Chapter 93
Chapter 93
k'asa. Karasa shiga kitchen d'in nayi na ajiye kayan hannu na sannan na fara gyarawa ina yi ina maganan zuci" ina ma ace kulawar da yake bani da kuma soyayya da yake nuna min da gaske ne, dan ni kam kullum soyayyar shi ƙaruwa take a zuciyata sai dai nasan abin da yasa yake wannan draman dan ya samu jiki na ne, kuma na san yana samu ni kuma na gama yawo domin lokacin da ya d'ibawa auren mu ya kusa cika". Ras-ras naji zuciyata tana bugawa, fargaban rabuwa da shi ce cike da zuciyar, ina ma zamu kasance ne har abada, domin a yanzu bani da burin daya wuce in ganmu tare ya kasance muna tare na har abada, bani da burin daya wuce in jini a jikin sa. A kullum shauƙin son kasancewa dashi ninkuwa yake a zuciyata da gangan jikina sosai nake kai zuciyata nesa wajan ganin banyi wani abin a gaban shi ba, dan in yana wani abin ji nake kaman in had'iye shi in huta. maganan zuci da nake yasa ban san lokaci ya d'an tafi ba, ganin sha biyu ya d'an gota yasa na daura mana abincin rana, abu mara nauyi na girka mana sannan na fito na kimtsa parlor duk da ba wani datti yayi ba na share nayi mopping sannan na kunna coal na zuba turaren wuta na zallan itacen sandal. Nan da nan ko gidan ya d'auki kamshi mai sanyaya zuciya, abincin da na gama kwashe mana cikin warmers na jera mana su kan dinning sannan na shiga wanka ganin ko ina yayi kal dashi, saida na kusan minti talatin ina wankan sannan na fito. Zama nayi agan mirror nabi jikina da lotions masu kyau da kamshi, light make up nayiwa fuskata domin ni ba ma'abociyar son kwalliya dayawa bane.lungu da tsako na jikina nabi da body spray masu sanyin kamshi da sanyaya zuciya. A gaban sip d'ina na tsaya ina karewa kayayyakina da suke a jere kallo ina tunanin wani kaya zan saka, cikin dube duben da nake ido na ya sauka kan wani english gown black color tsayin shi da kadan ya wuce guiwa ta sai adon stones da red flowers da akayiwa gaban rigan daya kara mishi kyau.duk da ban taba saka irin kayan tunda nazo gidan ba amma haka nan zuciya ta ta kwadaitu da saka kayan. Ina sakawa kuwa yayi min cip na cika kayan ya lafe a jikina ya fito mun da shape d'ina sosai kayan ya min wani irin kyau nida kaina na san na canza,tsayawa nayi ina karewa kaina kallo sai naji sha'awan shafa lipstick a labba na Red lipstick na shafa a labban nawa nan da nan ko ya kara haskani ko dan ni ba ma'abociyar lipstick bace oho. Hijabi na zura na kabbara sallahn azahar jin har an fara sallah a wasu masallatan anguuwan. Shi kuwa Zafar yana fita gidan su ya wuce kai tsaye ba tare da ya biya wani wajan ba,yana fitowa a motan shi bayan ya daidaita parking d'in shi ya hango Abba na saukowa daga steps d'in fitowa a parlour su cikin haraman fita hannun shi rike da 'yar brief case. Da sauri Zafar ya karasa gare shi cikin natsuwa da ta fara zame mishi jiki ya rusuna ya gaida Abban shi, shima cikin jin dad'in canjin tilon d'an nashi ya amsa yana tambayan shi lafiya ta. Cikin dan jin kunya ya amsa da " tana nan lafiya lau tana gaishe ku". "Muna amsawa, daga gida kake ko"? "Eh Abba naga kaman fita zakayi?"ya tambayi Abban yana kallon jakan hannun shi. "Tafiyar gaggawa ce ta same ni zuwa kasar Germany, munyi order wasu kaya aka samu akasin da dole sai naje da kaina. Wayanan nan abubuwan kai ya kamata kayi su ko Kuma ka fara taya ni da wasu harkokin ne amma ban san meyasa baka son aiki ba sai zaman banza" Abba ya bashi amsa a d'an kausashe. Murmushi yayi Yana sosa keya tare da fara in ina " ammm ummm Abba na kusa karban business din ka dawo gida ka huta da sweetie ka " duka Abba ya kaiwa keyar shi yana dariya tare da cewa " ja'irin yaro kana son maida ni kakan ka ko ganin babu su kusa da kai ko?" Shima dariyan yayi ya nufi cikin parlour da gudu cikin nishad'i yace "safe trip Abba". Driver da tundazu yake jiran su gama tattauna tsakanin uba da d'an sa ya nufo Abban da saurin shi ya karbi jakan hannun Abban ya wuce gaba Abba na bin shi a baya har zuwa inda ya fito da motan da zai kai shi airport dashi,bayan motan ya bud'e mishi ya shiga ya zauna sannan ya ajiye jakan a gefen Abban sannan ya rufe murfin motan sannan shima cikin sauri ya zagaya ya bud'e mazaunin driver ya tada motan tare da nufo gate da mai gadi ya dade da wangale musu gate suna fita ya kama hanyan airport. Shi kuwa Zafar da sallama a bakin shi ya shiga parlour amma bai samu Mom a nan ba sai masu aiki, direct sama ya hau zuwa dakin ta yayi sallama ya tura kofan ya shiga. Amsawa Mom tayi tare da juyowa daga gyara gaban dressing mirror ta da take yi tana mishi sannu da zuwa. Karasa shigowa yayi ya zauna kusa da kafar ta ya fara zuba mata shawgwab'a kaman yanda ya saba itama tana biye shi, " ga breakfast a dinning room if u re hungry" tace mishi tana shafa mishi gashin kan sa. "Haba Mom I'm a married man fa now how comes ba zanyi breakfast ba har zuwa wannan lokacin" ya bata amsa cikin turo baki kaman karamin yaro, kamin tabashi amsa cikin sauri ya daura hannayen shi duka 2 kan guiwa ta yace" Momy guess What"? Dan dariya tayi tana " just tell me what is going on kaima ka san I'm not good at guessing" shima dariyan yayi yace " yau ni na girka mana breakfast a gida". Cikin mamaki Momy tace " bangane kai ka girka breakfast ba". Gyara zaman shi yayi ya fara cewa "yes Mom yau ni na shiga kitchen tana ma bacci na girka mana breakfast chips nd fried eggs nd tea" ya karasa so excited. Zuciyar Momy na bugawa ta kara tambayan shi" kai da ko ruwan zafi baka iya tafasawa ba ya akayi har ka soya dankali da kwai?" "Google " ya bata amsa kai tsaye kuma cikin kwarin guiwa. Kai ta jinjina ta tafi duniyan tunani dole nema ta tashi tsaye kamin komai ya ida juye mata, ita fa shiyasa tun farko bata maraba da wannan auren domin talaka in Bai iya samun wuri ba balle Kuma ni yar malamai.shikenan iyaye na sun asirce mata yaro da mijinta ma baki daya duka-duka yaushe akayi auren amma gashi duk mun saye zuciyar su,l Abba yayi min kyauntan company nd yanzu Kuma tilon d'an nata yazo yana fad'a mata Wai ya girkawa yar yarinya karama abinci abinda duk tsawon shekaru da sukayi tare ko sha'awan shiga kitchen d'in bai tab'a nuna mata ba?. Tayi nisa da bata jin yanda Zafar ya dage yana mata bayani dalla-dalla ta yanda yabi yayi girkin shi cikin sauki, tab'a ta da yayi ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99