Chapter 17
Chapter 17
cream a rayuwa ta, dan gobe kad'ai ban sha ba me zai same ni, bai kyale ni.ba sai da nayi masa alkawarin zan je in sayo a today's d'in sannan ya hakura mukayi sallama ya tafi tare da bani hakurin inda zai tafi babu service dan haka ba zamu waya kaman yanda muka saba ba. Haka ya wuce duk sai naji na damu domin sosai na saba kullum sai naji muryan shi nake iya bacci yanzu haka muryan sa shi ke tada ni a bacci. A tsakar gida na tarar da Gwaggo Aisha da wata 'yar figaggiyar kaza guda d'aya ta saka a tire ta d'auko sharb'eb'iyar wuka sai faman kacan canawa take tana ta hura hanci,ni dariya ta bani ban ma kalli inda suke ba nayi shegewa ta d'akin mu anan na iske Baba yana zaune yana zaman jiran in shigo yaji karin bayani dan duk yanda yaso ji Inna kin bashi had'in kai tayi saboda ta san ba dan Allah yake neman sanin ba. "'Yar albarka har kin shigo kenan" "Eh Baba sannu da hutawa" na amsa ina ajiye kayan hannu na kusa da Inna amma kud'in yana hannu na cikin hijabina. Ko kallon kayan Inna taki yi ta cigaba da d'inkin hulan ta hankali kwance, gefe na samu na zauna shima Baba zama ya gyara yana jiran Inna ta bud'e yaga menene a ciki amma ta basar, can daya gaji da zama ya ce," 'yar albarka me kika shigo mana dashi ne?" "Kayan dad'i ne Baba na" na bashi da murmushi akan fuska ta ina kallon Inna ta gefen ido da take harara ta. "A'a toh...toh... Wato Bintu yau kuma rashin kirkin ne ya tashi muna ji muna gani zaki hana mu kayan dad'i?" Cewar Baba cikin raha, Inna dai bata ce k'ala ba ta cigaba da d'inkin hulan ta. "Mu kam bama zuciya kuma ba inda zamu je sai mun ci kayan dad'i ko 'yar albarka?" Dariya nayi ina kallon Inna da tayi kicin-kicin da fuska dan ita al'amarin Baban mu sosai yake bata takaici da haushi, ya za'ayi ace wai kana ganin 'yar da ka haifa ta shigo da kaya masu yawa haka kuma kasan daga hannun saurayi ta samu, baka damu da binciken waye shi ko kuma ya akayi ya bata ko meye tsakanin su ba, saima jiki na b'ari kake son handame abinda ta kawo koma menene kai ba damuwar ka bane. Cike da takaici halin sa da surutan sa daya ishe ta, ta bud'e d'ayan jakan da ta riga ta gane tambarin su kasancewar kullum ana kawowa, ba tare da ta lura da ko kaza nawa ne a ciki ba ta d'auko guda d'aya ta saka mishi a wata leda da babban roban juice d'aya duk ta had'a ta mik'a mishi . Ba batun fushi ko zuciya yasa hannu yana washe baki ya amsa har zai fita na tsaida shi nima na jawo d'ayan jakan sanin cewa nawa shi saboda kullum aka kawo Inna bata tab'awa tarkacen kayan zaki na ne a ciki, roban ice cream babba dasu chocolate dasu snacks ne a ciki nima na cika mishi leda na mika masa harda dubu biyar na saka masa a kasan ledan bayan na faki idon Inna. Ai Baba yanda kasan yayi hauka haka ya koma saboda murna dan akan idon shi na had'aa mishi kud'in yayin da Inna kuma hankalin ta yana kan hulan ta saboda dukkan mu haushi muke bata. Fita yayi yana baza babban rigan shi, zai wuce Gwaggo Aisha ta tare shi da cinyar kaza a hannu cike da jin kai ta ce," Mallam tsaya ka saka albarka kaga 'yar ka Hajara Allah yayi ta samu saurayi mai mota, shine daga zuwa zance ya kawo mata gashasshiyar kaza na rabawa yara shine nace bari kai ma in kawo maka ka saka albarka". "Amma Aisha kike kowa? Wallahi kin matukar raina ni, ni zaki tara ki tsamma wannan abu sai kace kin samu wani kwadayayye ko maye, toh tsaya kiji ni na fi karfin wannan abin naki mai kama da cinyar fara. Dubi kiga inda ake cin arziki da kaza kuma aka san darajan miji ba watsatsu irin ku ba" yana magana yana nad'e hannun babban rigan sa nan manyan ledojin suka bayyana. " Kinga wannan dakwaliyar kaza ce ta gidan gona da taji gashin inji ga lemon roba mai dad'in gaske, sannan kinga nan kuma kayan makulashe ne da sai in rantse da Allah ko wuka aka d'aura miki baki tab'a ganin irin su ba balle ki san sunan su, bayan nan kalli kasan kiga" yace yana nuna mata kud'in kasan ledan sannan ya mike tare da mai da komai cikin ledan ya cigaba da masifa," na dai gaya miki kada ki kara tare ni da maganan banza ko ranki yayi mugun b'aci ba abinda kika iya sai shegen surutu tsiya " nan ya shige d'akin shi ya bar Gwaggo Aisha da mataceccen jiki. Tabbas sai sun sake shiri babba ma kuwa dan bata tab'a sanin haka Bintu tayi nisa ba,gaskiya dole ne ta nemi shawaran aminiyar ta dan samun mafita ko kuma suna ji suna gani wankin hula zai kai su dare. Dariyan yaran gida ne ya dawo da ita hayyacin ta, sun had'a kai kusan su biyar suna mata dariyan yanda Baba ya bar ta da cinyar kaza a hannu, bata kula kowa a cikin su ba ta shige d'akin ta dan ji tayi gaba d'aya jikin ta ya mutu. A d'aki kuwa Baba yana fita Inna har ta juyo da niyyan yi min fad'a dramar su da Gwaggo Aisha ya dakatar da ita, bayan sun gama ya wuce ya bar ta na ce," haba Inna ta, me yasa kike fushi haka yanzu fa kin zama 'yar lele a gidan Mallam". Waje na fice da gudu da roban ice cream d'ina d'aya a hannu ina dariya ganin Inna ta shiga neman abinda zata buga min a kusa da ita bata samu ba. Ciki na shiga b'angaren su Dije muka zauna sha muna hiran Yaya ina bata labarin yanda yau muka rabu da juna dan kawai zaiyi tafiyan kwana d'aya. "Hmmmm gaskiya ke kam Zareefa Allah ya baki, ki ga yanda yake mutuwan son ki kuma yake nuna kulawa yake tarairayan ki, a gidan ku ma ya kula dake haka ina ga ya aure ki ya killa ce ki a gidan sa abin ba magana". Cewar Dije kenan. "Allah gaskiya soyayya akwai dad'i Dije, kin san yanda nake jin sa a cikin raina kuwa? Allah ya nuna min ranan auren mu" duka Dije ta kai min a gadon baya na tana dariya tace. "Shegiya Zareefa har nawa kike da zaki zauna kina maganan aure?" Murkud'a mata baki nayi ina ," eh d'in kema ai shirin yi miki ake nan da shekara d'aya idan munyi sauk'a, toh nima ina gama secondary shekaru biyu da rabi suka rage za'ayi mana ni da Yaya naaa" na karasa ina rungume hannye na biyu a kirji na tare da rufe ido nayi baya kaman zan fad'i Dije ta taro ni tana tafa hannu ta ce," ke yarinyan nan haka kika zama baki tafasa ba zaki kone mana mu shiga uku?" "Wai da kike fad'an haka shekaru nawa kika bani da kike ta cika
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99