Chapter 45
Chapter 45
daidai da shi, kamin in samu amsan da zan bashi naji muryan Inna a kaina tana " baki ji bane ana kiran ki kikayiwa mutane shiru ko duk salon wulakanci ne haka, wato duk maganganun dana gaya miki ta bayan kunne suke wucewa ko?" Kamin in bata amsa ta cewa yaron yaje yace tana zuwa, shi kuwa ya amsa da toh ya fita abinsa. Itama kitchen ta koma ba tare da ta kara kallon inda nake ba, hannu nasa na goge hawayen da suka zubo min sannnan na mike na d'auki hijabi na dake kan kujera na saka na kama hanyan fita nima. Har na kai hannu zan bud'e kofa naji muryan Inna a bayana tace" ki tabbatar kin shigo dashi parlour baki na Baban ku kada ki bar shi a waje kuma in kun shigo ki zo ki kai mishi ruwa". Da toh na amsa na fita, ina jan kafa har na fita waje na tsaya a kofar gidan mu da yanzu ya koma gate, na kusan minti uku tsaye a wajan ina kallon motan banida niyyan karasawa, shima kuma ko fitowa bai da niyyan yi balle in saka ran zai fito. Tunawa da yanda naga Inna ta b'ata ran ta d'azu yasa na fara takawa a hankali kaman mai tsoron kasan har na isa jikin motan na tsaya. Sauke glass d'in motan yayi yana min kallon up nd down fuskar shi d'auke da wannan shu'umin murmushin sa na gefen baki " 'yar Mallam Ni kike jira in je in same ki kenan, baki san cewa duk zuwan da zaki ga nayi nan dalili yake kawo Ni ba wai dan kin isa ba...." "Kaman yanda nima dalili ne yake sakani fitowa ba dan kana gaba na" na katse shi nima ba tare da na bari ya gama ba. "Really!!! I like ur courage, ki cigaba but ki rike a ran ki cewa zaki gane kuskuren ki when we are together under the same roof" yace har yana wani cize lebe. Kaina na kawar gefe ina son bashi amsa amma abinda nake hangowa a nesa damu kuma cikin d'an duhu shiya d'auke min hankali har na kasa kula shi, shima ganin hankalin na baya tare dani yasa ya fito tare da sauke kayan da ya kawo ya kira yara da suke wasan su a gefe yace su shigar min dashi cikin gida. Shiga motan shi yayi ya tayar yayi revise, karan motan shi da naji shiya da na mayar da hankali na kan motan ba tare da ya kara ko kallon inda nake ba yaja motan shi ya tafi na raka shi da ido, sai da ya kusan b'ace min sannan na dawo da ido na wajan dana d'auke sai dai Kuma yanzun naga wayam babu kowa a wajan sai duhu da ya kara mamaye wajan. Dafe Kai na nayi da naji yana juya min saboda tsananin ciwo da yake min , da kyar naja kafafu na da suka min nauyi na nufi gida ina mai mamakin ya akayi Inga mutum kuma lokaci d'aya kuma ya b'ace, ko dan na kasa cire shi a raina shiyasa yake min gizo. [6/16, 9:15 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *26&27* Haka na shigo ciki hannuna dafe da kaina, ragwajab na zube akan kujera ina lumshe ido ba tare da na lura da kayan da aka shigo da su ba Inna ta saka su a gaba tana aikin kallo. "Ban san yaushe kika samo wannan halin na rashin ji ba Zareefa, yanzu duk maganan da na gaya miki amma babu wanda kika d'auka kika bar bawan Allah nan a waje ko balle ki kai mishi ruwan sha?" Ban iya bata amsa ba sai goge hawaye da suka ki tsayawa nake dan na san ba lalle ne ta amince da abin da zan fad'a ba kasancewar bata san komai akai ba, nima kallon kayan da ban san daga ina suka zo ba nake domin ko za'a yanka ni ba zan iya cewa shi ne ya kawo su ba. "Kai jama'a wannan lodin kaya daya kawo su kuma na menene, uhum harda su gwalagwalai kuma da alamu na fitan biki ne ko?" Na tsinkayi muryar Inna ta katse min zancen zucin da nake. Bani da mafitar da ta wuce na amsa mata da " eh " tunda yanzu na fahimci daga ina kayan suka fito. "Toh Masha Allah amma hidiman nasu yayi yawa bana so gaskiya ki gaya mishi su rage hakan nan kinji?" Nan ma dai gyad'a mata kan nayi ina mamakin dukiya da aka narkar wajan sayan kayan nan. Nan na kwanta kan kujera duk abin duniya ya ishe ni na rasa ya zanyi da rayuwata, ban tab'a kawowa a raina zan shiga cikin irin tashin hankalin makamancin wannan ba A kwana a tashi babu wuya wajan Allah dan yau shine karshen gyaran fata da ake min sai lalle da aka shiga yarfa min na jan lalle gwanin sha'awa taso a yi min kitso nace mata bana so ta bar min gashi na haka, ba dan taso ba ta kyale ni suka maida hankali kan lallen. Sai bayan sallah isha'i muka samu daman komawa gida ta d'eba min wasu kayan gyaran tace in rinka yi a gida tunda auren saura kwana 3, karb'a kawai nayi na amsa mata da toh amma ba dan ina da niyyan yi ba. A kofar gida suka sauke ni Maryam bata shiga ba saboda dare yayi suka wuce tana ta santin lallen da akayi mata wai yayi kyau, ni dai ban iya biye mata na juya zuwa gida abina kasancewar na kwaso gajiya. Mutane na gani cike a cikin gidan mu ana ta cece kuce kuma kana jin maganan kasan kaman fad'a ake , d'an d'aga kai na nayi naga matan gidan mu ne harda makota, ban kara gigin d'aga kai na ba na wuce b'angaren mu tunda banga Inna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99