Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,440 words 0 views Progress saved
Download Book

Ban dawo gida ba sai da Inna tasa aka kira ni sannan na dawo nan ma kayan makulashen ta d'ibarwa Maa tare da dubu uku tace in kai mata ince Abdulbasit ne yazo yau. Karb'a nayi na fita ina maimaita sunan a raina wai Abdulbasit ni dai ban tab'a jin suna haka ba sai yau. Maa kin karb'an kud'in duka tayi dubu d'aya ta d'auka tayi godiya na komawa Inna da kud'in ta karb'a tana zata je anjima da daddare da kanta wajan ta. Kayan makulashen Inna ta bani, ice cream d'in nayi ta sharba dan ya min mugun dad'i sosai duk da rabi da kwata sun narke amma abinka da baka tab'a sha ba sai naji kaman madara empty nake sha,sai da ya kare muka ci kazar mu mukayi nak abin mu ranan ko girkin dare ba muyi ba. Sai bayan sallah magariba sannan Inna ta nuna min kayan da Abdulbasit ya kawo min, aiko kaman in haukace saboda murna kayakin da ban tab'a tsammanin zan mallaka sai gasu har kala biyar duka nawa ni kad'ai harda Baby na. Da kyar na samu nayi bacci a ranan saboda murna ina rungume da Babyn nawa nayi bacci a ranan. Da washe gari da safe na fito ina share kofar d'akin mu naga Jameela ta fito dasu ledan alale da sob'o ta ajiye a wajan wanke-wanke tana kallon ido na tana murmushi irin su jiya sun ci kayan dad'in biki. Ban kula ta ba sai da na kwashe sharan da nayi sannan na shiga d'aki nima na fito da robobin ice cream da kuma takardan naman kaza da muka ci harda warwarewa yanda za'a ga kasusuwan cikin sannan na ajiye a wajan wanke-wanke nima inayi mata murmushi na koma d'aki karb'o omo da zanyi mana wanke-wanken. Da na karb'o omo sai da na d'auko Baby na na fito ina danna madannin jikin ta fara wak'an larabci,ina fitowa na tarar da Gwaggo Aisha tana leken inda na ajiye kwanukan mu. Dariya nayi na ajiye Baby na a gefe na fara wanke-wanke na hankali kwance,ina jin Gwaggo Aisha tana jan tsaki tare da cewa," karyar banza bayan mun san komai me za'a nuna mana. Tana magana ne tare da shigewa d'akin ta sai dai tana shiga naji suna rigima da Jameela wai a saya mata irin Baby na,tun tana rarrashi naji an kai mata maka ta tsala ihu tayi waje da gudu. Ko a ido ka kalli babyn ka san mai tsada ce shiyasa tayi mata haka domin bata da kud'in sayan shi. Ranan muna zaune a d'aki bayan magariba ana gobe Inna zata karb'i girki muka ji muryan wani abokin Baban mu yazo yana ta masifa kan wai Baban ya ranci kud'in shi naira dubu biyu bai biya ba, ashe tun bayan la'asar Baba yake gida ya kasa fita majalisa saboda bashin da ake bin shi bamu sani ba. Abu kamar wasa fitinan yayi girma dan ana ta bashi hakuri yace babu inda zai je sai Baba ya biya shi kud'in sa yau kusan wata 2 kenan ana abu d'aya kuma shi ya gaji da yanda Baba ke cewa yau ko gobe. Jakar kayanta Inna ta bud'e ta ciro dubu biyun tace min in kaiwa Baban mu,karb'a nayi na fito kai mishi ba dan raina yaso ba saboda shima baya tausayin mu baya nuna kulawa gare mu sai sauran 'yan gidan shiyasa nima banga dalilin da yasa zamu tausaya mishi ba. Sai dai ina zuwa saida na tausaya mishi,yana rab'e jikin k'ofan shi yayi abin tausayi shi kuwa mai bashi sai ci mishi mutunci yake, ga kanin Baban mu da muke kira da baffa shima sai hakurin yake badawa amma a banza Ina zuwa kusa dashi na tab'a shi ya d'ago ya kalle ni da idon shi daya canza kala, mika mishi kud'in nayi na ce," gashi inji Inna tace ka biya su kud'in. Baba kasa karb'an kud'in yayi ya tsaya kallo na haka sauran matan ma suka tsaya kallon kallo. *Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*. [9/3, 9:06 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊 *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ مَنْصُورٍ وَقُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ وَأَبُو كَامِلٍ الْجَحْدَرِيُّ وَاللَّفْظُ لِسَعِيدٍ قَالُوا حَدَّثَنَا أَبُو عَوَانَةَ عَنْ سِمَاكِ بْنِ حَرْبٍ عَنْ مُصْعَبِ بْنِ سَعْدٍ قَالَ دَخَلَ عَبْدُ اللَّهِ بْنُ عُمَرَ عَلَى ابْنِ عَامِرٍ يَعُودُهُ وَهُوَ مَرِيضٌ فَقَالَ أَلَا تَدْعُو اللَّهَ لِي يَا ابْنَ عُمَرَ؟ قَالَ إِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ لَا تُقْبَلُ صَلَاةٌ بِغَيْرِ طُهُورٍ وَلَا صَدَقَةٌ مِنْ غُلُولٍ وَكُنْتَ عَلَى الْبَصْرَةِ. *It was narrated from Simak bin Harb, that Mus`ab bin Sa`d said: "`Abdullah bin `Umar came to visit Ibn `Amir when he was sick and he said: `Won`t you supplicate to Allah for me, O Ibn `Umar?` He said: `I heard the Messenger of Allah (s.a.w) say: "No Salat is accepted without Wudu` (purification), and no charity (is accepted) that comes from Ghulul," and you were the governor of Al-Basrah."`* [ Sahih Muslim ] *7* Baban mu jikin sane yayi sanyi sosai, wai Bintu ce ta biya mishi bashi. Bayan duk abubuwa da yayi mata basu da misali bayan wa'yan da ya fifita duk suna tsaye babu wanda yayi gigin biya mishi alhalin suna dashi, more especially 'yar gaban goshin sa wato Gwaggo Aisha, ga Baffan mu duk suna wajen taya zai iya kallon idon ta nan gaba?. "Amma Mallam Hassan ka cika mugu azzalumi,wato yanzu a baka kud'in da zaka biya ni shine ka rike ka maida ni d'an iska wato inyi in gama ko? Allah ma yasa a gaba na aka aiko da kud'in da shikenan sai ka cigaba da raina min hankali kana cewa babu" yana banbani ya matso kusa da Baban mu ya kwace kud'in a hannun sa ya fita yana," Allah ya so ka Mallam". Da ido kowa ya bi bayan shi har ya ida ficewa, bai san cewa mamaki ne daya cakud'u da mutuwar jiki su suka hana shi bayar da kudin ba, bai kara kallon kowa a wajan ba ya koma d'akin shi ya zauna a bakin gado tare da rafka uban tagumi yana tunanin ta yayane zai shawo kan Bintu yaci dad'i kuma ya samu na kashewa, dubu biyu fa?. Can shi kad'a ya saki murmushin jin dad'i alamun ya samu mafita kenan. A waje kuwa Baban mu yana shiga d'akin sa Baffan mu shima ya bar wajan yana tab'e baki dan bai ga dalilin da zai saka ya biya mishi bashi ba, da ace

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99