Chapter 34
Chapter 34
dai da alamu nayi kuskure dan abin naki kara gaba yake. Pls ki bar nan in daina ganin ki ko zuciya ta zatayi sanyi saboda yanzu ko ganin ki nayi zuciya tafasa yake, dama abinda ya kawo ni kofar gidan ku kenan kada ki kara kira na a waya cos I don't have time for cheap girls like u". Yace yana min wani kallon tsana. Wani irin kuka na fashe da shi na juya zuwa cikin gida da gudun tsiya har bana iya ganin gaba na, saura kad'an in mangaje Baban mu da yazo fita yayi sauri ya bani hanya na wuce shi zuwa cikin gida ko waiwayowa banyi ba duk da kira na da yake ta faman yi. A masifance yace" wani d'an kwal uban ne ya tab'a ki a anguwan nan, bari inje in gani duk wanda na gani mai raba ni dashi sai Allah" ya faman gyara babban rigan shi ya nufi hanyan fita. Da sauri ya dawo da baya yana zare ido tare da dafa kirji yace" wai-wai dama da wannan hukuman ne????? [1/26, 7:08 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *19* "Masha Allah an gode ranka ya dad'e har zaku tafi kenan?" Su Zafar suka tsinkayi muryan Baban mu a bayan su, wani malalacin murmushi yayi sannan ya juyo yana yiwa Sadiq signal da ido. "Eh Baba zamu wuce tunda jikin nata da sauki sai mun kara dawowa" Sadiq ya bashi amsa ya juya zuwa ga motan nasu. Zafar gaban Baban mu ya dawo ya tsugunna yana wani sunkuyar da kai kaman mutumin Kwarai yace" nagodewa Allah daya had'a ni da kai Baba, dama na dad'e ina son muyi magana amma ta ki hadani da kai". "A'a ranka ya dad'e ni kuma gani na abu ne mai sauki me kake bukata?" Baba ya amsa jiki na rawa. Sai da ya d'an sosa keya alamun yana jin nauyin abinda zai ce yace" Abba ne yake son su zo ayi maganan aure na da ita, shine nace bari in fara fad'a maka in ka amince sai su zo" wannan karan Baba rasa inda zai saka ran sa yaji dad'i yayi ji yake kaman ya kurma ihun murna sai dai ba hali cikin sauri har muryan shi na rawa yace" kai amma yaro yaro ne meye na wani sai an tambaye ni, bayan babu inda zan je kullum ina gida. Ko yau suke so su zo ina jiran su kaji?". "Toh Baba nagode, mu zamu tafi" yace tare da mikewa ya kara ciro wasu bundles d'in ya zubar da su a gaban Baba sannan ya mike har suka fita daga compound d'in Baba bai dawo daga suman ganin makudan kud'ad'e daya tafi ba. Sun hau kan hanya ba tare da Sadiq ya kalle shi ba yace " Zafar it's wrong, it's totally wrong". "And who are you to say so?" Zafar ya tambaye sh yana kara cin magani, Sadiq bai kara ce mishi uffan ba sai ma kara maida hankalin shi da yayi kan tukin da yake. A nan asibiti kuwa Gwaggo Aisha kasa zaune ta kasa tsaye sai jujjuya ido take wai me yake shirin faruwa ne, bata gama da wancan ba kuma ace ga wani ya bullo? Ita abinda yafi d'aga mata hankali shine ita 'yan matan ta basa samun masu kud'i sai ni, shi wannan kam bayan mai kud'in ne kuma gashi balarabe. "Wallahi ba zata tsabu ba wai bindiga a ruwa wannan karan sai ta raba ni da komai na jin dad'in rayuwa ko da duk abinda ta mallaka zasu kare ba zata tab'a zuba ido Bintu da 'yar ta su kasance fiye da ita da yaran ta ba. Kaman wacce aka tsikare ta da allura muka ga zuruf ta mike fuuu tayi waje kaman wata kububuwa,da ido kowa ya bi ta dan tunda su Zafar suka fita babu wanda yayi magana cikin d'akin kowa da kalan tunanin da yake a cikin zuciyar shi. Tashin hankali da Gwaggo Aisha ta tarar a waje yasa taji kaman ta kurma ihu dan bakinciki, akan idon ta Zafar ya yiwa Baba kyautan makudan kud'ad'e suka shiga mota su dashi kad'ai ta kalla ta san cewa kud'in sa ya wuce duka tunanin ta. Ganin Baban mu ya hangame baki ya kasa dawowa hayyacin sa tunda yaga ruwan kud'i ya kara tunzura ta, ta taho a fusace ta cikin d'aga murya tace "kai Mallam meye haka?" sai a sannan yaja doguwar ajiyan zuciya ya juyo ya kalle ta,ba tare da yace mata ci kanki ba ya kwashi kud'add'en sa yayi gaba abin shi. Sosai Gwaggo Aisha ta shak'a wato ya mai da ita mahaukaciya ko? Zasu gani zata nuna musu ainihin true colors d'in ta zasu san da ita suke zancen, sai matsayin ta na da ya dawo ta cigaba da mulkan gidan baki d'aya. Bayan fitan Gwaggo Aisha Inna abu da Hajara suka mike sukayi mana sallama tare da yi min Allah kara sauki suka fita, cikin sauri Inna tabi bayan su dan basu kud'in mota d'akin ya kasance daga ni sai Maryam da Maa da ta juya mana baya ta kwanta da alamu dai tayi bacci. "Ni fa na kasa yarda Yaya na zai min haka, saboda yana matukar so na Maryam wallahi yana so na" na karasa ina fashewa da sabon kuka. Gyad'a kai kawai Maryam ta iya yi min tana share hawaye itama saboda ta shiga duhu sosai a yanda muke matukar son junan mu ace ya juya min baya lokaci d'aya, tabbas babban al'amari ne zai iya raba mu , addu'an ta Allah ya daidaita tsakanin mu. "Kiyi hakuri Zareefa ko wani tsanani yana tare da sauki, mu cigaba da addu'a insha Allah komai zai daidaita" ban iya bata amsa ba sai kuka da nake ina jin zuciya ta na min wani irin suya. "Hmmm ni ban san su Ya Sadiq me ya kawo su nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99