Skip to content

Chapter 80

Chapter 80

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,188 words 0 views Progress saved
Download Book

fashe da kuka sosai jin ta ambaci sunan waya nace " yanzu Baban mu yana cikin wannan halin shine babu wanda ya kira ni dan a gaya min?" "Baban ku karami shi ya hana a gaya miki sanin cewa ba zaki tab'a kwantar da hankalin ki ba dole kice zaki fito shi kuma baya son fitowan naki saboda ko cikakken wata 3 baki yi a d'akin ki ba" Inna Asabe ce ta bani amsa a daidai wannan lokaci kuma Baban mu karami da Zafar suka shigo tare da sallama. Amsawa su Inna sukayi suna gyara lullub'in jikin su ya durkusa har kasa ya fara gaishe su kai a k'asa, amsawa sukayi suma kawunan nasu a kasa sun kasa kallon shi a zuciya ta na fara gulman shi ina dube shi yanda yake ta tsunne kai kaman da gaske. Suna gama gaisawa Baban mu karami yaja shi zuwa b'angaren Baban mu da yake a rufe ya bud'e suka shige ciki, bayan wucewar su Inna ta ture ni daga jikin ta tana " ke Kam ban san ranan da zakiyi hankali ba ya zaku taho tare da mutum ki shigo ki bar shi a waje ba tare kinyi mishi iso ba?" Baki na turo mata na shagwab'a zanyi magana ta nuna min hanyan ciki tare da had'e fuska, banyi gardama ba na juya zan shiga kenan naji muryan Hajara cikin ihu ta ambaci suna na nima na juyo cikin murna ina amsa mata da d'an karfi ta taho cikin sauri muka rungume juna sannan muka shige ciki su Inna kuma suka cigaba da aikin su. A can b'angaren Baban mu kuma koda suka shiga Zafar zubewa ya karayi a k'asa ya fara gaida shi cikin sauri Baban mu karami ya dakatar dashi yana haba ya zauna akan kujera mana ai sun riga sun gaisa a waje. Tashi yayi ya zauna amma bai hau kan kujeran ba ya sunkuyar da kai yana sauraron Baban Dije daya fara koro mishi bayanin yanda al'amarin ya faru da irin wahalhalun da suka sha amma ko takamaimai inda yake basu sani ba balle akai ga maganan fito dashi. "Tun farko da na samu labari da ba zai kai har war haka a hannun su ba kasan wani lokacin mutane suna yiwa mutum cune su Kuma ba zasu bi diddigi ba su kama mutum su jefa cikin barracks d'in su shikenan in mutum bashida gata sai a nemi labarin shima a rasa but insha Allah akwai abokina da mukayi karatu tare a abroad Baban shi Marshal ne zanyi mishi magana in Allah ya yarda komai zai zo karshe" . Cike da farinciki Baban mu karami ya fara mishi godiya amma ya dakatar dashi yana " haba nima ai Baba nane dan bana son Abba na yaji labarin ne saboda wasu dalilai amma da waya kawai zaiyi ba tare da mutum yaje ba zasu sako shi". Nan ma Baban Dije gyad'a mishi Kai yake cike da gamsuwa da bayanin nashi domin karshen ta in Abban Zafar d'in yaji wannan labarin babu dad'i ko dan kare mutuncin sa hakan yana da kyau, sai yaji Zafar d'in ya kara birge shi . Sun dan kara tattaunawa sannan yace zai tafi wajan friend din nashi duk yanda sukayi zai zo musu da labari kamin nan nima zai barni anan sai in ya dawo sai mu koma tare, har bakin gate ya rako shi sannan suka rabu. Ni kuma muna parlour Inna da ya sha gyara sai kamshin turaren wutan sandal yake nake ce ma Hajara " ni dai nayi fushi tunda irin wannan abu ya faru ace harda ke wajan masu boye min, ba dan Dije ta Kira ni tayi min jaje ba Ina can ban san me yake faruwa ba aiko ba abinda zan iya yi zan taya shi da addu'a". " Ke ni tunda abun ya faru da washe gari naso a fad'a miki ko dan mijin ki kila zai iya yin wani abu amma Baban Dije ya hana kuma yayi gargadi kan kada a kuskura a gaya miki wai yaushe aka miki aure " Hajara ta tari numfashi na. Haka muka yini muna ta hiran mu da Hajara a parlour Inna har kusan Azhar sannan Maa da yan uwan Baba da suke gidan ta suka shigo nan suma suka hau murnan zuwa na daga baya kuma muka jajantawa juna aka zauna ana maida abinda ya faru har wannan lokaci Gwaggo Aisha tana ciki bata leko ba duk da hayaniyan mutane da ya cika gidan dan harda makota duk sun shisshigo. Kasa hakuri nayi na sassauta murya na tambayi Hajara ko ina take? Ita kuwa cewa tayi ta fita anguwa tunda sassafe ta boye min, ni kuwa abin ya bani mamaki ace ana cikin wannabe halin har ta iya zuwa anguwa. Zafar tun a mota ya kira abokin shi mai suna Hamis kan yana Ina? "Ina gida " ya amsa mishi bai bari ya Kara cewa wani abu ba ya katse kiran tare da yin hanyan Pori dan a wannan anguwan yake da zama, tafiyan kusan minti 40 ya kawo shi kofar gidan Hamis horn d'aya kawai yayi mai gadi ya bud'e mishi gate ya shigo hadadden gidan daya qawatu da flowers kana ganin gidan kasan shima ya taka kasa . Parking yayi a wadatattacen parking space na gidan ya fito ya nufi cikin gidan cikin takun katsaita da ya zama jikin shi, door bell d'in ya danna ko second 30 ba'ayi ba aka bud'e kofan wani matashin saurayi da ba zai wuce sa'an shi ya bayyana a gaban shi yana murmushi yace " wai da gaske kake dama zaka zo, ni wallahi ban d'auki abin ma da gaske ba sai da gan ka da idona" ya karasa yana bashi hanya . Shiga yayi ciki bakin shi d'auke da sallama bai kula abinda Hamis d'in yake ce mishi ba, shima Hamis d'in murmushi yayi yabi bayan shi bayan ya rufe kofan, anan hadadden parlour nashi suka iske kyakkyawar matar shi da cute kids d'in su mace da namiji sun baza toys a tsakiyan parlorn suna ta wasa abin su gwanin sha'awa. Gaishe shi sukayi da kanuri ya amsa musu yana musu murmushi maman su ma gaishe shi tayi sannan ta tattara kayan wasan yaran tayi ta kai su d'akin su sannan ta had'o drinks ta kawo wa Zafar ta shige ciki. Gaisawar su ta abokai sukayi Hamis na kara tsokan shi amma bai tanka ba ya shiga yi mishi bayanin abinda yake tafe da shi. "Hahhh dama na sani haka kawai ba zaka tuna dani har ka kawo min ziyara ba saida dalili" nan ma bai ce mishi uffan ba sai ma kara daure fuska daya karayi dan ya riga ya san dole sai Hamis ya mishi iskanci kamin ya saurare shi. Haka ko ya karaci neman maganan shi Zafar bai kula shi ba daga baya kuma ya koma serious suka fara magana akan abinda ya kai Zafar d'in gidan sa. "Ban san me yasa ba yanzu duniya ta lalace da zallan mugunta, mu talakwan ma kenan da ace wani mai mulki ne yayi hakan sai ace dan Allah ya bashi saurauta yake taka mutane. "Mutum ya san shi kad'ai ya shuka tsiyar shi amma in yaga abun zai rufta

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99