Skip to content

Chapter 62

Chapter 62

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

hankali. "Hmmmm hakane Maa har hankali na ya kwanta da tunda na dawo na kasa sukuni domin na san yanda wannan matsalar take" Inna ta amsawa mahafiyar ta cikin sanyin murya.. " Ki kara kwantar da hankalin ki saboda mun yarda da tarbiyan da muka bata ba zata tab'a yin abinda zai b'ata sunan ta ko na gidan ku ba" Maa ta kara tabbatar mata nan dai ta daura da shawarwari da hira masu sanyaya zuciya sai ga Inna da tazo mata wani cikin damuwa da sanyi jiki ta ware suna ta hira harda kyalkyalan dariya. Bayan kwana 2 Gwwggo Aisha ta had'a duk wasu 'yan kud'ad'e da suke hannun ta tare da sayar da wasu kayayyakin ta saboda ta samu isassun kud'in zuwa wajan boka, dama haka take duk tabi ta sayar da abinda take dasu dan ko dakin Inna Asabe yafi nata kyan gani domin ita ta fawwalawa Allah lamarin ta ta rungumi sana'an ta kuma alhmdlh tana samu daidai gwargwado domin tana sayan kayan daki da kadan kadan tana gyara dakin ta. Sun je wajan bokan ita da lantana da yake can jejin Goshe ko tsoro basa ji na yanda hanyoyin maiduguri suka lalace, sunyi sa'a sun same shi ya basu magani amma yace a abinci za'a zuba mishi na kwana 3 in dai har yaci abincin toh zai min wani irin tsana da bashi da iyaka ya min koran kare a gidan shi. Wani kullin maganin ya Kara miko musu yace shi wannan kuma a turare zasu saka Hajara ta rinka shafawa a duk lokacin da zata je kusa da shi , in har ya shaki kamshin toh shikenan an wuce gurin zata zama itace mace kad'ai a rayuwar shi ko uwar shi ba zai kara tuna ta ba. Cikin tsananin farincikin samun nasara ta dawo gida ta labartawa Hajara yanda sukayi da boka, nan kuwa ta hau murna kaman da gaske harda su rawanta wai ta kusa samun miji balarabe. *************** Kaman yanda ya saba kullum sai yaje ya gaida iyayen nashi yauma ya isa gidan nasu akan lokaci domin ya samu Abban shi a gida bai fita ba, cikin girmamawa ya isa gare shi ya zauna wajan kafafun shi sannan ya gaishe shi yana daura kan shi kan kafar Abba. Cike da so da kaunar tilon d'an nashi ya amsa yana mai shafa gashin kan shi, dan yanzu sosai suke shiri ba kaman da ba da kullum suke cikin rigima kan hallayyar shi ganin yayi auren yasa yake ganin ya natsu sosai. "Ina 'yata tana lafiya ko?" Abba ya tambaya bayan ya amsa gaisuwan nashi. "Tana nan lafiya Abba tace ma in gaishe ku" ya bashi amsa yana wani tsunne Kai kaman da gaske. "A'a ni gaisuwan nan ta ishe ni hakan nan tunda taki zuwa mu ganta koda yake bata da laifi kai ne kake mana rowan ta ko Hajiya?" Ya karasa yana maida hankalin sa kan Mom da take saukowa yanzu. Sai da ta tab'e baki ganin dukkan su basa kallon ta sannan ta kirkiro murmushi tare da karasawa gare su ta zauna kusa da Abban tana mai cewa " babu batun rowa ririta amaryar sa yake" ta karasa tana dariya kaman da gaske. Dariyan suma sukayi suka cigaba da hiran su har zuwa wani lokaci sannan ya mike yace zai tafi "Ya maganan da mukayi da kai sai yaushe zaka fara fitowa office?" Abba ya dakatar da shi. "Sai nan da 2 months" yace yana sosa keya, dariya suka mishi Abba yana " ja'iri wata 2 ai kaman kwana 2 ne yanzu zai zo ya wuce, amma ka tabbatar ka kawo min 'yata mun gaisa". Mom da duk haushi ya cika ta na me yasa Abba yake son gani na ta bud'i baki zatayi magana yayi saurin dakatar da ita wajan daga mata hannu ba dan taso ba tayi shiru tana gani har Zafar din ya fice zuciyar shi fari tass dama abinda yasa yace sai bayan wata 2 zai fara aiki kamin nan ya gama da chapter na ya Zama free man zaiyi abinda yake so. Ni kuwa bayan wannan incident daya faru tsakanin mu wanda ya kasa barin kwakwalwata bamu kara zama waje daya dashi ba sai dai da naji motsin shi zan l'eko in kare mishi kallo sometimes yana cin abinci sometimes kuma yana wannan danne- dannen shi a laptop, ni dai har yau ban san me yasa bana gajia da kallon shi ba. Yau tunda na tashi na gama aiki na zauna ina duba wani littafin Hadisi cikin litattafai na islamiya, wannan mayen kamshin nashi shi ya fara min sallama, wani irin zillo zuciya ta yayi kaman zai fad'o kasa jin wannan sassayan muryan yana cewa " ki shirya anjima da daddare zamu je ki gaida su Abba, nd saura in muka je kada ki kama kan ki kije kiyi ta musu kauyanci ki da kika saba kiga yanda zan tsaba miki ". Maimakon inji haushi ni dariya ma ya bani dan haka ban san lokacin da na saki wani kayataccen murmushi ba, wai nice zanyi mishi kauyanci ko ce mishi akayi daga kauye nake oho. Cike da takaici yake kallon yanda na sunkuyar da kai kasa ina murmushi, shifa wannan sabon dabi'a da na samu haushi yake bashi da duk abinda zaiyi min ko ya fad'a min baya bani haushi balle in nuna ko inyi kuka, in ya ganni ina kuka wani dad'i yake ji na musamman amma da yanzu bana nuna jin haushi sai yaji duk haushi ya kara cika shi. Cike da tsana ta ya hamb'are ya fice yana" duk abinda za'a mata sai ta zauna tanawa mutane dariya, mayya kawai ni dai ba zaki cinye ni ba" yana magana yana mai ficewa daga parlourn. Tashi nayi na karkad'e jikina still murmushin bai bar fuskata ba wai nice mayya hmmmm. Tunda yace zamu je gaida iyayen shi duk sai na kasa zaune na kasa tsaye ina tunanin me zan kai musu da zan burge su, abinka da masu kud'in nan ba komai zaka musu kayi gwanin ta ba. Duk tunani na ya tsaya ne kan girki, toh in banda girkin me nake dashi da zan kai musu, kitchen na shiga nayi tsaye ina tunanin what should I cook? Wai meye nawa da zan takura kai na kan sai na musu gwanin ta kwana 2 nan mantawa da nake cewa auren temporary nake zai iya sallama ta at any time tunda yanzu mun bawa wata d'aya baya, saurin kawar da wannan tunanin nayi saboda yanzu na tsani in tuno da hakan a cikin raina. Tunani na ya tsaya ne kan inyi musu abincin gargajiya maybe zasu fi son ci, ina da garin ndalayi da aka had'o min cikin gara ban tab'a amfani da shi ba,yau shi na d'auko na daura tukunya mai dan girma da ruwa dai-dai yanda nake so. Kamin ruwan ya tafasa na gyara kayan miyana na daura miyan a gefe, miyar kubewa danya da yaji zallar naman rago sannan na tuka tuwo bayan na wadata ruwan daya tafasa da man gyad'a, sabuwar warmers da ban tab'a amfani da su ba na ciro na zuba abincin a ciki bayan nayi malmala masu kyau sannan na Kara bin man su da man shanu na

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99