Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,233 words 0 views Progress saved
Download Book

sai zare ido da nake zuciya ta na cigaba da bugawa, Inna zata kara min magana muka ji muryan yaron daya rako mutumin nan ya ce,"wai ana neman zareefa". Wani kallo Inna tabi ni dashi sannan ta dubi yaron ta ce," yana ina?" Yana nan k'ofan gidan nan" yana gama bata amsa ya juya ya tafi abinsa. "Waye shi kuma me kika masa ya biyo ki har gida?" "Sh...shine wan...wanda ya biya min kud'in jarrabawa" na bata amsa. "Shine ya biyo ki har gida,ko dai da wani abu daban?" Shiru nayi na kasa bata amsa sai zare ido da nake saboda ban manta abinda tayi min akan shi ba. Hijabinta da yake gefenta ta saka ta fita dan taji me yake tafe dashi,a tsakar gida ta tarar da 'yan gidan mu kwan su da kwarkwatan su suna tsatsaye suna k'us-k'us. Suna ganin ta suka fara yi da karfi wasun su na cewa k'ila sata nayi mishi,wasu kuwa cewa suke asirin mu ne ya tonu k'ila yana cikin mazan da nake bi,tunda dama cewa suke karatun karuwanci nake. Inna ta bata kula kowa ba ta fito 'yar rub'abb'en zauren gidan mu da niyyan yi mishi iyaka dani domin ta gane fad'an da tayi min kwanaki shi ya firgita ni haka. Katuwar mota da ta gani ana sauke kayan abinci a ciki kaman za'a bud'e 'yar karamar shago yasa ta tsaya cak tana kallon d'an matashin saurayin da ba zai haura shekaru 21 zuwa 22 ba yana danna wata laftatiyiyar waya a hannun shi. Inna sai yayi mata kwarjini ta kasa karasa fitan balle tayi mishi magana,shine dai daya gaji da danne-danne shi ya d'ago da kai karaf suka had'a ido da Inna ta,asalin kamanin ta na d'auko shiyasa yana ganinta ya gane ta. Wayar nashi ya mayar aljihun rigan shaddar shi lafiyayya blue ya karaso gaban ta cikin sauri ya duka har k'asa ya fara gaishe ta,fuska a had'e ta amsa kana ta ce," lafiya kake neman zareefa,ko kuma akwai wani abinda kake nema daga gare ta,dan ta bani labarin duk abinda ta faru tsakanin ku kuma shine yau ka biyo ta har gida"? Girgiza mata kai ya fara wasu waye na taruwa a idon shi ya ce," ba haka bane Aunty kada ki min mummunan fahimta saboda ni ba nufi na kenan ba,domin duk had'uwa da muke da ita Allah ne yake had'a mu,lokacin da na gan ta a hanyan makaranta na fito zan tafi wajan aiki ne na gan ta tana kuka sai na biyu kuma na tsaya siyan ruwa a gefen hanya ne na ganta ita da wani yaro suna zaune a gefen titi suna kuka,and still yau shima gefen kwata na ganta zaune tana kukan garin ta ya fad'a kwata mutane duk sun zagaye ta ana taje gida ta fad'a amma taki tashi saboda wai Baban ta ba zai bar ta duk taji ciwo amma ko jin zafin bata yi. Ni suna na Abdulbasit kuma ni maraya ne da tunda na taso ban san kowa nawa ba,banida kowa akan titi nake rayuwata cikin yunwa,kunci da kuma kad'aici sai daga baya na samu wani bawan Allah ya tallafawa rayuwata har kika ganni haka sannan shiyasa na tsani inga karamin yaro yana kuka domin yana tuna min da lokacin kuruciya ta kuma duk yanda zanyi sai na san yanda zanyi in share mishi hawaye sannan hankali na zai kwanta. Ba ita kad'ai nakewa haka suna dayawa Aunty bana son kowa ya sha wahalan da nasha a baya amma in har hakan ya b'ata miki dan Allah ina neman alfarman ki yafe min". Inna da jikinta duk ya gama yin sanyi sai ta kasa furta komai saima jin ba dad'i da tayi kan yi mishi mummunan zato. "Ga wannan kayan abincin a saka su ciki Aunty sannan a bawa Baba hakuri kada ya dake ta tsautsayi ne " taji ya yanke mata tunani. Tulin kayan abincin ta kalla ido a waje ta girgiza mishi kai,"ta ce a'a ka tafi da kayan ka mun gode Baban ta kuwa zanyi mishi bayani zai fahimta kuma...." Katse ta yayi cikin sauri ya ce,"haba Aunty ba'a maida hannun kyauta baya,sannan ni ina farincikin na samu ahali da zan iya nunawa a ko ina amma kika ce haka? Sannan hakan na nunawa baki karb'e ni a matsayin d'an uwa ba,ina neman alfarman ki rike ni a wannan a matsayin inji ya ake ji in mutum yana da ahali". Wannan furucin da yayi saida yasa Inna hawaye,gyad'a mishi kai ta iya yi domin ta tabbata tana bud'e bakin ta kuka ne zai kufce mata saboda tsananin tausayi daya bata, shima cike da farinciki ya mike yana share hawayen idon shi ya ce,"nagode Aunty Allah ya saka da alkhairi zan tafi sai bayan kwana 2 zan rink'a zuwa mu gaisa". Bai jira cewar Inna ba ya fad'a motan shi sai da yayi ribas sannan ya kira wani yaro ya bashi kud'i masu yawa ya ce ya kaiwa Inna ta,yaja motan shi ya fita a layin namu. Inna tana tsaye ta rasa ta ina zata fara tab'a kayan sai ga yaron da aka bawa kud'in yazo gaban ta ya mik'a mata kud'in ya ce," wai gashi inji wancan mai motan ya ce in baki" Wani yawu ta had'iye da kyar hannun ta na rawa ta karb'i kud'in a ranta tana ayyana anya wannan bawan Allah abinda ya fad'a gaskiya ne kuwa? Nan wani sashi na zuciyar ta ya ce mata tunda take bata tab'a cutar da wani ko tabi wani da mugun kulli ba insha Allah in ma da wata manufar yazo Allah ba zai bashi sa'a ba. Da wannan kwarin guiwan ta samu ta kira wasu matasa da suke zaune gefe tace su taimaka mata su shigar mata da kayan abincin ciki,ba musu suka fara jidan kayan domin suna ganin girman ta sosai. Su Gwaggo Aisha baki da hanci suka bud'e suna kallon kayan da ake wucewa dashi d'akin mu,bakin ya mutu murus sun rasa abin fad'a,nima ina nan a bayan k'ofa duk na had'a zufa naga a nata shigowa da kayan suna jerawa a gefe har suka gama suka fita ban fito daga mab'uya na ba dan haka basu san da mutum a d'akin ba. Suna gama shigo da kayan Inna ta basu 500 cikin kud'in hannun ta tace su raba,cikin farinciki suka karb'a tare da yi mata godiya suka koma wajan zaman su,hannayyen ta cikin hijabi ta shigo dan haka babu wanda yaga abinda ke hannun ta. "Hmmmm kun ga ikon Allah ko 'yan gidan nan gaskiya ta fito fili ga ribar boko nan mun gani yarinya 'yar k'arama an koya mata bin maza har gida ake biyo ta,Allah yayi mana tsari ya kare mana 'ya'ya".cewar Gwaggo Aisha kenan cike da hasada. Suma sauran kaman jira suke suka fara nasu kowa na fad'an albarkacin bakin shi, Inna ko kallon inda suke ba tayi ba ta shigo d'aki ta cire hijabin jikin ta tare da zama dab'as kan simintin d'akin mu dako leda babu tana kallon kayan zuciyar ta na bugawa,kud'in hannun ta ta shiga kirgawa taga dubu goma ne cif ta ajiye a gefe. Hango ni tayi a bayan k'ofa ina lek'en ta tace," ba zaki fito bane ko sai nazo na same ki" cikin

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99