Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,230 words 0 views Progress saved
Download Book

ya rik'e hannunta yace"nagode Yaya Allah ya biya miki bukatun ki" "Ameen" Balaraba tace ta mayar da hankalin ta kan Iya, tace"Iya sannu da jiki" Kai kawai Iya ta iya d'agawa "Bari in d'auko miki hijab muje Chamis kinji" D'aga kai ta kuma yi a karo na biyu. da taimakon Balaraba Iya ta mike tasa mata hijab d'in ta rok'ota suka futo, Su Sadiya nan suka zauna jiran dawowar su Kasancewar Walidi ya futa daga gidan yasa Lantana yi musu wani kallo shek'ek'e tace"munafurcin banza da wofi, zaki lanjare kice baki da lafiya, duk kuje ku gama munafurcin naku ku dawo ku same ni nice dai Lantana ban can zaba Babu wanda ya kulata cikinsu Uwa! lokacin tana band'aki, sai ita kad'ai a zaune a tsakar gidan, suna futa suka ci karo da Sallau ya dawo,tun daga bakin lungu a kasanar dashi abunda ya faru a gidan, cikin tashin hankali ya shigo gidan, Yaji dad'in ganin ta a sabuda haka sai ya ja tsaya yana surfa mata ashar yace"bantab'a sanin ke "yar daba bace sai yau, duk ikirarin da mutane suke a kan " yayana cewa suna harkar Daba! a she ba haka bane, duk abunda ya faru d'azu ina da labarin sa, to bari kiji wani abu da baki sani ba, duk k'iyayyar da kike wa Iro shine dai mijin ki ko kink'i ko kinso sabuda haka dole ne zakije har d'akinshi ki bashi,hakuri idan kuma kink'i sai dai kije ki nemi wasu iyayan bamu ba, domin ni nan da kika ganni sharri na yafi kala dubu,wallahi duk inda kika shiga,sai naje na b'ata miki suna" Ya karashe maganar a zafafe! Da kyar! Iya ta bud'e baki tace" haba Sallau bai kamata kafad'i wannan maganar ba,kamata yayi kabi ba'asi kafin ka yanke hukunci, me Iro yayi mata har ta d'auki mataki a kanshi, ni duk da akwance nake a d'aki bana jin dad'i hakan bai hanani na jiyo abunda yake faruwa ba, da Iro da Balaraba duk naka ne, in dai adalci ake" "Ke Iya rufe min baki, bana son hauka, me zai yi mata kuwa? wanda har zata d'auki wuka ta cire masa d'an yatsa, wallahi sai kin biya kud'in magani yanzu-yanzu, domin yana can Chamis za'ai masa d'inki, duk abunda ya faru shi Iro da kanshi yaje ya fad'a min komai, ni sam banga wani laifi a nan ba, dan yayi yunkurin tab'a jikin ki sabuda shine mijinki, dama kuma addini ya hallata cewar namiji zai iya tab'a jikin matar da zai aura kafin auren domin ya san wace iri ce matar gudun abunda zai je ya dawo, sabuda haka bayan kin biya kud'in maganin shi zakije ki bashi hakuri har shagonshi, kamar yadda na fad'a a farko" Cikin mamaki Balaraba take kallonshi, jin abubuwan da yake fad'a bata tab'a yadda Kawu Sallau mugun jahili ne ba irin yau, a wace mazahabar a ka yadda namiji ya kusanci mace kafin auransu, itakam bata tab'a jin wannan k'aulin ba, Iya tace"to kayi hakuri mu dawo sai mu yi maganar in sha Allahu zata bi umarnin ka kamar yadda kake so" Kaucewa yayi ya basu hanya yace"kuje ku dawo ku taddani ina nan ina jiran ku" Suna futa shi kuma ya shige gidan yana zage-zage kamar wani mahaukaci, Lantana ta mik'e zaune tana taya shi zage-zage tace"ashe kaji abunda ya faru ko? "E naji ai shi Iron yaje ya fad'amin, duk abunda ya faru,kuma ina shigowa unguwar ake ta tarata ana fad'amin" "Hummm! kagani ai sai ka d'auki mataki akan ta in ba haka ba kuwa sai dai kazo ka tarar ta kashe mu,a gidan dan yarinyar ta zama abunda ta zama, a duniyar nan" Nan Sallau ya zauna kusa da mahaifiyar tashi suna k'ara maimaita maganar, Uwa!ce ta futo daga band'aki hannunta rik'e da buta, aje butar da sauri ganin d'akin Balaraba a bud'e tun dazu Walidi ya bud'e mata, lokacin da zata shigo,gidan sam ta manta bata kulle ba suka futa, kai tsaye d'akin ta nufa, Lantana ta mik'e da sauri tabi bayanta, shima Sallau d'in mikewa yayi ya rufa musu baya, Bunkice suke mata sosai a cikin d'akin sunyi mata filla-filla da kayan sawar ta sun jefo waje, Lantana tace" yawwa Uwa! d'aga katifar nan ko anan take b'oye k'udi ki kwasa maganin dukan d'anki da tayi, aikuwa kafin Lantana ta rufe baki, Sallau ya d'aga katifar da sauri, babu komai k'asan katifar, ya mayar da ita ya aje, dama Balaraba bata wani ajiyar k'udi duk in ta samu na b'ukata ne shiyasa basa taruwa, mafi a kasari ma tafi ajiya cikin jakarta,kuma tana jikinta a rataye, haka suka k'araci bunkucen su basu ga komai ba, suka futo suna ta zagin ta,kamar mahaukata Babu abunda yake damun Iya illa zazzab'i na maleria nan me chamis din ya had'a mata magani yace"dole za'ai mata allura ta kwana uku, Balaraba duk ta biya kud'in me chamis din yace"Iya kinci abunci in ce ko"? "Eh to ba sosai naci ba" Iya tafad'a da kyar! yace "babu damuwa dama illar guda d'aya ce ayi miki allura bakici abunci ba, tunda kinci ko yaya ne shikkenan, nan ya had'a allura yayi mata, suka kamo hanya suka tawo gida,gurin wani mai balango da gurasa suka tsaya Balaraba ta sai mata gurasa da balangu,suka wuce gida, suna shiga soran gidan suka dinga jin hayaniya tana tashi a gidan, Iya tace" wannan masifa ta gidan nan Allah kayi mana maganinta, "Humm Iya ki kyalesu suyi su gama insha Allahu na kusa barin gidan sai kowa ya huta tunda nice basa buk'ata, duk kuma wanda ya zalunce ni Allah zai saka min" Balaraba tafada lokacin da suke shiga gidan, kayanta tafara cin karo dasu a watse a tsakar gida wasu a gurin rijiya wasu a kusa da shara, Cikin mamaki ta tsaya tana binsu da kallo, dawowar Mabaruka kenan daga talla, tana tsaye ita da Shamsiyya tana wassafa mata abunda ya faru, tsalle ta buga tayo kan Balaraba tace"Allah nagode maka,kullum mu ake kira karuwai, yau gashi yau Allah ya nuna mana karuwa a gidanmu,,zatayi zina da d'an gida, Huuuuuuuuu!!! tir dake da halinki shegiya karuwa" tak'arashe maganar cikin ihu! dama hanya take nema wacce zata ci mutumcin Balaraba sabuda mak'ure ta da tayi a bango kwanaki, kayanta dake watse tabi tana tumurmusawa da k'afafunta, babu abunda Balaraba tace, takama hannun Iya ta shigar da ita d'akinta,sannan ta futo su Sadiya na biye da bayanta, suka shiga d'aki, zama tayi gefan katifa ta zabga tagumi hannu bibbuyu, tunani take yaya zatayi da rayuwar ta da ta k'annenta, sai yanzu tafara jin rad'adi a kafarta, kallon k'afar tayi taga ta kara tasawa alamun k'ona, ita ba wannan ne abund ya dame ta ba yadda za'ayi su futa daga wannan jarabar itada "yan uwanta, shawarar da ta yanke kawai shine ta nemi gidan haya su bar gidan, shine mafuta duk wanda zai yi zargin ta, ya dad'e bai yi ba,dama kuma a cikin zargin mutane take, kullum, tun tana jiyo motsin da hayaniyar su Lantana ta a tsakar gida, taji shiru da alama kowa ya shiga d'akinshi, buta ta dauka ta futo tsakar gidan domin ta daura alwala, suka ci karo da Sallau ya shigo gidan afujajan, gabanta ne ya fad'i sai tafara karanta innalillahi a zuciyar

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108