Chapter 72
Chapter 72
yake damunka ba but ka sani in aka ce maka kana da iyali dole sai kayi hakuri da kai zuciya nesa domin mata da kake gani akwai su da rauni manzon Allah yace da kashin hakarkari aka hallice su, kaga kuwa a lankwashe suke in kace zaka mikar da karfin tsiya sai dai ka karya so kabi komai a sannu. Kaji ko?" Abba ya karasa yana shafa gashin kan shi. Murmushi yayi yana gyadawa Abba kai dan ya san Abba bai san matsalar da take damun shi bane, yanda ya fahimci abin daban ne, a haka Mom ta dawo ta same su ta zauna akan kujeran dake opposite da inda suke zaune idonta akan su tace" me Baba da yaro suke tattaunawa ne?" " Shagwab'a ke damun yaron naki, kin riga da kin shagwab'a shi tun farko gashi ya girma harda iyali bai san ya girma ba" Abba ya amsa mata yana dungure kan Zafar. Hannu ta mika mishi tana " come here my boy ai yaro baya girma a gaban maman shi" da rarrafe ya karasa wajan kafan ta ya zauna tare da daura kan shi akan guiwar ta. "Yi shagwab'ar ka yanda kake so d'ana ko akwai wani abu da kake bukata ne?" Rungume kafaun nata yayi ya girgiza mata kai, dariya ta saka tana "lalle yau yan shagwab'an na kusa kuwa". Abba ma dariyan yayi suka fara consoling d'in d'an nasu tare da yi mishi hira mai dad'i har ya wassake ya fara dariya harda kyakyatawa, damuwan dake ran shi kusan kashi 70 ya ragu sai kusan karfe tara sannan yace zai tafi gida yayi musu sallama ya fito ya shiga motan shi ya nufi gida. Yana nufo gida damuwar shi da yaji ya d'an ragu yaji ya dawo sabo , ji yayi kaman ya fasa shiga gidan ya koma amma haka nan ya daure ya shiga saboda ya san rashin shigan ba shine mafita ba, koda yayi parking ya d'an dad'e zaune a cikin motan tare da daura kan shi jikin staryn yana neman mafita. Ya jima a haka sannan ya hakura ya mike jiki ba kwari ya nufi cikin gida. Ni kuwa tunda ya fita nake kuka wanda nima ban san dalilin shi ba amma can kasan zuciya ta soyayyar shi ce dankare a ciki yana dawainiya dani hakan yasa kowani irin hali ya shiga sai naji dumbin tausayin shi tare da jin zan iya taimaka mishi ta kowani hali dan ya samu farinciki. Sabon yanayin da nake ganin shi ciki yana matukar damuna duk da wani b'angare na zuciya ta yana tunasar dani cewa yaudara ce sai nake kokarin karyatawa, har aka Kira sallah mariba bai dawo ba. Ina zaune akan sallaya bayan na idar da sallah magriba ina jiran inji shigowan shi amma shiru gaba daya hankalina yayi kan shi domin ko lokacin da muke 'yar tsama dashi ya kan shigo da yamma sai bayan anyi sallah sannan in zai fitan ma ya kara fitan, gaba daya hankalina yana kan shi na kasa natsuwa I was so restless sai kallon agogo nake. Jin an fara kiran sallahn isha'i yasa na tashi nayi sallah harda shafa'i da wutri but na kasa mikewa wa akan sallaya sai kara kallon agogo nake Ina jin kaman in fita in nemo shi zuciya ta sai kara ingizani take akan in sassauta muyi zaman mu tunda abinda nake buri kenan nima tunda shima duk girman kanshi ya sauke yana bi na harda roko. Gajiya nayi da zaman na tashi na shiga wanka Ina fitowa na kama shirn bacci riga da wando na saka na wani yadi mai tsanti rigan da botira a gaban, gashi na kuwa tattare su nayi parking a tsakiyan kai na shafa humra na da aka ce min sai zan kwanta in rinka shafawa, na kuwa bulbulawa shi a jikina domin nima sosai kamshin sa da sanyin sa take tsaya min a rai. Wutan d'akin na kashe na bar dim light bayan na hau gado ina ta sake-sake a zuciya ta har bacci yayi nasaran sace ni. Zafar a nutse ya shigo gidan without making any noise ya shige d'akin shi ya rufe kofa ya zauna akan couch dake d'akin na wani lokaci yana tunanin anya yayi abinda yaji zuciyar shi take ingiza shi yi ko Kuma ya bari yabi komai a sannu?. Haka ya hakura ya tashi ya shiga wanka ba tare da ya tsaida wani mataki da zai d'auka ba, wanka yayi with his bath gels masu bala'in kamshi ya fito ya shirya cikin singlet da boxers sabbi Kuma farare kal ya fesa body perfumes sannan ya shige cikin bargo tare da fatan Allah yasa yayi bacci da wuri ko zuciyar shi zata huta da wannan sabon al'amarin. Rage karfin Ac yayi dan wani sanyi yake ji duk da yana cikin bargo, figigit ya bud'e idon shi domin yana lumshe ido da niyan bacci fuskata ya fara cin karo dashi ina dariya. Tashi yayi zaune ya saka hannun sa cikin lallausan gashin kan shi Yana yamutsawa tare da rutse idon da karfin gaske domin yanda yake jin wani abu yana fisgar shi, yama rasa ya zaiyi da rayuwar shi. Ya kai good 40 mins a haka tsam ya mike kaman wqnda aka tsikare shi da allura ya fita, kai tsaye d'aki na ya nufo dan a yanda yake jin shin nan gwara ayi ta ta kare dan in ya cigaba da zama a haka kila zuciyar shi ce zata buga. A hankali ya turo kofan ya shigo yana tafiya a hankali cikin hasken dim light da ban kashe ba,yana hango ni cikin bargo da alamu bacci nake a hankali ya karaso ya tsaya ta wajan fuskana yana kare min kallo yanda nake bacci na cikin kwanciyar wanda shi ya gagare shi cikin kwana 2 nan. Durkusawa yayi a gaban gadon yana mai cigaba da kallon fuskata kaman mai neman wani abu akai, wani masifan kyau yaga ina yi mishi ya fara kallo tundaga goshina da kananan gashi ke kwance kaman na jarirai har zuwa kan ido na da eye lashes suke a mike kaman wacce ta Kara da na kanti, hanci na da yayiwa fuskata kyau shima yabi da kallo ji yake kaman ya lashe ni. Cak idon shi ya tsaya kan tsukakken lips d'ina da suke pink gwanin sha'awa bai san lokacin da ya duka a hankali ya min light kiss ba ganin na dan motsa yasa ya dan ja baya kad'an ya tsaya na wasu seconds yana kallo na yana jin yanda zuciyar shi take ingiza shi kan ya hau gadon ya rungumo ni ya saka ni a jikin sa. Samun kanshi yayi da zagayawa ya haura kan gadon ta dayan side d'in a hankali kaman mai tsoron gadon. Cikin tsanda ya daga bargon ya shiga ya lulluba shima yana kallon baya na so yake ya manna ni a jikin shi amma yana gudun kada in farka in kore shi yasa ya kwanta shiru yana sauke ajiyan zuciyan samun relief na ya kasance kusa dani. Sai dai me ko cikakken minti 2 baiyi ba wannan fitinannen kamshin ya fara ruguza mishi lissafi ya fara manta a ina yake shi dai burin shi ya jini a jikin shi yana shak'an wannan daddadn kamshin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99