Chapter 54
Chapter 54
zai dawo ya d'auka sai dai yunwar ta kashe ni. Na kusan minti 30 zaune sai tsaki nake ta jerawa saboda takaicin da ciki na ke bani na kasa hakurin yunwan ni kuwa nace sai dai in mutu ban cin kazar da aka dangwar min. Jiki na rawa ya fara na kai last stage da ba zan iya jurewa ba kuma,tashi na kara yi ina tafiya da kyar tare da addu'an Allah yasa bai fito ya d'auke ba dan na lura in na zauna yunwar ta kashe ni ba matsalar shi bace Inna ta akayiwa asara. Ina bud'ewa kuwa naga tana nan ajiye kaman yanda na barta, wawurar ta nayi na koma ciki da sauri bayan na maida kofa na rufe, ban iya karasawa cikin bedroom din ba a nan parlorn na zauna jiki na rawa na dauki goran yogurt na kafa kai ban sauke ba sai da na shanye tas sannan na ajiye roban Ina ajiyan zuciya. Kullin kajin na warware shima na fara ci hannu baka hannu kwarya, ban sarara ba sai da naji nayi kat sannan na ture su gefe na jingina da jikin kujera sai sakin ajiyan zuciya nake amma kuma can kasan zuciya ta kuma haushin kaina nake ji da na kasa hakuri na ci wannan kayan shikenan ya samu hanyan cewa ni kwad'ayayyiya ce na san kad'an daga cikin halin sa kenan. Tashi nayi na tattara su na kai su cikin frdge da na gani cikin parlour na saka duk wai dan Kar ya shigo ya gani na ci, hmmm in banda abu na a Ina ma zai ganni ai duk hanyan da zan kaucewa had'uwa ta da shi zanyi har lokaci da ya d'iba yayi ya sallame ni in kama gaba na. Da wannan kwarin guiwan na shiga bathroom na wanko hannyaye na yafa veil karami a kaina na fito parlour na zauna akan sofa tare da cigaba da nazarin rayuwata tun daga kuruciya zuwa yau. Tun yanzu na kogu lokacin da ya d'iba yayi ya sallame ni makaranta zan shiga abuna inyi karatu mai zurfi in cika buri na, na zamewa Inna farinciki kuma abin alfahari. Ban san lokaci ya tafi sosai ba nayi zurfi cikin tunani naji muryan mace na sallama. Firgigit na dawo hayyaci na tare da tashi zaune na amsa sallaman tare da aro 'yar fara'a na yafawa fuska ta Ina kallon kyakkyawan yarinya da ba zata wuce age mate na ba hannun ta rike da wani hadadden basket mai dan girma da warmers masu kyau a ciki, nuni nayi mata da wajan zama nace ta zauna. Ba musu ta zauna ta fara gaishe ni jin abun nayi bambara kwai wai ni za'a gaisar, amsawa nayi Ina tambayan ta mutanen gida tace min suna lafiya. Miko min basket din hannun ta tayi tare da cewa " suna na Yasmin ni cousin sister ce ga Ya Zafar, mama na da Abban shi 'yan d'aki d'aya ne yanzu ma ita tace in kawo muku wannan breakfast din sannan akwai sakon da tace a bashi". D'an murmushi nayi nace " Allah sarki yayi kyau". D'aukan basket nayi na kai kan dinning table na jajjera warmers din na dawo na zauna kusa da ita da ko motsawa bata yi ba a inda na bar ta ba, I'm feeling nervous dan ban san wani irin hira zamuyi ba. "Pls kiyi mishi magana zan tafi dan ance kada in dad'e" naji muryan ta ya katse ni. "Toh" kawai na iya ce mata na mike Ina d'aga kafa da kyar zuciya ta kuwa kaman ya fasa kirjina ya fito, me zan ce mishi tayaya ma zan iya shiga d'akin wannan masifaffen?. Na fi minti biyar tsaye a bakin kofan amma na rasa tayaya zanyi sallama ko kwankwasawa ba mamaki ma in ya ganni kofan d'akin shi yayi min wata fassarar, ganin babu sarki sai Allah yasa na daure na kwankwasa kofan amma a hankali kaman mai tsoron kada a jita. Nayi knocking kusan sau 3 amma banji alamun motsin mutum ba, hakan yasa na bud'e a hankali na leka naga babu kowa sai sanyin ac daya had'u da kamshin sa ya bada wani yanayi mai ni'imar gaske, lumshe ido na nayi Ina kara bud'e kofofin hanci na Ina shakan kamshin naji bud'e kofa wanda ya haddasa min bud'e ido ba shiri. Shine ya fito daga bathoom d'in shi daure da towel alamun daga wanka yake ya rike waya da hannu daya d'ayan kuma rike da karamin towel yana goge kirjin shi da ya wadatu da yalwataccen gashi mai taushi da d'aukan ido. Zafar da sai yanzu ya lura da mutum a d'akin shi ya bini da kallon mamaki yana watsa min harara , ganin nayi nisa hankali na baya tare da shi ,tsawa ya daka min yana tambaya ta uban me na shigo yi a d'akin shi? . A zabure na d'auke ido na akan shi tare da sauke kaina kasa ina mai jin haushin Kai na, how comes har nayi haka na tambayi kaina, shikenan ya gama raina ni na gama zubar da aji na a gaban shi dama ba wani girma na yake gani ba. Ban iya yi mishi magana ba Kuma na kasa juyawa in koma inda na fito, kaman daga sama naji hannun shi mai d'an danshi ruwa akan hannu na, cikin kid'ima na d'aga kai na ina kallon shi da idanuwa na da suka fiffito kaman zasu fad'o kasa. Murmushin gefen baki ya min yana kashe min ido daya yace " irin wannan kallon haka 'yar Mallam kaman zaki cinye ni , wato kin ga well builded body ko baki san cewa kwalele kike kallo ba" "But let me help you ki d'an rage zafi na San abinda ya shigo dake kenan" yana gama fad'an haka naji ya d'aura hannu na kan lallausan gashin kirjin shi yana bina da naughty look harda karkata kai gefe d'aya. Yanda kika san an d'aura min hannu kan wayan wuta tsirara haka naji wani irin shocking tun daga tsakiyar kai na zuwa tafin kafa ta, ba shiri na janye hannu na da karfin gaske jiki na rawa na fice a d'akin da gudu Ina jin dariyan mugunta da yake min. [6/16, 9:18 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99