Chapter 13
Chapter 13
wannan kud'in yayi amfani dasu wajan ciyar da iyalin shine zai iya biya amma tunda kansa kad'ai ya sani bai san hakkin daya rataya akan sa ba shi ya sani yaje can ya karata. "Allah sarki Bintu Allah dai yasa ba mugun halin kema kika fara kaman sauran matan ba saboda mugun halin d'an uwana duk shi ya jefa iyalin shi cikin halaka" yana magana ne tare da shigewa b'angaren shi. Gwaggo Aisha da Inna Asabe duk sun kasa barin wajen suna tsaye a wajan kaman wanda aka dasa su kowacce da irin tunanin da take a zuciyar ta saboda Abin ya mugun daure musu kai sosai ita da duk gidan itace wacce bata dashi amma yanzu ta dara kowa a gidan. Gwaggo Aisha fargaban ta d'aya shine kada Inna tazo ta kwace mata matsayi a wajan Baban mu domin ta san halin shi tsab zai iya juya mata baya dama saboda tafi kowa kud'i a gidan yake fifita ta, kai dole ne tayi wani abu akai dan ba zata tab'a zuba ido Inna ta ta kwace mata ba. Da washe gari ina dawo daga makaranta a nesa na hango motan Abdulbasit a k'ofar gidan mu, aiko da gudu na karaso wajan motan cike da murna dan yanzu na daina tsoro tunda Innata da kanta take cewa inje mu gaisa bayan haka ga kayan dad'i da kullum in zai zo yake kawo min, yana zaune a ciki motan amma kafafun shi a waje hankalin shi yana kan wayar shi ban san me yake dan dannawa ba. "Sannu da zuwa Yaya na" na fad'a da d'an karfi bayan na karasa kusa dashi,a d'an razane ya d'ago sai kuma ya saki murmushin sa mai kyau da baya barin fuskan sa. "Har kin tsorata ni saura kad'an in ruga da gudu" ya ce yana dariya. Nima dariyan na kyakyale dashi sannan na ce," toh ya zakayi da motan ka in ka gudu ka barta?" "Sai in bar miki ita ki rink'a zuwa makaranta dashi" toh ai ban iya yanda ake tukawa ba" na fad'a a shagwab'e. "Kada ki damu zan koya miki, kije ki cewa Aunty zan shigo mu gaisa". Da toh na amsa sannan na juya na shige gida da sauri na, su Hajara duk sun tafi tallah iyayen nasu ma ban gan su ba da alamu duk sun fita. Inna tana k'ofar d'aki tana shara na shigo da sallama ta amsa tana yi min sannu da zuwa,ciki na shige na ajiye jaka ta sannan na kara fitowa na ce mata," Inna Yaya yazo yana waje yace zai shigo ku gaisa". "Ciki nan zai shigo yace?" Ta tambaya da alamun tsoro da damuwa akan fuskan ta, gyad'a mata kai nayi ina kallon duk yanda ta zama wani iri. "Toh ya shigo" ta ce tana komawa d'aki ni kuma na fita waje na sanar dashi kan ya shigo, a bakin k'ofan d'aki muka tadda Inna zaune cikin tagumi amma tana ganin mu ta saki ran ta tana mishi sannu da zuwa. Kallon gidan namu yake tare da nazarin sa,har k'asa ya duka suka gaisa da Inna a mutunce tare da bata hakurin rashin zuwan sa akai-akai kaman yanda yayi mata alkawari, nuna mishi tayi babu komai kana ta d'aura dayi mishi godiya tare da addu'oin gamawa da duniya lafiya. Cikin jin dad'i yake amsawa da Ameen sannan ya mike yace zai wuce dai-dai lokacin kuma iska mai karfi ya d'aga d'an yalolon labulen mu karaf idon sa sai a d'akin mu da ko arzikin leda babu sai siminti dasu ghana must gon mu a gefe. Tare muka fito dashi har zuwa wajan motan sa ya ciro manyan jakuna na shopping daya saba kawo mana ya mik'a min sannan ya kara da kud'i masu yawa yace in bawa Inna ince ta sayi carpet na tsakar d'aki dasu gado. Cikin tsananin murna na dawo cikin gida da kaya niki-niki sannan na nunawa Inna kud'in daya bata tare da fad'a mata abinda yace tayi dasu. Karb'a Inna tayi ta ajiye gefe ba tace komai ba dan yanzu zuciyar ta ta fara amincewa dashi sannan ta fara sabawa da lamarin sa. Ni kuwa duk na k'ogu ta bud'e kayan domin na san duk tsaraba nane a ciki, tana bud'ewa kuwa sune ice cream da sauran kayan dad'i sai kaza gasassu biyu,ice cream na na d'auka na koma gefe na fara sha domin ni yafi min kaza sau dubu. Da washe gari Inna ta sayo mana carpet d'in mu maroon mai d'an karan kyau harda katifan mu da sabon labule, murna a waje na ba'a magana muma munyi katifa kaman sauran 'yan gidan mu, a ranan da kyar Inna ta kirani waje domin tarewa nayi akan katifan. A wannan rana mun ga hasada kiri-kiri a wajan matan gidan mu, Gwaggo Aisha tafi kowa shiga tashin hankali sai zage-zage take babu wanda ya kula ta sai 'yan koron tane suke taya ta. Babu abinda zan cewa Allah sai Alhamdullilahi saboda rayuwar mu ta canza sosai yanzu muci mai kyau mu sha mai kyau mu kwanta a waje mai kyau hatta suturar da muke sakawa ya canza albarkacin Abdulbasit. Mu muna nan zaune zuciya d'aya ashe bamu sani ba Gwaggo Aisha ta saka ana tayi mata bincike ta ina muke samun kud'i har rayuwar mu ta canza muka zama zara a cikin su. Bata sha wahalan samun cewa wani saurayi mai kud'i ne yake taimaka mana ba, daga wannan rana ta saka ido sosai tana jiran zuwan shi,cikin ikon Allah duk lokacin da zai zo bata nan sai dai taji labarin yau yazo ya tafi. A wannan lokacin Gwaggo Aisha duk yawon ta daina fita muka ga tayi a gida take wuni haka Hajara ma ta daina zuwa tallah kullum suna gida,ni na d'auka cewa sun daina tallah ne ashe wai ta gaji da kullum sai ta dawo daga gantalin ta taji cewa yazo har ya tafi shiyasa suka daina fita kullum hanya suke kallo suna jiran zuwan shi. Sun kai kwana biyar da shiga kullen nasu Abdulbasit yazo yanzu mun saba sosai ni dashi dan har tambaya ta yake abubuwa da nake so, ni kuwa in kirgo mishi in zai dawo ya kawo min. Ranan ma haka ya kawo min sautu da nayi mishi na kayan kwalliya shi kuma ya sayo min masu tsadan gaske kaman wata budurwa da kuma kayan makulashe daya zame masa jiki kullum zai zo sai ya kawo min, bayan ya gama zolaya ta na gama kuka na muka shirya na kwashi kayana na zan shiga ciki bayan nima na saba kullum in yazo sai na zolaye shi da in d'an b'uda murya ince," sannu da zuwa Yaya naaa". Sai ya juyo a d'an razane yace," kin tsorata ni zaki sa in fita a guce" sai inyi ta kyalkyalan dariya. A zaure na tarar da Hajara tana tsaye sai lek'e take ta sha kwalliyan ta na 'yan tallah fuska ya sha make up har yayi over. Tana gani na ta had'a rai ta tsaya ni kuwa da hankali na na kuruciya ban kawo komai a raina ba nayi shigewa ta ciki, tana ganin na shiga ta fito da saurin ta zuwa wajan shi domin har ya shiga motan shi ya tayar saura yaja. "Assalamu alaikum
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99