balaraba, Allah yayi miki albarka, ta cigaba da cewa, kin futo to Allah ya bada sa'a" "Ameen Iya nagode, yanzu ba kasuwa zani ba,zanje in ciro kud'i a banki zan sa a fara neman min gidan haya, ko a bayan layi ne,domin bana so in yi nesa dake" " Yanzu ashe baki bar wannan k'udirin naki ba, Balaraba" Iya tafad'a cikin jimami "Iya kiyi min addu'a kawai zaman gidan nan nagaji dashi wallahi,gwara in tafi in bar musu" "Shikkenan Allah yasa haka shiyafi alkairi" "Ameen sai nadawo" Balaraba tafad'a tana k'okarin tafiya, ta jiyo mitar Lantana, ko waiwaya batai ba, ta futa daga gidan. ***** Kwana yayi yana tunanin ta ina zai fara bunkican Asalin Balaraba, ga Moddibo yau yak'i kwana a shashen sa, ya gudu nasa sabuda tunda ya dawo nan yake kwana, dole gobe kafin ya futa,ya nemi Moddibo a kan al'amarin domin shi kam bai san ta inda zai fara ba, kwana yayi yana mafarkin da yasa bayi kullum, asubar fari ya tashi, yana had'a gumi, mafarkin yau yafi na kullum bashi tsoro, yau ganinshi yayi tare da yarinyar nan mai kama da budurwar Moddibo, yana tara da ita kamar matarsa, abunda bai tab'ayi ba kenan, tunda yake bai tab'a mafarkin wata "ya mace ba, ya san dai shi mutum ne mai yawan sha'awa shine dalilin da yasa ma yake yawaita azimi, domin tsare kanshi, kuma baya tab'a yadda ya keb'ance da mace ko wace iri ce mutukar ba muharramarsa bace, sosai ya ganshi a mafarkin tare da yarinyar suna mu'amula irin ta ma'aurata, jikinshi a mutukar sanyaye ya mik'e ya shiga toilet domin ya tsarkake jikinshi, dole sai yayi wanka, kamar yadda addini ya tanada, bayan ya gama ya d'aura alwala ya futo, jikinshi d'aure da wani k'aton towol mai kauri da tsane ruwa, wani k'arami ne a hannushi yana tsane kanshi dashi, farar jallabiya mai yankakken hannu ya saka ajikinshi had'e da gajeran wando, ya sanya hula irin ta larabawa, a kanshi sai ya zama tamkar wani balaraben kasar Saudia,kalar fatarshi ta futo sosai, ya zura wani farin takalmi ruffafe mai mutuk'ar kyau a kyawawan k'afafunshi, ya nufi massalaci cikin nutsuwa. *Muje zuwa* *Comment* *Vote and Share* [17/07, 21:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿52* Tare suka futo daga massalaci da Maimartaba, cikin nutsuwa suke tafiya tamkar wasu abokai yayin da wasu fadawa suke take musu, baya Waziri da Shamaki ne a bayansu, Shamaki ya kalli Waziri cikin sigar munafuci yace"Allah ya taimake ka, wai yaya kasake har haka tafaru? tuntuni tane fad'a maka wannan shak'uwar dake tsakanin Maimarta ba da yaron nan tayi yawa,kamata yayi ka d'auki mata, a matsayin ka na k'ani gare shi, ka lura da kyau, sam baya baka kulawa kamar yadda yake kula da d'anshi, ko wani abu ne ya faru, in ka lura Maimarta ba baya zartar da wani hukunci sai yasa anyi masa kiransa, kuma duk gaku a zaune a fada, kai da Ciroma da Galadima baku da amfani, nine Shamakin Maimarta ba,nafi kowa sanin shi, tunda kusan kullum tare muke yini a fada, kwanciya bacci ne kawai yake rabamu da shi, ina mai tabbatar maka da cewar in bakai da gaske ba, sai dai kaga wannan Yaro wata rana yana mulkar ka, Allah shi taimakake kayi tunani kan maganar da nafad'a maka" Shamaki ya k'arasa maganar yana sunkuyar da kai, cikin munafurci Ajiyar zuciya Waziri yayi yana kallon Maimarta ba tare da Sarki! suna tafiya a nutse hatta da tafiyar su iri daya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108