Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

mahaifiyar ki tun muna kanana har zuwa girman mu" "Koma menene Dije su d'in 'yan uwa na ne, jini d'aya yake yawo a jikin mu daurewa kawai nake ina share su amma ina kaunar su har cikin raina ina kuma sha'awa in ga mun had'a kan mu kaman sauran 'yan uwa" Hawayen da ya zubo min na share na mike na kama hanyan bangaren mu itama Dije ko motsi kasawa tayi dan maganganu na sun kashe mata jiki,ko da na shiga d'akin mu na samu Inna zaune gefen gado ta rafka tagumi da alamu itama taji zancen kenan. "Tun d'azu ake kiran wayan ki" ta ce min ba tare da ta sauke tagumin ba saboda wannan al'amari ya bata mamaki da tsoro samarin yanzu mayaudara ne kuma macuta ne, in banda cuta kazo da wata siffa da suna dan a baka mata me yasa ba zai zo a yanda yake ba? Ko da yake Maman Dije ta ce wai sun riga sun nunawa duniya cewa in ba mai kud'i ba akai kasuwa shine yasa shi zuwa da wannan siffa. Ajiyar zuciya ta sauke wanda sai da na juya na kalle ta dama rply na tex nake rubutawa 'yar ajin mu a islamiya ta kira bana kusa shine ta min tex tana min tuni kan abubuwa da muka shirya na walimar mu. "Inna lafiya kuwa na gan ki haka?" Na tambaya. "Hmmmm ba komai je ki wanke min hijabi na da da yake cikin bukiti a waje" da toh na amsa na fita wankin. Ina fara wankin naga Gwaggo Aisha sun shigo da kannen ta 2 duk sunyi wujiga-wujiga ko kallon inda nake ba suyi ba suka wuce, a zuciya ta na ce," chab Gwaggo Aisha ana cikin tashin hankali tunda bata harare ni ko ta tsaya ta zage ni ba, lalle yau tana cikin matsala, d'aki suka shige suna neman mafita. Har gari ya waye ba'a cimma abu d'aya ba sai shige da fice suke, sun samu Baban mu da maganan yace toh me zai mata, ta riga da ta fita a hannun sa lafiya dan haka sauran ya rage musu ita da mijin ta. Gwaggo Aisha takaici ya hana ta sauran sauran bayanin nashi tayi ficewar ta, ta rasa ina zata kai kukan ta a share mata hawaye, babban burin ta shine a raba auren domin jiya da daddare ita da kannen ta daga gidan Hajaran suke suka ja mata kunnen kada ta yarda ta bashi kan ta duk rintsi duk wuya dan gobe-goben za'a raba auren nasu sai gashi har sha biyu ta kusa babu alamun nasara ko kad'an. Gwaggo Aisha bata gama shiga tashin hankali ba sai da d'ayan kanwar ta da ta tura gidan Hajara dan a dubo mata lafiyr ta ta dawo da mummunan labarin cewa Haladu yayi nasaran kusantan Hajara jina-jina suka same ta abun babu kyan gani ko taimaka mata bai tsaya ba ya tsallake ta yayi tafiyar shi. "Yanzu fisabillilahi duk fad'an da muka yi mata sai da ta sakewa wannan mayaudarin jiki ya gama da ita?" Gwaggo Aisha ke tambaya tana goge hawaye da gefe zanin ta. "Ba laifin ta ba ne shi mijin ne tantiri, ta bamu labarin komai cewa da ta fara mishi taurin kai shine d'aure ta a jikin gado yayi abinda ya ga dama da ita wai bata isa ta hana shi more kud'in sa ba" 'yar uwar ta ta bata amsa. "Amma wannan yaro anyi tsinanne Allah ya isa tsakani da shi, ina zan shiga da wannan abin kunyan, kayyah " yanzu kam kuka Gwaggo Aisha take tsakani da Allah tana tunanin tayaya zata kalli idon 'yan gidan bayan duk abubuwa da tayi musu wai ita 'yar ta zata auri mai mota. "Mama kada ki tada hankalin ki domin nayi miki alkawarin saka ki farinciki, ba zan tab'a kula kowa ba kuma ba zan auri talaka ba sai mai kud'i" Jamila ke fad'an haka da take sauraron su tun d'azu ba tare da sun sani ba,d UK kallon juna suka tsaya yi babu wanda ya iya bata amsa sai dai ita Gwaggo Aisha ido ta zuba mata tana nazari tare da hasko yiwuwa da nasara a cikin abinda ta fad'a domin Jameela tafi Hajara kyau da tsarin jiki nesa ba kusa ba. Haka akayi wannan wunin a tsaye babu wanda ya lek'a gidan Amarya wasu ma saboda bakinciki a ranan suka koma inda suka fito shiyasa gidan namu ya zama shiru kaman ba biki ake ba. Bayan kwana 2 da bikin Hajara Yaya na yazo da rana bayan azahar cikin kananan kaya wandon kaman na sojoji sai bakin t shirt da bakin glass sosai yayi kyau, muna hira a kofar gidan mu yana tambaya ta me da me nake bukata a walimar saukar mu? Ni kuma ina ce mishi bana bukatan komai duk abinda ake bukata mun gama shirya su. A wannan lokacin ashe Baba yana gida ya dawo saboda wata bukatar shi lokacin da yazo Yaya na bai zo ba yana ciki ya zo dan haka bai san da zuwan shi ba,yana d'aki Gwaggo Aisha tabi shi tana magiya akan yayi wani abu akan al'amarin Hajara a raba auren domin muddin tana raye ba zata tab'a barin auran nan ya dad'e ba. Bata san duk haushi ya cika shi ba tazo ta ishe shi da surutu alhalin shi in ya tuna tsoro ya hana shi gaisawa da Yaya na da yanzu yana cikin kud'i yanzu gashi bashi da kud'i a hannu, tsaki yaja yana bin ta da mugun kallo ya ce," ke Aisha wai wace irin mace ce ke da zaran kin ga mutum ya shigo gida sai ki bi shi da korafin ki na banza da na wofi yarinya tana gidan mijin ta shine kike neman wai ni uban ta inje in fito da ita wannan wani irin rashin kan gado ne, toh ba dani ba wallahi kije can ki gama haukan ki kada ki kara tunkara ta da wannan iya shegen ko kuma ranki yayi mugun b'aci". Yana gama maganan shi ya mike a fusace zai fita ya juyo ya ce," ba sai kin kara gani na a gidan ba balle ki zo ki takura ni" Fita yayi rai a b'ace yana ta masifa shi yasa kai zai fita da sauri ya koma baya yana tunanin anya idon shi dai-dai ya nuna mishi kuwa? Kara lek'a kan shi waje yayi yaga dai da gaske ne Yaya na ya gani fuska a murtuke wai shi ala dole yayi fushi me yasa ban fad'a mishi maganan saukar namu ya d'auki nauyin komai na ba nayi da kai na. "Innalillahi wa inna ilahi rajiun wai shi wannan yaro banda bala'i irin nasu na sojoji meya kawo shi da rana tsaka yana muzurai sai kace anyi mishi dole" Baba ke fad'in haka bayan ya koma cikin zaure ya manne da bango wai duk dan kada Yaya na ya gan shi. Da kyar na shawo kan sa ya daina fushin muka ci gaba da hiran mu cikin annashuwa da shaukin soyayya, abinda bamu sani ba ashe Baba yana nan mak'ale a zaure yana jiran tafiyan Yaya na ya samu shima ya tafi majalisa, yaki komawa cikin gida kuma saboda rigimar su da Gwaggo Aisha kada taga ya koma

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99