Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,279 words 0 views Progress saved
Download Book

yana taya ta,ita kuma Balaraba sai fad'a take mata. Ko da Sarki! suka sauka k'asa da Halisa, zamansa yayi a inda ya tashi,ta k'araci k'orafe-k'orafen ta,bai ce mata komai ba, haka ta mik'e tana niyyar tafiya ranta duk a b'ace! ya d'ago kai a tsanake yace"koma ki zauna zamuyi magana" Komawa tayi ta zauna, ya aje littafin dake hannusa,fuskarsa babu yabo babu fallasa yace"kin san Gimbiya Azima,"yar Sarkin Yalwa"? Gabanta ya fad'i! jin sunan wacce ya fad'a ita kuwa tasan Gimbiya Azima,domin abokiyar fad'anta ce, basa shiri ko k'adan dalili kowa yana ji da izza! gami da tak'ama. Bakinta na rawa tace"Eh nasanta" "Yawwa itace zata zama abokiyar zaman ki in Allah ya yarda" Wani irin yarrrr! ta ji ajikinta lokacin da taji abunda yace mak'ogaron ta ya bushe k'amas, tace"ban fahimci abunda kake nufi ba" Wani irin kallo yayi mata yace"kin San bana magana biyu, kije kiyi tunanin maganar dana fad'a miki" Kuka ta fashe! dashi kamar wacce a ka aiko mata cewar uwarta ta mutu, tace"yaushe har a k'ulla wannan al'amarin ban sani ba,kuma mahaifiyata bata sani ba,Dan anga cewar ita macace shiyasa har ake abu batare da saninta ba,wannan ai yaudara ce" Cikin kuka ta k'arashe maganar. Ransa a mugun b'ace ya d'ago Kansa ya zuba mata idonsa,masu kwarjini,tuni tayi k'asa da kanta tana sharar hawaye Yace"dukanin ku ke da ita Azimar babu zab'ina a ciki, ke kin kasance zab'in Mamana,ita ta kasance zab'in Waziri, duk zan aure ku ne ba dan inaso ba,sai dai n in cika umarnin magaba tana" Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa na fad'a miki ne saboda ki sani kuma ki shirya, saboda kin fi kowa sanin halina bani da munafurci kuma bana san hayaniya, da fitina,wanda na lura ke haka halin ki yake tada zaune tsaye, idan anjima zata zo nan domin ta kawo min ziyara zan tara Ku guri guda dake da ita,ku fahimci junanku, kar wata b'araka ta futo daga gare ki, nasan halinki, in xaki kwantar da hankalin ki ki kwantar domin ke da ita ba da ku kad'ai zan zauna ba,kin fi kowa sanin yaya tsarin masaraurmu yake" Kuka mara sauti Halisa take,lallai tana cikin tsaka mai wuya, yanzu ta tabbatar da cewar Baba Waziri baya k'aunarta tunda har ya had'a "yar abokinsa aure da masoyin ta, ita da take burin taci lokacinta ita dashi kafin ya kawo wata,tasan ta more kuma sunsha soyyaya, yanzu ko auran a kayi tilas su raba kwana ita da Azima. Tunda ya gama maganar shi,ya kishin gid'e kan kujerar ya lumshe idonsa Allah kad'ai yasan abunda yake damunwa, yana jin kukan Halisa yak'i k'arewa ya bud'e idonsa wanda suka d'an yi ja kad'an, yace" kin cika min kunne fa da gunjin kuka, kije ki tambayi Baba Waziri yadda a kai haka ta faru tunda na lura ke baki da kunya, har kina cewa an yaudare ku" Yadda ya fad'i maganar da yanayin b'acin rai! yasa ta gane tayi kuskure domin Sarki! mutum ne wanda baya saurin nuna b'acin ransa da wuri, in ransa ya b'aci a yanayin maganar sa zaka gane, mik'ewa tayi ta nufi kujerar da yake zaune, ta rab'a jikinta a jikinta harda langwab'e kai, ta rik'e hannusa guda, d'aya, tayi k'asa da murya ta sosai tace" Allah ya huci zuciyar Habibi na, zuciya tana azabtuwa da so da k'aunar ka, shiyasa na rasa tunani na,lokacin da naji wannan maganar,ina kishin ka,mutuk'a bana k'aunar ko wace mace ta rab'eka sai ni,amma ina ganin burina bazai cika ba, Habibi nasan Azima ciki da waje,zata aure ka ne da wata manufa,a zuciyarta, gaskiya banso Azima zata kasance matarka ba, amma tunda haka Allah ya hukunta mama zan cigaba da tayaka addu'a" Yanayin yadda tayi masa magana a nutse yasa yaji ta bashi tausayi, gyaran murya yayi gami da d'an gyara zaman sa,a nutse yace"ki koma inda kike mana, na hanaki irin wannan" Muryar shi bata futa sosai yayi maganar, Mik'ewa tsaye tayi tana gyara alkyabarta tace"tafiya ma zanyi,yanzu sai anjima zan shigo,da kamar k'arfe nawa zata zo"? Tafad'a cikin sigar tambaya. "Hud'u zuwa biyar na yamma" "Shikkenan to" Tafad'a a sab'ule jikinta babu kuzari ta futa daga falon To,can gidansu Balaraba kuwa,babu wanda ya damu da rashin dawowar ta gida da wuri har wajan k'arfe tara da rabi na dare bata shigo gida ba, Iya hankalinta ya tashi ta futo ta nufi d'akin Sadiya matar Kawu suna maganar,can sai ga Sallau nan ya shigo fud'un-fud'un yana sab'a babbar riga, Iya ta tare shi cikin damuwa tace"Sallau har yanzu Balaraba bata shigo ba,babu ita babu yaran" Da sauri ya kalli k'ofar d'akin nata, cikin mamaki yace"to ina ta tafi mutsiyaciyar yarinya,me shegen yawon tsiya,ai gwara in aurar da ita,kar ta jawo min masifa" Lantana ce ta bankad'a labulen d'akinta ta futo da futular k'awai a hannunta, tace"wai zancan me nakeji ne" "Wannan munafurkar ce bata shigo gida ba" Lantana tace"Oho! dai a banza, duk inda ta shiga ta dawo,dole ace da mijin iya baba mune dai tilas d'inta, ehee"!! Sallau yace"ai ko guduwa tayi bazan fasa abunda na shirya a kanta ba, sai na d'aura auranta da Iro" Lanatana tace"kayi min dai-dai, da taje ta jawo mana abun fad'a" Uwa! na daga cikin d'aki tana sako baki, bak'in ciki da b'acin rai yasa Matar Kawu komawa gurin ta, Iya ma d'akinta ta koma tana addu'ar Allah ya tsare mata su Balaraba duk inda suke. Lantana Sallau Uwa su Shamsiiya baccin su sukai babu abunda ya dame su. Sab'anin Iya da matar Kawu baccinsu rabi da rabi ne, saboda fargaba, Asubar fari suka dunga jin bugu, a gigice Sallau ya diro daga gado,babu salati babu komai yaje ya zare sakata, yana hamma! Idonsa duk kwantsa abun k'yamk'yami! d'an aiken gidan me gari ne yazo, Sallau gabansa ya fad'i yace"lafiya dai ko"? D'an aiken yace"me gari yace"kazo yanzu-yanzu me Martaba ya aiko yana neman ku" Saura kad'an ya fad'i saboda razana da yayi,baki na rawa yace"me nayi ni Sallau"? D'an aiken yace"Ai ba kai ka dai zakaje ba tare dashi zaku" Ihu! ne kawai sallau ba kurma ba,ya shige gida cikin tashin hankali! *Muje zuwa* [02/08, 18:14] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ _*DEDIGATED*_ *_TO_* ```RAHAMA ALIYU``` ```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM``` *🅿65* Lantana ce ta futo daga d'aki hannunta rik'e da butar alola, taga Sallau ya shigo wurjajan, kafin tayi magana ya tare,ta yana cewa "Lantana masifa ta same ni ,yanzu aike ya same ni,cewar muzo ni da me gari wai me Martaba yana neman mu" Sakin butar tayi tafadi a gurin saura kad'an zaninta ya fad'i k'asa saboda tsorata da tayi,salati take tana sallalami, cikin tsora tace"Allah yasa ba wani laifin kayi ba" Yace"yanzu dai zanje in ji, d'aki ya shiga yana tashin Uwa,ya fad'a mata halin da ake ciki,ko a jikinta ta koma tai kwanciyar ta Wani kud'addan yadi ya d'auko ya sanya a jikinsa,ya d'auki wata daud'add'iyar hula ya kwafa a kansa ya futo da sauri,har yanzu Lantana na tsaye a tsakar gida,jikinta duk yayi sanyi, tarasa abunyi,ta kalli Sallau lokacin da ya futo,tace"Nifa inajin wannan shegiyar yarinyar nan ce ta ka k'arar ka gurin Sarki kasan ba kunya ce da ita

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108