Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
Download Book

sai ta ganshi. Gefe can taja ta tsaya domin yadda a ke bangajeta gashi Sam Sam bata son hayaniya da jira da tana da damar tafiya da tayi tafiyarta wallahi domin kwata kwata bata son batawa kanta lokaci sanin da tayi cewar kannanta nacan na jiranta a gida, To ganin yadda makarantar ta karramata a matsayinta na daliba ta farko yasa bataso ta watsa musu kasa a ido Duk a zaton ta Sulaiman Ahamad shine na farko ganin yadda yake da kokari domin ko musa bakace shine yake cinyewa Amma Abin Mamaki sai taji sunanta a farko ,Tabbas ta yadda da kanta tunda Ita kanta tasan tana da masifar kokari domin wani sa'in itakewa "yan ajinsu kari idan malami bai shigo ba ita dai kyaleta da rashin kunyarta da gadara gami da takama gashi ita kuma ba "yar gidan kowa ba! Da kyar bushira ta hangi Sarki! Daga can nesa sai ta riqa mamakin ganinshi jin Balaraba nace da ita ae yaro ne Lallai Balaraba da son girma take cikin zuciyarta tace gaskiya yana da kyau wai!! Dole yaji dakanshi duk da cewa bai fiye haske ba amma kalar fatarshi abin kwatance ce ga wani uban saje da yabi ya kewaye fuskarshi a tsare hade da mitsitsin bakinshi idonshi Manya farare tas dasu sun Dan risina kadan bazaka taba gane girmansu ba sai ya bude masu duka Amma idan ka kalli saman fatar idonshi zaka gane yana da Manyan idanuwa a sabila da dimun'da'iman idan nashi a lumshe yake ba yadda ya bude su sabida shi kanshi yasan Allah yayi masa baiwarsu . Tun kan ta karaso gurin Balaraba take zabga mata harara tace"wallahi Sam Sam ba kuyi ba kun zubar mana da qima kuna mata kuriqa rububin zuwa kallon wancan waishi Dan sarki Mtssss Wallahi babu da Namijin da zanyiwa wannan rawar jikin ba'a haifeshi ba tafada a zafafe tanaji tamkar taje ta gaggaurawa matan dake rububin zuwa ganin shi. Kallonta Bushira tayi tana Mamakin Balarabar da yadda ta dauki kanta ita ba "yar kowa ba I dillalin kashi. Tace"laifi ne Dan munje ke tunda bazaki ba ae shikkenan ,humm gaskiya ya hadu duk da banganshi sosai ba tabbas nasan yana da mugun kyau. Tsaki Balaraba taja tace kyawunshi din baza bai dameni ba ni nan Sam Sam kyauwun wani Namji bazai rude ni ba ko wata sarautarsa tafada tana girgiza jiki gami da ji da kanta Dariya Bushira tayi kadan tace" Wallahi wannan Abinda kekeyi yana mutukar bani Mamaki wai ko Dan kinga kina da kyau ne? Banza Balaraba tayi mata tana hura hanci! Bushira tacigaba dacewa Dan kinsan bazaki taba samun kamarshi bane a matsayin Miji shiyasa kike ta wannan Abin" "Wani kallon Tara shaura kwata Balaraba tayiwa bushira tana ya mutse Fuska tace " Billahillazi kika sake yimin wannan Furucin sai na fasa miki baki ae kin San zan iya ko"! *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š [04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€ *🐾GIMBIYA BALARABA*🐾 πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€ *✍🏻Written by* _*Binta Umar*_ ~*MAMAN ABDUL WAHABU*~ ~*MRS AHAMAD GWADABE*~ _*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_ 08089965176 *πŸ…Ώ6* Bushira tace"idan baki fasa basa min baki ba kya tsoran Allah Mtss ke daga anyi magana sai kiriqa nunawa mutane gadara Aikin kawai! Shiru Balaraba tayi mata ganin rantaya baci Sam bata son bacin ran Bushiran sabida ita kadai ce ta iya zama da ita take jure halinta ,tace"Ai sai ki shige mutafi ni wallahi nagaji da tsayuwar gurin nan wai sai yaushe za'a tashi tunda dai Maimartaba ya tafi ba shikkenan ba kowa sai ya yi nasa guri" Tafada tana wani daga kai! "Sai dai ke kiyi tafi Amma ni bazan biki ba ke kullum ba kya gudun Abin Magana duk da halinki Amma haka A ka karramaki gurin nan gashi kina nema ki watsawa mutane qasa a ido"Bushiran tafada tana dauke kai daga kanta Gaba tayi kawai ta kyaleta tsaye a gurin tace "Sai kin tawo ae wallahi bazan zauna ina bata lokaci Na ba kinsan su Sadiya nacan A takure babu Mai basu Abinc......kafin ta karasa Sallau ya tari gabanta Cikin yaqe yace"diyata yarinyar Albarka ina Alfahari dake" Gabanta ya fadi!! Sai ta dake tace"Kawu Ashe kazo gurin saukar banganka ba sai yanzu" Washe hakoransa yayi yace"ae nazu tuntuni a gaban idona Maimartaba ya fito duk ina kallonshi har ya koma cikin gida yafada yana ta dariya Mara dalili domin kana ganin yadda yakeyi kasan karfin hali kawai yake "Allah sarki Kawu wato kazo Ashe Amma kanajin lokacin da Maimartaba yake fadin ina waliyyina yake yafito domin ya karbar min kyautittika Na kayi shiro ko? Tana sane tayi mashi Magana domin taga Halin da zai shiga sanin da tayi basu da Makiyi sama dashi da iyalinshi duk da yana Amatsayin wan Mahaifinta. Duk sai ya diririce Sabida yasan yarinyar "yar zafin kai ce duk da cewar bata masa rashin kunya Amma yana shakkar ta yasan kallonsa kawai takeyi gashi shi kullum nuna mata yake Ubanta ne shi tunda ba ran Mahaifinta, Amma duk wani hakkinta yakasa daukewa Asali ma da hadin bakinsa A ke muzguna musu a gidan ita da "yan Uwanta. Sai ya hau dudduba jikinsa yace"dube ni fa Balaraba babu sutturar Arziqi kunya nakeji shiyasa ban fito ba"yafada bakinshi na rawa kai daganin yadda ya yi maganar kasan tsari ne kawai da Rashin gaskiya Bata ce komai ba kawai ta hau duba kayan jikinshi. Tace"Kawu kenan kowa ae da sandar hannunsa yake kai duka maye laifin tufafinka yanzu gaskiya banji dadi ba wallahi ni kai dai a guri kowa da "yan Uwanshi da iyayenshi ban dani duk su Kawu Habu da Kawu Maman da Kawu Salisu babu Wanda yazo gurin Harsu Safiya da Mabaruka ma haka ai shikkenan tafada tana daga kafada , Duk sai ya rasa Abin fada Sabida babu gaskiya yace"kin San wa "yan nan basa son Zumunchi kowane shege sai yace kasuwa zai tafi su kuma su Safiya da kike magana a kan su kin sansu da shegen son kudi kamar jaraba suna can suna Aikin A wara da kulelensu kamar ko da yaushe" "To Kawu ina Uwa da Iya su mai yasa basu zo ba? Tafada domin taji mai zai ce domin tasan bata bakinta takeyi sabida tasan bazuwa zasuyi ba Lokacin da sukaji Labarin saukar cewa suka dinga yi ae saukar zuqu ce wannan. Yace "ke ma dai Balaraba kin san wa"yannan tsinannun Matan baza su zo ba su Neman kudinsu ya fiye musu komai ki rabu da waddanan "yan hassadar ,yafada yana kokarin karbar Allon hannunta gami da kyautitikan hankalinshi na kan Mukkalan gidan da shagon sai faman washe baki yakeyi *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š [04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€ *🐾GIMBIYA BALARABA*🐾 πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€ *✍🏻Written by* *Binta Umar* ~*MAMAN ABDUL WAHABU*~ *MRS AHAMAD GWADABE* _*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_ 08089965176 *πŸ…Ώ7* _Bissimillahi_ Sakar mishi tayi tana bin shi da kallo ganin yadda jikinshi yake rawa Humm Kawu kenan tariga ta Fahimchi Abinda yake wa Yace"Diyar Albarka gaskiya ina Alfahari dake da Dan Uwana Ayuba da ya hafeki Allah yajikanshi ya gafarta masa "Ameen

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108