Skip to content

Chapter 43

Chapter 43

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,220 words 0 views Progress saved
Download Book

ce sai dai kasaitar Sarki! har tafi ta mahaifin nashi, "Akwai abunda nake shiyarwa,domin Ni kaina wannan abu yana damuna Shamaki, tare nake so mu had'a baki da Ciroma amma yak'i bani goyan baya a kan k'udirina kansu,to amma yanzu na samo mafuta, kwananan buk'ata zata biya kan Yaron shiyasa duk wata giggiwa da yake nake d'aga masa k'afa sabuda nasa ta lokaci kad'ance, zai shafe a duniya kamar ba'ata b'ayin sa ba a doran duniya" Waziri ya k'arasha maganar yana kallon su ganin yadda hadimai suke zubewa k'asa suna kwasar gaisuwa,wasu tun daga nesa in sun hangosu suke zubewa k'asa kansu a sunkuye, had'e da daga hannu, alamun girmamawa har sai Maimarta ba ya shige suke mike wa tsaye, wannan abu yana mugun b'atawa Waziri rai, shima suna gaishe suna bashi girma a matsayinsa na Waziri,amma baya gani, yafi son suyi masa gaisuwa wacce tafi ta Maimartaba da d'anshi Sarki! Maganar da suke tattauna tsakanin Maimarta ba da Sarki! yana sanar dashi cewar zai fara bunkice da ya umarce shi, amma yana neman alfarmar ya barshi ya futa da Normal kaya,domin yin basaja, kuma bayaso a had'ashi da kowane bawa, in ba Direba ba, wato mai janshi a mota Maimarta ba,yace"wannan tunanin naka yayi kyau sosai sabuda idanun jama'a wani ma in ya lura ga daga inda yasa ake bunkicen zai iya fad'in k'arya a kan yarinyar, dan haka duk in da ka tsara kaje kayi, Allah ya kiyaye hanya" Sarki! yaji Dad'in amuncewar da Maimarta ba yayi, domin a k'aidar masarautar su, basa futa da Tufafi dole sai na sarauta in kagansu da Normal tufafi to a cikin gida suke. Tare suka shiga b'angaran Mama Fulani domin yau Maimarta ba a gurin ta yake, ta k'ofar baya ya shiga, shi kuma Sarki! ya shiga ta k'ofar da kowa yake shiga, Tana zaune kan wata katuwar daddamu, ja mai adon fulawa, gefan tumtum ne manya-manya guda uku, gabanta kuwa shak'e da kayan marmari, tana sanye da wata lifaya mai tsananin kyau da tsad'a hannuta rik'e davwani k'aramin carbi mai kyau sai kyalli yake, tayi kyau har tagaji Mama Fulani kenan mace mai karamci da karramawa, mace mai kaunar talakawa da nakassau, Jakadiya Shafa'atu ce zaune a gabanta,da mufuci a hannuta duk da safiya ce amma fiffita take mata, cikin sakin fuska tace"Shafa'atu wai ke bakya gajiya ne"? " Yaya za'ayi in gaji da hidima da uwar d'akina" Jakadiya Shafa'atu tafad'a tana sunkyar da kai, Shiru Fulani tayi kawai tana mamakin karamcin Jakadiya Shafa'atu, macace mai dattako da sanin ya kamata, duk wasu munafurce munafurce da ake a gidan babu ruwanta, an sha had'a baki da ita, domin cutar da ita, tana kare ta, domin farat d'aya bata ce musu bazata yi ba, ko magani suka bata sukace ta sanya mata a abunci sai ta karb'a da yarjejeniyar zata aikata, tana ganin sunbar gurin zataje ta zubar,kuma tazo ta fad'a mata cewar ta dage da addu'a, tana da mak'iya sosai a gidan, ko Waziri yaso ya had'a kai da ita lokacin cikin Sarki! tak'i yadda , shiyasa sam batada farin jini a cikin "yan uwanta har kullum suna kiranta da munafuka, ta sha hak'o tarin layu da hade da bak'in gashi irin na bunsuru, a harabar shashen Fulani sai dai kawai taje ta k'ona, ko kuma ta kaisu can wajan dukonan gidan suyi masu futsari, a kwai lokacin da Uwar gidan Maimartaba ta aiko Jakadiyar ta da wata bak'ar kaza, an cire mata kai, sai digar jini take, gashi an farka cikinta, anzuba layo suma an d'inke su da bak'ar fata, an saka a cikin kazar an d'inke da bakin zare, can wani lambu taga ta nufa, sai ta bita a baya tana kallonta tana tona rami, mai zurfi tayi saurin sa kazar a ciki ta mayar da k'asar ta rufe gurin, sauri-sauri tabar shashan dan kar a ganta ko gama futa batai ba taje ta tone gurin ta futo da kazar, ta bude cikin ta ta zazzago layun, nan ta tara ice ta had'a ta kone su tass! yana mamakin rashin imani irin na Uwar gidan Sarki, wato Kululu mai d'akin kudu, haka suke kiranta To duk irin wadan nan abubuwa suna faruwa, a cikin gidan, duk abunda Allah ya nuna mata irin wanda ake kullawa a gidan tana k'okarin ganin ta kare Uwar d'akin nata, *Wannan shine karamacin Jakadiya shafa'atu a gurin Mama Fulani* Da sallama ya shiga d'akin. "Barka da shigowa Magajin Sarki Allah ya ja zamanin Uban d'akina" Jakadiya Shaf'atu ta fad'a kanta a k'asa, A nutse ya zauna gefan mahaifiyar tashi, yace"barka kadai, fatan kun tashi lafiya"? "Lafiya lou alhamdulilahi" tafad'a tana kokarin mikewa da niyyar futa dama indai ya shigo takan basu guri ne su gaisa, sosai sai bayan ya futa take dawowa, Cikin sakewa suka gaisa da mahaifiyar tashi, tace" nasan da akwai abunda ya kawoka tunda naganka yanzu da safe, ina sauraron ka" Fuskar shi a sake, yace"Mama lafiya lau, na shigo mu gaisa ne" Harararsa tayi kad'an tace"yayi kyau, yau an tuna dani kenan, ai ina lissafawa, yau kwananka uku, rabon da ka shigo min nan tun sanda nayi maka maganar Halisa" "Mama ba haka bane, wallahi Moddibo ne yake zuwa yana takura min shine yake hanani futowa" "Babu ruwan Maddibo yaron arzik'i kullum sai ya shigo da safe mun gaisa, kwanaki ma da yaje can gurin yarinyar da zai aura,har abu ta bashi ya kawo min, kai ka tsaya muskilanci, in anyi maka maganar aure sai ka tsiri kauracewa mutane" "Mama kiyi hakuri maganar Halisa ta wuce, tunda na amunce,bayan itama Baba Waziri jiya mun zauna dashi, akan Maganar Azima" yar abokinshi Sarkin Yalwa, na kuma amunce zan aureta domin na faranta muku rai" Sakin fuska tayi sosai tace"naji dad'in wannan abu, Allah yayi maka albarka, ya taya ka rik'o" "Ameen, ya rabbi" Yafad'a ya da cewa, Mama har yaushe kuka saba da budurwar Moddibo da har take miki aike, haka"? "Tun ranar da Moddibo ya fara sonta, nake da labarin ta a gurinshi, kuma itama tana da labarina, mutukar yaje, gurin sai ta bada abu an kawo min" Shiru yayi na munti biyu yana nazarin maganar da tayi, A nutse yace"na lura kema kin yaba da yarinyar tunkafin ki ganta, Maimarta ba ma na lura ya son al'amarin, Moddibo ya b'oye muku wani abu wanda baya son ku sani a kan ta, yanzu halin da ake ciki Maimartaba ya turani bunkice a kanta" "Gaskiya banaji yarinyar tana da wani aibu, domin har waya munayi da ita wani lokacin in yaje gurinta, ya kan kira waya ya bata yace mu gaisa,ko ga muryar ta nasan yarinya ce me kamun kai" Shiru yayi, daga bisani yace"Mama yanzu ace kamar d'an nan gidan yaje ya auro "yar bakin kasuwa mai sai da abunci a titi, Mama wai Moddibo ya rasa yarinyar da zai so sai wannan yarinyar ni nafi kowa sanin wacece ita" Murmushi fulani tayi tana girgiza kai tace"ta yaro kyau take bata k'arko, meye laifin ta ai ya fad'amin komai a kanta, yarinyar neman na kanta take, kaga na d'aya dai bata sata bata maita, bata zina, yanzu babban abunda za'a bunkita a kanta shine asalin ta Shikkenan, ai duk inda mutum yake yana tare da baiwar shi" Tab'e baki

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108