Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,308 words 0 views Progress saved
Download Book

barka da war haka ya kyakkyawan d'an saurayi". Fasa jan motan yayi ya tsaya kallon ta da wani irin fuska sannan ya ce," meke tafe dake?". Juya ido tayi mishi irin na jan hankalin nan sannan ta ce," haba yanzu har sai nayi maka bayanin abinda yake tafe dani,me budurwa zata nema a wajan saurayi? Koda yake bari in fito in fad'a maka yanda zaka gane. Naga kana wahalar da kanka akan wancan 'yar karamar yarinya, bayan gani na had'a duk abinda kake nema zan saka ka farinciki domin babu abinda zaka nema a waje na ka rasa" ta karasa tana kara matsowa jikin motan tana girgiza mishi kirji. Kallon takaici da kyama ya bita dashi sannan ya ce," pls matsa min ka jikin mota kada kisa min k'azanta a jiki". Kasa matsawa tayi ta tsaya da idanuwa a waje tana kallon shi dan tunda take ba'a tab'a ci mata mutunci haka ba duk yanda taci kwalliya nan yace wai zata shafawa motan shi k'azanta , a firgice ta koma baya jin ya fisgi motan da matukar gudu saura kad'an ya take mata k'afa ya tafi ya bar ta a wajan. Da hawaye shame-shame ta shigo gida tun daga bakin kofa ta fara ihu tana magana," ni Gwaggo wallahi baki ga wulakaci......" Da hannu Gwaggo Aisha tayi mata alama da tayi shiru, kama hannun ta tayi suka shige d'aki. A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah dan yanzu har munyi exam na third term muna hutu in mun koma kuma zamu shiga j.s.s 2. Ranan nan muna wasa a k'ofar gida da kawaye na 'yan mak'otan mu naga Baban mu yana dawo wa gida ban kula ba dan shima ba kulanin yake ba kuma ya tsani in kula shi dan ma yanzu da sauki naga ya rage tsana da yake nuna min. Bulala naga ya d'auka yayi kaina gadan-gadan zai zane ni bansan hawa ba ban san sauk'a ba, da gudu na kwasa nayi cikin gida ban tsaya a tsakar gidan ba na wuce d'akin mu sanin cewa baya tab'a biyo ni, Inna tana raba gasassun kaji da Abdulbasit ya kawo na fad'a d'akin ina haki. Inna barin abinda take tayi ta kama min fad'an waye na tsokono zan fad'o mata d'aki haka? "Inna wallahi ba tsokana nayi ba muna wasa ne sai naga Baban mu....." Had'iye sauran maganan nayi ganin Baban ya d'aga labule ya shigo, bani ba har Inna sai da ta zaro ido tana kallon shi da matukar mamaki. "Ke yanzu Bintu haka ake tarbiyan 'ya mace yarinya ta fara girma amma ki bar ta tana wasa a waje sai kace namiji" yana maganan ne idon shi na yawo a d'akin har ya sauk'a kan kajin da suke gaban inna, mukut ya had'iye yawu tare da tsura musu ido shiri. "Toh Mallam ayi hakuri insha Allah za'a kiyaye gaba" tana gama fad'an haka ta ture tiren da kajin suke ciki gefe tare da rufewa da wani tiren. *Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*. [9/8, 5:01 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊 *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Abin da ake fada idan za a yanka dabba, ko za a soke ta.* بِسْمِ اللهِ واللهُ أَكْبَرُ اللَّهُمَّ مِنْكَ ولَكَ اللَّهُمَّ تَقَبَّلْ مِنِّي. Bismil-lah wallahu akbar, allahumma minka walak, allahumma taqabbal minnee. Da sunan Allah, kuma Allah ne Mafi Girma. Ya Allah! (wannan dabba) daga gare Ka take, kuma mallakarka ce. Ya Allah! Ka karba daga gare ni. *~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* _Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇 https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp _Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._ *8* Karasa shigowa d'akin Baba yayi tare da yiwa kan shi masauki kan katifan mu yana kallon rufaffen tiren ya ce," haba Bintu yanzu iya abinda zaki ce kenan, Fateema ta fara girma sai da saka ido sosai fa". Cike da mamakin furucin sa ta ce," naji Mallam za'a kiyaye gaba insha Allah" a zuciyar ta kuwa bata daina mamakin wannan sabon al'amarin ba domin ita dai tunda take a gidan bata tab'a ganin ya damu da 'ya'yan matan shi da yake so ba balle 'yar ta da kullum sai ya tsaya a tsakar gida yace ba son su yake ba shiru ne ya biyo baya a d'akin,ni ina can bayan Inna ta saboda tsoron bulala duk da ya ajiye ta tuntuni naki fitowa, ita kuma Inna al'ajabin me ya zaunar dashi har yanzu a d'akin take gashi tana so ta gama rabon kazan in kaiwa wayan da take bawa kullum. Mun kai minti kusan ashirin muna zaune shiru babu mai magana shi ya gaji da zaman kurame da muke ya d'an gyara zama yana kallon tiren ta gefen ido ya ce," naga kaman aiki kike Bintu dana shigo ko, toh ki karasa abin ki mana, in ta nine babu matsala Wallahi". "Haba Mallam ba haka bane na riga da na gama ne shiyasa". Ta amsa mishi. "Kin gama, me kika gama?" Ya tambaya tare da kafe tiren da ido. "Rabo nake kuma na gama saura in bawa Zareefa ta kai" Inna ta amsa mishi cikin k'osawa da zaman nashi a d'akin. "Toh su waye kuma zaki aikawa?" "Maman Dije da Maa saboda sunyi yawa ga Zareefa ba ci take ba shiyasa nake aika musu". "Ikon Allah amma Bintu kina da abin mamaki, ya za'ayi ki aikawa wasu alhalin ga 'yan gida nan, ko kin manta da nine?" Cike da takaicin halin sa ta girgiza mishi kai sannan ta d'auko wani d'an gutsuri kad'an ta mika mishi jiki na rawa ya karb'a ya fara ci yana," kai amma Bintu baki da dama yanzu haka kike cin dad'i kuma ki manta uban 'yar ki?" Ita yanzu inna halin nashi tsoro ya fara bata ya za'ayi kana magidanci mai iyali baka damu da ka samu ka kawo musu ba sai dai in ka gani a wajan su jiki na rawa ka karb'a, dubi yanda yanzu jiki na rawa yake neman a bashi kaza bai damu da tambayan a ina kika samu ba, sata ko maita ko karuwanci duk kiyi in dai zaki bashi to kece ma 'yar gaban goshin sa. "Dama

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99