Chapter 25
Chapter 25
ta mishi dariya. A takaice mun kai good 1 hour sannan mukayi sallama ya wuce ni kuma na shigo gida cikin farinciki hannu na d'auke da sayayyar da yayi min. Ina shigowa zaure saura kad'an in zubar da kayan hannu na saboda firgita ganin mutum manne a jikin bango yana goge zufa, sai da na tabbatar Baban mu ne sannan na samu natsuwa amma kuma mamaki da tambaya fal cikin zuciya ta me kuma yau Baba yake a nan ? Hanyan fita ya nufa yana masifa kallon inda nake bai yi ba hakan ko ya kara saka ni cikin konkonto, a yanda nasan Baba da son dad'i amma yau ko kulanin baiyi ba bayan ga shopping bags a hannu na, juyawa nayi da niyyan shiga gida naji muryan Baban mu yana," wallahi Allah yau yaron nan ya cuce ni, in banda ina gudun abin kunya cikin anguwa kada a ce ga Mallam Hassan can yana fad'a da sirikin sa ba Allah da na nuna mishi ko ni waye, Aikin banza wa zai yiwa barazana har kofar gida har da wani sako kayan sojoji toh sai me...?" Dariya na tintsire da shi har da dukawa sai yanzu na gane me Baba yake a zaure, da kyar na tashi na kwashi kayana zuwa cikin gida. Bayan kwana 2 akayi bikin saukar mu a islamiyar mu wanda ya tara duban jama'a ciki kuwa har da Yaya na sai dangin Inna a 'yan gidan mu Inna Asabe ce kad'ai ta tafi dan Gwaggo Aisha cewa tayi karatun karuwanci dama nake shine yau kuma za'a je party toh ba da ita ba. Bajintar da Yaya na yayi ba a cewa komai kayan rabo kala-kala ya kawo aka raba harda na malamai suma nasu daban ga gifts nima daya kwaso min ba zasu lissafi ba duk da haka cewa yake komai ya min gani yake bai yi ba saboda sauke Al' Qurani mai girma ba abin wasa bane. A islamiyar ma na samu kyauta daban-daban saboda hazaka ta daga karshe taro ya watse bayan mun sha pics saboda tarihi. ************************* Wato ka mai da ni mutuniyar banza a gidan nan saboda ban isa in fada kaji ba ko, fisabillilahi ka kyauwa kan ka kenan?"cewar wata 'yar dattijuwa mai kamala da kyau da haiba wacce ba zata haura shekaru hamsin ba. Wani kyakkyawan saurayi ne zaune a gaban ta shi take takewa fad'a amma shiru yayi kan shi a kasa yana kallon lallausan rug da yake malale a katafaren parlour nasu wanda kallo daya zaka mishi ka kira shi da aljannan duniya domin babu ne kawai babu a ciki, just ku hasaso shi a cikin zuciyar ku domin in nace zan tsaya zayyano muku tsari da kyan gidan sai mu kusan cika novel din bamu gama ba Duk da kan shi a kasa yake bai hana ni hango dogon hancin sa ba ga sajen sa baki wuluk na lallausan gashin sa sun kewaye fuskar shi, gashin kan sa kuwa kaman na larabawa saboda laushi da tsantsi sai dai yayi mata wani aski wanda an kwashe daga gefe-gefe da keya sai tsakiya da ta gaba ne da gashi kana ganin gashin ka san ya sha gyara da kulawa wajan mai shi. "Zafar... Wai ba da kai nake magana ba ka min shiru" wannan kyakkyawar dattijuwar ta fad'a cikin tsawa. Wanda ta kira da Zafar ya d'ago kai masha Allah ashe da kan sa yake kasa ban ga komai ba sai yanzu. Zafar fari tas irin farin nan mai yellow yana da dogon hanci wanda ya kawata kyakkyawan fuskan shi ga maidaicin bakin sa mai d'auke da jajayen lips sun kara fiddo ainihin kyan fuskar sa, idon sa kuma kaman mai jin bacci suke a takaice Zafar ya had'u iya had'uwa sai dai ya kasance d'an shan minti ne kasancewar shi d'a tilo ga multi millionaire. A shagwab'e ya d'ago da kai yana d'an tale baki kaman d'an karamin yaro alhalin ya kai shekaru ashirin da takwas yana kallon mahaifiyar tashi da lumsassun idon shi da baturai sukewa lak'abi da sexy eyes ya ce," wai ya kuke so inyi ne Mom for god sake ni komai nayi kice bai yi ba, look at dis " yace yana nuna mata gashin kan sa sannan ya cigaba. "Wats wrong with it nayi wancan kunce baiyi ba nayi wannan ma kice baiyi ba then which 1 do u want me to do?" Ya karasa yana watsa hannayen sa cikin iska. Wacce ya kira da Mom ido kawai ta zuba mishi ta kasa cewa komai domin lamarin tilon dan nata ya fara bata tsoro a ce d'an da ka haifa shi zai rink'a mayar maka da magana haka, babu wanda yake shaka a gidan sai Abban shi, sanin haka yasa ta cewa," ok haka kace ko? Kaje kayi duk abinda kake so amma kafin ka fita inayi maka albishir da gobe Abban ka zai taso daga Portugal zuwa gida sai ka tanadi bayanin da zakayi mishi in ya ga askin naka". A rikice ya dawo kusa da ita, da ya kai har tsakiyan parlour da niyyan komawa part d'in shi yana zuwa ya zauna a gaban ta tare da d'aura hannayen shi duka 2 kan guiwoyin ta ya ce," na san ko Abba ya dawo my sweet Mom zata kare ni kaman yanda ta saba ko Mommy naaaa just once daga wannan shikenan ba zan kara ba I promise shima wannan dan zamu yi bachelor's eve na Musaddiq ne shiyasa". Murmushi tayi tana shafa gashin kan nashi ta ce," promise.. promise dai wanda ban san sau nawa aka yi min su ba remember jiya me kace?" Dafe goshin sa yayi yana d'an tuno yanda yake mata in taki yi mishi abu, zai fara yi mata ta dakatar dashi tana," bana son wannan shagwab'an naka jeka let me think about it" "Yesss.... dats my sweet Mom" yace yana d'an tsalle a gaban ta sannan ya fita da gudu yana dariya, itama dariyan take a zuciyar ta kuwa tana blaming kan ta da duk abinda Zafar yake itace sila domin a koda yaushe itace mai kare shi wajan Abban sa in yayi wani laifi, ita da kan ta bata jin dad'in abinda take wasu lokutan amma ya zata yi shine fa kad'ai kwan ta a duniya dan ma Allah ya tsare baya wasu mugayen dabi'un na 'yan zamani shi dai bar shi da zuwa parties da kula 'yan mata sai kuma son swagger. *Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*. [1/26, 7:04 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* *13* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99