Chapter 36
Chapter 36
ya kai wayar Maddibo hannun mace, kwata-kwata bai dauki muryar ta ba, Gabanshi ya fadi kad'an,tunowar da yayi yanzu haka Maddibo yana gurin yarinyar nan me abunci, sabuda da zai tafi ya fada masa. Muryar shi ya bude sosai sauti,da a mo suka bayyana, yace"Wacece keee? ina me wayar"? kitttt!! ta kashe wayar ta mikawa Maddibo, cikin dauriya tace"kiranshi a waya bashi ne zai sai in hakura,kawai ka kawo min shi nan" Tafada cikin bada umarni" Girgiza kai yayi kawai yace"ta kwana gidan sauki insha Allah zan kawo miki shi nan" Sakin jiki tayi suka cigaba da hira cikin nishadi cikin zuciyar ta kuwa murna take ta kusa daukar fansa a kan abunda Sarki! yayi mata. *Ni ko nace anya zaki iya kuwa Balaraba,amma dai muje zuwa😀* Bangaran Sarki! kuwa kashe wayar da tayi, yayi mutukar bata masa rai sosai,domin ya tsani yana waya a kashe masa, ranshi a mugun bace! ya fara kiran wayar, lokacin Maddibo ya kashe, sabuda ya san dole zai kara kira yaji ba'asi sabuda yasan Wayar sa ce, *Comment* *Vote and Share* [13/07, 06:19] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®REAL BINTU BATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*Zamani Writes Association*_🤝🏻 _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` *🅿47* ```Bisimillahir-rahamanir-rahim``` Sau uku yana kiran wayar bai dauka ba,gashi ta na ringin, amma sabuda tsabar rainin hankali irin na Maddibo yaki dagawa,kashewa wayar yayi ransa a bace, yanzu ya tabbatar da cewar Maddibo ya kira wayarsa ne domin ya bawa yarinyar tai masa wulakanci. Sai kusan Sha biyu da rabi na rana Maddibo ya yi wa Balaraba sallama, har inda yayi parking din motarsa ya ta rakoshi, mutane suka dinga bunsu da kallo, wadanda suka san Maddibo suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa. Balaraba, Zuciyar ta ta amunce da Maddibo sabuda kyawawan halayen sa,ta lura ya san abunda yake,a rayuwa, zata iya auransa, zata cigaba da addu'a Allah ya yi mata zab'i mafi alkairi a gareta, amma duk da haka ta nan a kan bakanta, ba zata nuna masa yardar ta da wuri ba har sai ya kawo mata Sarki! tarama abunda yayi mata. Sosai Sarki! ya nunawa Maddibo bac'in ransa a kan abunda yayi masa, yace"dan tsabar rainin hankali,ka kira waya ka bawa wata, ina magana,a kashe min waya,kar ka k'ara yi min haka" Ganin yadda Sarki! yake masa hayaniya yasa yayi masa shiru har sai da ya yi mai isarar sa,sannan Yace"in kagama fadan sai ka saurare ni" Ko kallonsa baiyi ba, ya cigaba da karka'da kafar sa, Maddibo yace" tabbas Na kira wayarka, kuma na bawa Balaraba, sabuda ina so in dai-dai ta alakar ku da ita, ni nakasa gane, wace irin gaba ce a tsakanin ku, yanzu da zan tawo ma tace in gaishe ka" Ya karashe maganar yana satar kallonsa, ganin ko kallonsa bai yi yasa ya cigaba da cewa"ga hotonan da nayi mata ma"nuna masa wayar yake, wai ya kalla, shi kuwa ya wani sha kunu yak'i kalla sai ma ya dauki tashi wayar dake gefe a jiye ya hau latsawa, Maddibo bai yi zuciya ba, yace"Mutumi na kalli nutsuwa da kamun kai gurin yarinyar nan dan Allah" Kamar da dutse yake magana, Sarki! ya share shi, Girgiza kai kawai yayi yana murmushi, ya aje wayar kan kujerar ya mike ya nufi bedroom din Sarki, domin yin wanka, badan baiyi da safe ba,kawai shima yanayin sa kamar na Sarki! ne baya son zafi,kullum cikin wanka, duk da haka Sarki ya fishi, sabuda shi ko da sanyi ne, sai ya kunna AC sannan yake iya bacci. Minti biyar da ta tashin Maddibo, ya dago kanshi yana kallon wayar Maddibo dake aje kusa dashi, a zuciyar shi, sai yaji yana son yaga hotan Yarinyar, har ya mika hannu zai dauki wayar wata zuciyar tace masa,me zakayi da hotanta, yarinyar da ta zage ka, kawai sai ya dauke hannushi yq cigaba da duba wayarsa yana jin wani abu cikin ransa a game da yarinyar, Kasa hakura yayi ya mika hannushi a karo na biyu ya dauko wayar, ya fara dubawa, Shagala yayi da kallon hotonan,Sosai yake kare mata so yake ya hango wani abu na aibu a tattare da ita bai hango ba, Jikinshi ne yayi sanyi, sosai tabbas wannan yarinyar itace wacce yake gani cikin mafarkin sa, da sauri ya dauki wayar sa a gurguje a tura hotonan cikin wayar sa baya so Maddibo ya futo ya same shi yana duba masa waya,aikuwa motsin sa yaji yayi sauri ya mai da wayar ya aje inda take,Allah yasa ya gama turawa Cikin jallabiya me yankakken hannu ya futo, ya zauna kusa dashi, da murmushi a fuskar sa yace"Mutumi na ina labari, ya kamata fa ka dai na wannan fushin domin auran Balaraba babu fashi" yafada yana dariya, ya cigaba da cewa"kai nifa daga yau na zama Balarabe,na Balaraba,kaga wanda zai yi mana wak'ar bukinmu ya huta" Dariya ce ta sub'uce wa masa bai shirya ba, yace"Wallahi kasa ni nayi dariya, ban yi niyya ba naji haushin abunda kayi min d'azu" Shima dariyar yake yace"ko dai naji haushin abunda kayi min jiya, haka kawai, zaka sanya ni a kwana, badan na buga sammako naje na wanke kaina ba, a gurin ta, da tuni sai dai in ga ana yi" Gaskiya ina son yarinyar nan sosai, ka dubi Allah ka tayani sonta, ka sauke duk wani abu dake damun ka a kanta" ya karashe maganar yana kwantar da kai. Tab'e baki yayi hankalin shi na kan wayar sa yace"kai ka kyale ni don Allah, kowa yaji da tasa matsalar, meye alaka ta da ita,da zaka ce dole in saki jikina da ita, ni babu ruwana, tunda kana ganin zaka iya zama da ita,Allah ya sanya al'kairi amma a zuciya ta sam ba nai maka sha'awar ka aure ta" "Meye dalilin ka na fadin haka"? " Sabuda yarinyar bata da kunya" yafada kai tsaye, ya cigaba da cewa"sam baza ka iya da ita ba,a yanda kake salo-salo, wannan yarinyar, in ta fuskanci irin son da kake mata, wata rana sai ta sanya ka kuka" "Ba dai Balaraba ba" Maddibo yafada da sauri yace"kaine kake ganin haka,sabuda rashin jituwar dake tsakanin ku amma nasan Balaraba, tana da ilimin zama da miji" Murmushi yayi yana girgiza kai yace"Shikkenan,Allah ya sanya al'kairi, yanzu ta yaya zaka fara,kasan dai dole ka fuskanci kalubale,gurin manyan mu,mutukar sukayi bunkice suka fuskanci yarinyar "Yar.... Shiru yayi bai karasa ba, ganin Maddibo ya sha kunu! sai ya fashe da dariya yace" Gaskiya zanga irin love din da zaka dinga zubawa da yarinyar nan, na fuskanci ka zarme da yawa wallahi, ni ban ga abunda yake rud'ar ka ba,a gurin ta ba yaga hasken fata" Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke yace" babu wani farar fatar ta dake rud'ata kawai na duba nagartar ta ne, maganar ta yaya zan fara, me sauki ce, kai tsaye me Martaba zanje in samu da maganar,nasan abun zai zo da sauk'i dama matsalar na gurin Waziri,dole zai k'alubalanci abun" "Yayi, har ka tuno min da maganar mu dashi d'azu da safe, kasan abokin shi Sarki Yalwa, ko"? " Eh mana" "Wai yariyar shi ce tace tana so in aure ta, in had'asu da Halisa, shine da kiran da yayi mun da safe" "Dariya Maddibo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108