Chapter 44
Chapter 44
sun kammala sai bikin kawai suke jira. Da yamma Mom ta kira shi a waya kan ya same ta a part d'in su, amsawa yayi da toh dama ba wani abu yake ba dan haka ya mike ya fita zuwa amsa kiran nata. A parlour ya iske su kusan su biyar da Aunty's d'insa wasu ta bangaren Mom wasu kuma ta bangaren Abba sun baza uban kaya a gaban su suna ta kallo. Gaishe su yayi ya koma gefe ya zauna yana yan dane-dane da wayar shi. "Ya kuma zaka zauna a nesa, oya come closer kayan amaryar ka ne zo ka duba in akwai abinda baiyi ba sai a canza ko" Mom tace mishi hakan. " No Mom ba sai na duba ba duk abinda kukayi daidai ne" yace yana kara gyara zama alamun bashida niyyan motsawa bare tashi. "Kema dai Yaya da son jan magana kike, wannan lefen nayi Imani ko gidan governor zamu iya kaiwa without fargaba balle Kuma wannan 'yar talakawan" cewar wata kanwar Mom da suke kira da Aunty Hauwa dama tana takaicin Zafar daya tashi aure bai nema a cikin 'yan uwa ba yaje ya jajib'o musu 'yar talakawa. "Hmmmmm" Mom tace tana tabe baki alamun maganan yayi mata dad'i. "Ai babu zancen duk abinda akayi dadidai ne kai kafi mu sanin matar ka da abinda take so da Kuma abinda zaiyi mata kyau dan haka kazo ka duba nace maka" Aunty Falmata ke fad'in haka babu alamun wasa kan fuskar ta. Da yake ya san halin ta bata da sauki sam kusan halin su d'aya da Abban shi shiyasa yake matukar shakkar ta, ba musu ya taso yazo ya tsugunna gaban kayan ya fara dubawa kaman da gaske bayan kawai d'agawa yake yana ajiyewa ,su Kuma kannen Mom da ita kanta sai tab'e baki suke na jin takaicin wai sai ya duba. Yana yi yana kallon ta ta gefen ido ganin hankalin ta baya kan shi ya mike ya dawo gabanta ya zauna cikin natsuwa yace " na duba su duk sunyi kyau sosai Baawa". Murmushin jin dad'i tayi tana ajiye wayar ta a gefe sannan ta maido da hankalin ta gare shi ta fara magana tace" yanzu abinda ya rage ga kayan da zatayi amfani dasu a events na bikin ku naka da nata duk suna wajan mahaifiyar ka it's a small gift from me". Mom da taji kaman tayi kuka dan haushi dama niyyan ta in har ba tayi magana ba ta tafi ba zata aika min su ba, cikin dauriya tace" eh gasu nan Son, zoka duba Baawar ka ta sayo muku latest designs na birgewa". Karasawa yayi zuwa inda Mom take nuna mishi ya zauna ya bud'e had'add'un trollys d'in da wani cool suits mai d'an karan kyau ya fara arba wanda kana gani ba sai an fad'a maka kasan mai tsada ne, cikin farinciki ya cigaba da duba su d'aya bayan d'aya ko wani event da kayan da zai saka har zuwa ranar daurin aure kuma kowanne da takalmi da wrist watch d'in shi, godiya ya fara yi mata cikin jin dad'i dan kayan sun burge shi sosai. "I'm glad u like it, sai dai ka manta baka duba na amarya ba" ta amsa mishi itama cikin farinciki, sai da ta fad'a ya tuna da wata amarya, bashi da wani zab'in illa kirkiro murmushi tare da bud'e first 1 dake kusa shi. Sai da yaji numfashin shi ya d'an d'auke na second biyar da yayi arba da wata gown na Indian material sai walwali da d'aukan ido yake ya had'u har ya gaji da had'uwan, daurewa yayi ya cigaba da duba kayan Wanda gaba d'aya anko ne da nashi sai dai a tunanin shi wayan nan zasu fi nashi tsada tunda su kowanne ga jewelry da takalmi da jakan shi. Tun yana kirkiro murmushi na kar a gane halin da yake ciki har zuciyar shi ta rinjaye shi fuskar shi ya nuna abinda ke cikin zuciyar shi, Baawa da hankalin ta yana kan shi tana jiran taga yayi ta murnan ganin irin kayan da ta hadawa amaryan shi sai taga tsab'anin haka fuskan duk a murtuke yake duba su. Cikin sanyin jiki ta fara mishi magana" da alamu dai Zafar kayan amaryar nan basuyi maka ba ko?" " Haba Baawa wad'an nan kayan ko makaho ya shafa su ya san sunyi matukar kyau, abinda yasa kika gan ni haka jikina ne yayi sanyi ban san wani kalamai zanyi amfani dasu ba wajan gode miki domin kayan sun burge ni sosai" yabata amsa yana gyara mood da kawata fuskar shi da yalwataccen murmushi. "Menene a nan da har kake fad'in haka Son, ko ka manta kai d'in gudan jini nane?" Girgiza mata kan sa da yake kasa yayi ya cigaba da murmushin dole. "Good yanzu abinda nake so da ksi shine kada ka bar kayan anan ka kai su can bangaren ka ko zuwa dare sai ka kai mata ko?" "Toh Aunty mun gode Allah ya saka da alkhairi" yace mata. "Ameen my son Allah ya nuna mana ranan lafiya mu sha biki" tace tana d'an dariya 'yar uwar ta Hadiza na taya ta dan su Mom sun bar musu parlorn tuntuni. Maida boxes d'in yayi ya rufe ya kira masu aiki suka taya shi d'auka yayi musu sallama ya fita, a parlour shi suka ajiye suka fita shi kuma ya nemi waje ya zauna yana ta jan tsaki dan shi raini ne baya so da girman shi da komai wai shi za'a aika wajan 'yar yarinyan ga Sadeeq ma jiya yazo mishi da rainin hankali wai shi zai kai mata invitation cards shi kuma yace in ba zai Kai da kan shi ba ya zubar dasu a bola shi Kuma ya watsar mishi akan gado yace ga bolan nan, da gudu ya bi shi ya fita yana mishi dariyan mugunta. "D'an iska zamu had'u ai sai na koya mishi hankali" yace shi kad'ai kaman wani sabon kamu. Ni kuma gyaran nan da akayi min na kwana 2 ya karamin masifan kyau kaman an canza min fata ta saboda yanda ya kara laushi da tsantsi ga kamshi na musamman da yake tashi jikina. Da daddare bayan mun idar da sallah isha'i Inna ta kawo min wani had'i da akayi na madara tace in shanye in bata kofin ta, karb'a nayi na shanye na saboda ta zata auren gaskiya zanyi take b'ata kud'in ta bata san auren wata 2 ko uku bane. Lafiyayyan abinci ta zubo min shima tace in cinye dan kwanakin nan abinci masu gina jiki take bani Kuma shine ya bada gudumuwar hana rama ta bayyana a idon mutane, ina cikin tsakurar abincin ina sauraron wa'azi da sheikh Aminu daurawa da yake akan rayuwa a tashan sunna tv,o sosai wa'azin ya saukar min da natsuwa domin kaman dani yake yi. Sallaman yaron makocin mu da yayi yasa na dago da kai na tare da amsa mishi kasancewar ni. kad'ai ce a parlour Inna tana kitchen. "Wai ana kiran ki inji wani mai mota a waje". Rasss shine sautin da naji zuciyata ya bada, na kasa bashi amsa saima zuciya ta daya tafi tunani waye zai kasance kenan,Yaya na ko d'an rainin hankali nan ne? Koma wanene ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99