Skip to content

Chapter 97

Chapter 97

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

having our dinner outside today dan haka ki huta yau". "Toh" nace kawai ina jin dad'in cewa zamu fitan da yayi,nan ya zauna muna dan hira jefi-jefi har aka Kira sallah magarib.tashi yayi ya shiga bathroom dina dan yin alwala na bishi da kallo hankali tashe saboda na shanya su panties dasu bra dana wanke dazu ban kwashe ba dan koda na shiga alwalan la'asar basu gama bushewa ba,aiko kaman in tashi in kamo shi nake ji sai dai babu dama. "Shikenan ya gama gane min sirri" nace kaman zan fashe da kuka.shi kuwa yana shiga bathroom din sai da ya lumshe ido saboda kamshin sabulai da nake wanka duk sun kama bathroom din ga Kuma turaren wuta da nake sakawa shima, tsayawa yayi Yana karewa bathroom din kallo kasancewar yau shine karon farko daya fara shiga, gashi nan fes komai a kimtse a bushe. Har ya fara takawa zuwa gaban sink da niyyan yin alwala karaf idon shi ya sauka kan shanya da nayi kaman Wanda aka sakawa magnet ana jan shi zuwa gare su haka ya karasa yana kallon su kaman bai taba ganin abu makamancin su ba. . Hannu yasa yana duba size d'in cikin mamaki ya sake tare da toshe baki yana dariya" wai dama haka yarinyan nan take ban tab'a gani ba,koda yake suna cikin kaya tayaya zan gane" duk shi kad'ai yake surutan sa a bayin yana mamakin ya akayi bai sani ba all this while,can kuma ya tuna ashe fa ko eye pencil bai saya an saka a lefe na ba,sai yaji Kuma babu dad'i " all this are fake zan hado mata nawa da kaina" yace yana nufan sink din ya fara alwala murmushi bai bar fuskan shi ba. Ni Kuma ina zaune ne kawai amma gaba daya hankali na baya tare da ni I was thinking maybe yana can yana kalle min sirri shiyasa ya dade,ina cikin maganan zucin sai gashi ya bud'e kofa ya fito.wani irin kallo daya min yasa na dauke Kai na da sauri ina jin kaman in fashe da kuka saboda tsab na fahimci ma'anar kallon " kiyi sallah sai ki shirya ba zan shigo ba sai bayan sallah Isha'i" gyada kaina kawai nayi ba tare da na kalle shi ba. Dariya ya fara kasa-kasa ya fita na raka shi da harara sannan na tashi ina ta mita na shiga bayin nima,sai da na kwashe shanya na sannan nayi alwalan na fito na shimfida abin sallah na fara sallah ta cikin natsuwa. .. Ban tashi akan sallayan ba sai da nayi sallahn Isha'i da shafa'i da wutiri sannan na shiga wanka,ban wani jima ba kasancewan yace zamu fita,koda na fito ban tsaya dogon kwalliya ba kawai mai na shafa sai powder da kwalli sai wet lips dana gogawa lebe na duk da haka ba karamin kyau nayi ba.parking d'in gashi na nayi na saka ribon na daure su ya koma kaman a cuci maza. Tashi nayi daga nan zuwa wardrobe ina duba kayan da zan saka, akan wani Turkish gown light blue ido na ya tsaya ba wata-wata na fito dashi ya sha stones work tun daga sama har kasa na saka kayan nayi rolling da gyalen, gaban mirrna dawo na fara shafa humra na mai dad'in kanshi sai gashi nan ya shigo bakin shi dauke da sallama. Numfashi na kusan tsayawa yayi na wucin gadi kamin ya dawo daidai ina tasbihi ma Allah da yayi wannan kyakyawan haliita da nake gani a gaba na,sosai yayi wani mahaukacin kyau cikin sabon shiga na wani yadi mai taushin gaske d'inkin half jampa kan shi babu hula sai gashinsa daya gyara sai sheki yake.wani abin mamaki kaman hadin baki shima yadin nashi light blue ne sai kamshi yake zubawa. Ashe shima ta wajan shi abin haka yake dan ba karamin kyau na mishi.ba da kyar ya samu ya tattaro kuzarin sa yace" muje ko" Tashi kawai nayi nazo zan wuce naji Yana" ba dai a haka zaki fita ba?" Kallon jikina nayi ina neman makusa amma ban gani a raina ina mitan shi komai sai yayiwa mutane iyayi. "Pls wear ur hijab,tayaya zamu fita a haka mutane su kalle min ke" yace min a d'an kausashe, juyawa kawai nayi zuwa gaban wardrobe na jawo wani hijab ba tare da nasan wani kala bane na fara warwarewa cikin fushi.ban san lokacin da ya zo ba kawai Jin mutum nayi a bayana daf sosai har kirjin sa da bayana sun hadu,kan shi ya daura a gefen wuya na numfashi sa na sauka a gefen wuya na.ban san lokacin da na lumshe idona ba saboda wani irin yanayi da na tsinci kaina a ciki. Kwace hijabin hannu na da yayi yasa na bud'e ido na sai gani nayi ya ciro wata dark blue irin mai hannun nan ya ajiye na hannu na sannan ya juyo dani ya warware ya fara kokuwan saka min,hannu na kawo da niyyan taimaka mishi ya saka min cikin sauri da sauran fushin sa ya kwabar da hannu na Wanda saida na kwabe fuska dan babu karya naji zafi. Yana gama saka min yaga wani sihirtacaccen kyau da Kamala sun bayyana kaman yanda yakewa kowace mace data saka hijabi,ajiyar zuciya yayi tare da jawo hannuna muka fito yana aiyyanawa a ran shi cewa dole sai ya nemo min nikaf a gaba. Har muka fito compound bai sake min hannun ba kuma bai ce min kala ba, wata mota baka dake pake a gefe ya nufa dani ya bud'e gaban motan ya sanya ni a ciki ya.rufe sannan shima ya zagayo ya bud'e mazaunin driver ya shiga ya zauna yayiwa motan key mai gadi ya bud'e mana get muka fita. Tsit cikin motan baka jin komai sai kira'ar sheikh Sa'ad al ghamdi dake tashi cikin suratul Nisa'i, munyi tafiya mai nisa ba tare da mun kula juna ba domin dukkan mu cikin fushi muka fito amma sauraron kira'ar nan ya saukar mana da natsuwa duk muka rinka sauke ajiyar zuciya akai-akai. D'an satan kallon inda yake nayi cikin rashin sa'a ashe shima ni d'in yaje kallo, wani sasssanyan murmushi mai kara min natsuwa ya aika min nima ban san lokacin da na mayar mishi da martani ba. Dayan hannun shi ya miko ya rike min hannu yana murzawa a hankali yana tuki da dayan hannun, haka ya cigaba da tuki muna sauraron kira'ar har muka iso wani hadadden restaurant dake by pass.da alamu sabon waje ne dan ni ko sunan ban taba ji ba. Shiya bud'e min mota na fito ya kulle motan sannan ya rike hannu na muka shiga ciki,duk inda muka wuce mutane sai sun bimu da ido suke dan ba karamin kyau da dacewa da juna mukayi ba. Bamu tsaya cikin mutane ba VIP naga muka wuce, Kuma shi yafi ko ina tsaruwa sannan babu mutane, wani table dake can gefe muka nufa yaja min kujera na zauna sannan shima yaja ya zauna ya fito da wayan shi yana daddanawa cikin basarwa.hakan da yayi ba karamin kyau ya mishi ba,muna zaune a haka wata waitress mai kama balarabiya tazo table d'in mu ta tsaya tana tambaya me muke bukata tare da miko mana menu. Zafar duk da hankalin shi yana kan wayan shi hannu ya mika

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99