Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

baki tun d'azu , ina biyu ne kawai harda wani ........ zaki kone mu shiga uku" na fad'a cikin kwaikwayon muryan ta, ta kai min duka na goje haka muka cigaba da shan ice cream muna hiran mu cikin raha.. Dije itace babban 'ya a wajan Maman Dije ta bani kusan shekaru biyu amma hakan bai hana mu zama kawaye ba domin yaran gidan dukan su iyayen su sun hana su wasa dani tun muna yara dan haka babu wani shakuwa ta 'yan uwan taka tsakanin na dasu sai dai kallon kallo. Ba Yaya na kad'ai ba nima na shiga damuwa sosai na rashin sa a kusa da ni, cikin kwana biyu da yayi baya nan duk sai na zama kaman ba ni ba abinda yafi tayar mun da hankali rashin samun sa a waya, duk da ya gaya min inda zai tafi ba service amma hakan bai hana ni kwana da waya a hannu ina gwadawa ba, Inna tana ankare dani amma bata ce min cikan ki akai ba. A ranan da ya cika na uku ne kiran shi ya shigo min yana fara ringing na d'aga cikin d'auki na ce," wayyoo Yaya naaa" "Na'am k'anwa taaaa" shima yaja kaman yanda nake jan nashi. Dariya muka sanya dukkan mu sai da mukayi mai isar mu kaman sabobbin kamu sannan ya ce," na kusan shigowa gari k'anwa ta, insha Allah gobe war haka muna tare" Tsalle na daka da wayan a kunne na na ce," yessss Alhamdullilahi Allah ya shigo da ku lafiya Yaya na" da Ameen ya amsa sannan ya katse kiran. Dije da take gefe tana min dariya tare da min signal ga Maman su a kusa inyi a hankali ko kula ta banyi ba, ita kuma Maman Dije murmushi kawai tayi tana girgiza kai ta shige kitchen d'in ta ta kyale mu tana mamakin wai yarinya kamata da iya soyayya, hmmm duniya kenan in da ran ka zaka sha kallo. Zama nayi tare da rafka tagumi ina tunanin ya kamata nima ko sau d'aya ne in kyautata mishi yanda yake kyautata min kullum ko ba komai shima zai ji na damu da shi. "Ke kuma lafiya, ba yanzu naga kina murnan masoyi zai dawo ba kuma inga kin zabga tagumi kina tunani kaman wacce akaiwa mutuwa?" Cewar Dije kenan. "Dije kawai so nake inyi wani abu da zai faranta ran Yaya na tunda bai tab'a tafiya ba shiyasa nake son inyi wani abu na tarban shi". "Gaskiya kinyi tunani mai kyau Zareefa in dai akwai kud'i a hannun ki ni zan taya ki ko abinci ne kiyi mishi". Cikin jin dad'i na amsa mata da akwai kud'i a waje na, nan da nan muka tsara yanda zamuyi da abinda zamu girka masa. Da washe gari tare muka je kasuwa muka sayo doya da nama sai kwai creast d'aya da mai muka dawo, gidan Maa muka kai kayan da muka sayo da taimakon Dije mukayi mishi yam balls da kwai cikin kwai da yake shine sana'an da suke ta kware sosai, Maa kuma tayi mana dambun nama mai dad'in gaske. 'Yan kulolli da Inna ta fara min tarun su nan gidan Maa na fito da set d'aya muka zuzzuba a ciki muka shirya a cikin tiren plastic mai kyau shima cikin kayan tarun muka d'auko. "Kinga yanda kayan nan sukayi kyau kuwa kuma sunyi dad'i da zamu had'a da kunun aya mai sanyi zai fi tafiya" Dije ta kawo sabon shawara nima ba b'ata lokaci na amince sanin yanda shima Dije ta kware da yin sa shima suna sayarwa amma a lokacin zafi. Da yake mu biyu ne bamu b'ata lokaci ba shima muka had'a ta muka zuba jug na glass haddade muka saka kankara, ni sai a ranan ma nasan na san cewa Inna tayi min taru dayawa haka, sai da muka gama tsab sannan muka wuce gida dan inyi wanka in shirya ita kuma Dije zata fita sana'a ta. Sai da na shigo Inna ta rutsa ni da tambayoyi ina naje tun dazu? Na amsa mata da ina gidan Maa tace karya nake bata yarda ba ta kira yaro ina gani ta tura gidan Maa dan a tambayo mata ni dai na shige wanka dan ina gudun kada Yaya na ya dawo ban shirya ba. Ko da na fito daga wankan bata kuma kula ni ba da alama an tambayo mata Maa,sai da nayi sallah naci ado na da riga da skirt na lace pure cotton dark blue ya sha adon flowers pink, sosai kayan suka min kyau domin Yaya na ya iya zab'en kayan da zasu yi min kyau. Inna duk tana kallon sabon falli da nake bata min magana ba sai da na gama sannan ta zaunar da ni ta fara min nasiha kan rike mutunci na na 'ya mace a duk inda nake, duk da ta amince da Abdulbasit amma tace kada in kuskura in bar shi ya rike min ko da hannu nane tunda shi ba muharrami na bane kuma ba aure na yayi ba, in ko na bari hakan ta kasance toh tabbas ciki ne zai bayyana a tare da ni wanda har jikokina zan barwa wannan bakin fenti. Sosai Inna tayi min nasiha daya kashe min jiki ba shiri na fad'a mata duk abinda mukayi a gidan Maa, nan tace ai ba wani abu bane kyautatawa wanda yake kyautata maka,kar inji komai in dan wannan ne ko yaushe na tashi yi inyi anan gida bai sai naje gidan Maa ba. Cikin jin dad'in fahimta da tayi muka zauna muna hira cikin dabara ta cigaba da wayar min kai akan zaman duniya da kalubalen da yawanci 'yan mata ke fuskan ta wajan kwad'ayi da bin maza kuma daki-daki suke shiga kaina, kiran wayan Yaya na ne ya katse mana hiran na saka hijabi na fito. Center kofan gidan mu yake kallo fuskar shi d'auke da murmushi na musamman, yana gani na ya kara fad'ad'a murmushi nasa cikin sabon takun da na koya saboda shi na karaso gaban shi sai dai ina zuwa na b'ata fuska ta. Cikin d'an damuwa yake tambaya ta me ya faru kuma nake b'ata fuska? "Ba kai bane yau baka kallon waya na fito balle in tsorata ka yanda na saba" na bashi amsa a shagwab'e. Dariya yayi yana shafa gashin kansa da hannun sa ya ce," ayi min afuwa k'anwa ta yau d'in ne nayi missing d'inki dayawa shiyasa na kasa hakuri har ki ban tsoro" "Nima nayi missing d'inka sosai Yaya naaa" "Ina son ki k'anwa ta" Rufe fuska ta nayi ina dariya kasa-kasa sannan na bashi amsa da ," nima ina son ka Yaya naaa". A take na bud'e fuska ta tunawa da nayi da abincin da na had'aa mishi a gidan Maa. "Dan Allah bani minti biyu ina zuwa" ban jira amsar shi ba nayi gaba na kira Bakura wani yaron makotan mu muka tafi tare na d'aura mishi tiren akai ni kuma na d'auko jug d'in muka dawo wajan shi. Tunda muka fito yake kallo na da mamaki har muka iso bai iya d'auke idan shi daga kaina ba, "Ban san a ina zan ajiye maka ka ci ba,ko zaure zan saka maka tabarma?" Girgiza kai yayi tare da nuna min motan

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99