Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,521 words 0 views Progress saved
Download Book

Compiled By Umar Dalha Funtua. Copied By Ummee Yusuf. [8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAKE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_💃🏻NBA SONTA NAKE BA💃🏻 *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊 *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* _Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇 https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp _Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana gwiwa a wajen rubutu._ *BA SONTA NAKE BA* littafi ne daya kunshi darrusa na yau da kullum,ina rokon Allah kaman yanda na fara lafiya yasa na gama lafiya. Da fatan zaku bani hadin kai kaman yanda kuka saba. حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ يَحْيَى التَّمِيمِىُّ وَأَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِى شَيْبَةَ وَمُحَمَّدُ بْنُ الْعَلاَءِ الْهَمْدَانِىُّ جَمِيعًا عَنْ أَبِى مُعَاوِيَةَ - وَاللَّفْظُ لِيَحْيَى أَخْبَرَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ - عَنِ الأَعْمَشِ عَنْ إِبْرَاهِيمَ عَنْ عَلْقَمَةَ قَالَ كُنْتُ أَمْشِى مَعَ عَبْدِ اللَّهِ بِمِنًى فَلَقِيَهُ عُثْمَانُ فَقَامَ مَعَهُ يُحَدِّثُهُ فَقَالَ لَهُ عُثْمَانُ يَا أَبَا عَبْدِ الرَّحْمَنِ أَلاَ نُزَوِّجُكَ جَارِيَةً شَابَّةً لَعَلَّهَا تُذَكِّرُكَ بَعْضَ مَا مَضَى مِنْ زَمَانِكَ. قَالَ فَقَالَ عَبْدُ اللَّهِ لَئِنْ قُلْتَ ذَاكَ لَقَدْ قَالَ لَنَا رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- « يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ الْبَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصَّوْمِ فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ ». *It was narrated that `Alqamah said: "I was walking with Abdullah in Mina when he was met by Uthman. He stood and talked with him and Uthman said to him: `O Abu Abdur-ur-Rahman, shall we not marry you to a young girl who can remind you of the times past?` Abdullah said, `If that is what you are telling me, (let me tell you that) the Messenger of Allah (s.a.w) said to us: O young men, whoever among you can afford it, let him get married, for it is more effective in lowering the gaze and guarding one`s chastity. And whoever cannot afford it should fast, for it will be a shield for him."* Sahih Muslim *BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM* ________Hmmmmm bansan ta ina zan fara baku labarin na da yake cukuikuiye ba *BA SON TA NAKE BA* wannan Kalmar da na saba ji kenan a gidan mu har zuwa gidan aure na, bari dai in fara muku daga d'an farko yanda zaku fi fahimta. Suna na Fatima. Amma Inna ta na kira na da Zareefa a halin yanzu shekaru na basu fi 10 zuwa 11 ba muna shirye-shiryen rubuta common entrance a makarantan mu na boko sai dai yau tunda na shigo kuka nake sosai saboda cin mutuncin da akayi min yau har yayi yawa duk da ba yau aka fara min ba sai dai na yau d'in ya tsaya min a rai. Uniforms aka zo dasu ana rabawa daga gwarzon Governor mu professor Babagana Umara Zullum, harda jaka wadda ya kunshi note books, tex books crayon pen da sauran tarkacen da d'alibi zai bukata gefe d'aya kuma ga sandal da socks amma aka tsallake ni wai dan ban biya 200 na PTA ba duk da kasancewar nafi kowa bukatan wa'yan nan kayan domin uniform d'ina ya gama yagalgalewa. Basa tab'a ganewa Inna ta ina zata samu gudan 200 ta bani in kawo musu Ita da kyar take samo 30 da safe ta bani 20 in sayi alale wajan Maman Dije dake gidan mu 10 kuma ta bani a matsayin kud'in tara, toh a wannan halin 200 ba karamin kud'i bane a wajan mu. Kudin taran ma in na zo dashi sai in rasa abun saya dashi, gashi kiri-kiri ana mana girki a makaranta a rabawa kowa banda ni da ban san me na tare musu ba, bakin jinin Malamai prefect harda monitor nake dashi akan wannan 200 da bana kawowa yasa duk suke jin haushi na, ina ji ina gani za'a tsallake ni a hanani abincin nan wanda nake masa kallon kaman naman kaza suke ci sai randa suka ga dama suke bani bani, duk ranan da na samu ci nake kaman in had'a da hannu na. Abinci ne da ake rabawa ko kwatankwacin sa babu a gidan mu, dan wata ran alale mai kwai da hanta ake rabawa wata ran kuma jallof d'in doya ko macroni ko kuma na shinkafa da wake yaji manja, toh ina mu ina cin wannan kayan dad'in a wannan gidan namu na yawa. Abban mu matan shi 3, dan haka in gari ya waye kowa shi zai nemawa cinsa da 'ya'yan sa abinda zai ci babu ruwan Baban mu da d'aukan nauyin ahalin da Allah ya bashi duk ranan da Allah ya bashi zai sayo masara ko dawa a nika dayawa a rinka tuwo da daddare da safe da rana kuma kowa yaji da kan shi dan haka duk yayuna da kanne na wanda muke uba d'aya da cousins d'ina duk tallah suke dan rufin asiri amma ni Inna ta bata yarda da tallah ba duk da ni kad'ai ce wajan ta tana iya kokarin ta wajan ganin ta sauke duk wani nauyi daya rataya akan ta dai-dai karfin ta shiyasa kaf gidan mu babu masu zuwa boko ko islamiya sai ni kad'ai wanda 'yan gidan mu sukewa lak'abi da iyayi ne sai dare kuma muke zuwa makarantan Allo gaba d'ayan mu amma banda 'yan matan da suke tsayawa zance abin su. Kona dawo makaranta wata rana babu abinda zanci in Inna bata samu wankau tayi ba sai dai ta tura ni gidan su da yake makotaka da namu inci duk abinda ya sauwaka a wajan kakata kasancewar suma kaman gidan namu suke babu wadata sai dai su basu da yawa kaman gidan mu,ranan da ta samu kud'in wankau kuma ta kan bani hamsin in sayi garau-garau nan wajan Gwaggo Aisha ta d'an yarfa min a roba dan mugunta ko mai da yajin kirki bata zuba min kuma in na fita waje na saya ya zama abin magana da habaice-habaice shiyasa ko zan fita saya a waje Inna ta ke hanani. *BA SON TA NAKE BA* shine kullum Kalmar da Baban mu yake fad'awa Inna ta in wani abu ya faru a cikin gida kuma kayan takaici a gaban kowa yake fad'a mata hakan sauran matan gida suyi ta shewa ana kara habaice-habaice tun bani da wayo har nayi wayo na gane me hakan ke nufi kuma a bakin matan gidan mu na tsinta wai Kakana Abban Inna ta tsohon soja ne in ba'a biya su fensho ba wajan Baban mu yake neman rance har kudin suka taru ya kai Kakana ba zai iya biya ba wanda yasa dole ya bashi Inna ta shiyasa ko kad'an bamu isa mu d'aga murya kaman kowa a gidan ba,Inna ta in ba wani abu

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99