Skip to content

Chapter 85

Chapter 85

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wannan page din naki ne rahama lawal Umar ( ummu Farhan ) kiyi yanda kike so dashi ,alkhairin Allah ya isa gare ki a duk inda kike nagode da soyayyar gare ni Allah ya bar zumunci Ameen* *Sorry last page nayi mistake wajan saka number maimakon 54&55 , na saka 44 &45. *56&57* Baba gaba d'aya jikin shi a mace yake da jin bayanan Abdulbasit tabbas ya tafka kuskure ko Kuma yace yana cikin b'ata, son duniya da sharrin shaid'an ya kai shi ga aikata duk abinda yayi sai dai komai rubutattace ne a kundin kaddara wanda ba makawa sai ya samu mai shi, in da ya kasance mai kulawa da iyalin sa da duk haka bata faru ba. "Na san ba zan kai labari ba dan kashe ni zasuyi kuma nima hakan nake fata domin tunda na rabu da Zareefa ban tab'a jin dad'in rayuwata daidai na second d'aya ba, nayi jinya a boye ba tare da kowa ya sani ba da naje asbiti doctor yace na kamu da ciwon zuciya mai tsanani , shiyasa na kudiri aniyar ganin bayan Emaka kamin in karasa 'yan kwanaki da suka rage min" Abdulbasit ya karasa da fashewa da kuka da bai samu daman yi ba duk watanin nan. Hawaye da suka zubo mishi Baba ya share zaiyi magana Baban Hamis ya kashe system d'in shi ya juyo yana facing abokanen aikin shi da duk suma labarin ya girgiza su kaman yanda ya girgiza shi shima sai dai kowannen su ya shanye abin sa a rai ba zaka tab'a fahimtar komai akan fuskokin su ba. Gyaran murya yayi sannan ya fara magana" duk da komai ya bayyana Ina son shi wannan Abdulbasit d'in ya amsa laifin shi da bakin shi sannan yayi jagora inda za'a samu gang d'in nasu gaba d'aya" babu wani ja suka nuna gamsuwar su kan hukucin da ya yanke bayan dan tattaunawa da sukayi suka wuce offices d'in su. Zafar bai masu isowa gidan mu ba sai da ya tsaya yayi sallahn azahar ya tsaya a wani shopping mall yayi sayayyan kayan masurufi masu yawan gaske sannan ya karaso gida. A waje yanzun ma yayi parking din motan shi ya samu yara a kofar gidan suna jiran a gama abincin sadaka a raba musu yace su shigar da kayan cikin gida nan da nan ko suka fara shigowa da sayayyan da yayi zuwa tsakar gida suna ajiyewa, Inna da fitowar ta kenan daga wanka tana neman Ibrahim ya fara kiran masu karban sakadan tayi arba dasu suna ta shigowa da kaya suna jibgewa hayaniyar su duk ya cika gidan. Cike da mamaki tabi su da kallo kamin ta tambaya Ibrahim da shigowar shi kenan rungume da carton na indomie yace " Innan Zareefa mijin Zareefa ne yace mu shigo da kayan nan kuma yace wai ta fito su tafi". Cizon yatsa Gwaggo Aisha da take leke ta window tayi tana jin bakinciki da takaici ya kume ta dole ne tayi maganin Inna ta shiyasa take ta d'agawa mutane hanci a gidan ita wai 'yar ta na auran mai kudi, Hajara da shigowan ta kenan zata wuce ciki ta ga yanda take rike da labule tana kallon yaran fuskarta kuwa kaman anyi gobara sai cizon d'an yatsa take, kain ta girgiza kawai tayi wucewar ta ciki tana mata addu'an shiriya ta barta anan tsaye tana faman leke . Na fito daga bathroom d'in daki na kenan fuskata na d'igan ruwan alwala da nayi murmushi nake sosai ina jin kaman babu inda na tafi iya watanin nan kaman bacci nayi na tashi haka nake ji domin komai na dakina yana nan tsab ba abinda ya canza kaman lokacin da nake nan. Kara fad'ad'a murmushi na nayi ganin Inna zaune a bakin gadon tana jiran fitowa na kamin in samu daman yi mata magana tace " kina idar da sallah ki fito ku tafi yazo yana jiran ki a waje" a take farar dake fuskata ya kau na kwab'e shi kuwa kaman zanyi kuka saboda ko kad'an ban saka ran tafiya yanzu ba na zata sai dare zai dawo. "Bana son shashanci kiyi sallah ki fito nace sannan kada ki yarda in kara dawowa dakin nan baki fito ba kema kin san sauran" cewar Inna kenan tana barin d'akin, hawayen da suka zubo min na share tare da karasowa ciki na shimfid'a abin sallah na fara sanin halin Inna in ta shigo ba zatayi min da dad'i ba. Har na idar da sallah ban daina hawaye ba dan ko kad'an bana son tafiyan, dole na na fito parlorn Ina sharar kwalla na samu Inna zaune da wani babban leda kusa da ita tace in shiga d'akin ta muyi sallama dasu Maa, jiki ba kwari na shiga na same ta harda 'yan uwan Baba duk sun idar da sallah kowacce rike da carbi suna lazimi. Har kasa na zauna dan niyyan yi musu sallaman amma na kasa furta komai sai hawaye na da suka karu, dariya suka fara min wai Inna ta shagwab'ani dayawa daga baya kuma suka shiga yi min nasiha kan in kara hakuri domin zaman gidan miji saida hakuri, ba gidan miji ba duniyar kanta in kana son kaji dad'in ta toh sai da hakuri da kauda kai. Tun ina kuka har na daina saboda yanda suka kashe min jiki daga nan suka ce in tashi in tafi yana Jira na, tashi nayi na fito Inna tana nan a inda na barta, miko min ledan tayi tace to in tafi mu gaida gida maimakon in karb'a kuka na saka mata ina sai naci abinci domin nayi missing girkin ta. Kala bata ce min ba sai ganin ta nayi da wani madaidaicin warmer ta zubo min abincin sadaka da sukayi tace in naje gidana inci kuma in biya wajan sauran matan gidan inyi musu sallama, dole na karb'a na fito Inna Asabe ita na fara yiwa sallama sai maman Dije ban shiga wajan Gwaggo Aisha ba kasancewar Hajara tace min ta tafi anguwa, a kofar d'akin su na tsaya dan muyi sallama amma sai ta karb'i kayan hannu na ta fara taka min tare muka fito bakin gate. Ta window Gwaggo Aisha take leken mu har muka fita bakinciki kuwa kaman ta had'ye zuciya ta mutu take ji wato na shiga ko Ina nayi musu sallama ita da na raina shine ban shiga mata ba ? Koda yake ta san Inna ce ta kitsa min hakan , ita kuma

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99