Chapter 46
Chapter 46
ta a wajan ba. A parlour na samu Inna da 'yan uwan ta zaune sun saka kaya a gaba suna maida abinda ya faru duk fuskan su babu dad'i sai ita Inna ce ba zaka gane mataa ba. Zama nayi a kasa kan carpet na fara gaishe su d'aya bayan d'aya duk suka amsa min fuska sake, muna gama gaisawa na wuce kitchen neman ruwan sha anan ma wasu kayan abinci na gani gari guda. Ina cikin shan ruwa ne naji Ya Maaji tana magana cikin b'acin rai wanda ya sani maida hankali kan zancen nasu I really want to know what happened. "Ni dai idan kun san ba zaku canza halin ku ba wallahi karshen ta ba dani za'a yi bikin nan ba, haba wannan wacce irin rayuwa ce ayi ta cutan ka ana kunsa maka bakinciki amma ka kasa ramawa, wa za'a nunawa hakurin muma ai muna da itan matsalsr idan yayi yawa sai a maida ki kwandon shara yanda kowa ya kwaso nashi kan ki zai juye". "Gaskiya ne hakurin Bintu yayi yawa sosai har ta doke Yaya wajan sanyin hali, amma wannan zalincin ne dai ba zamu bari ba dole ne a d'auki mataki saboda gaba" cewar Aunty Batool. "Kina ji fa ita Bintun da bakin ta yanzu take cewa ba yau ta fara yi ba wai ranan da aka fara musu gini an ga wasu layu wanda aka kona ita kuma a take ta fara iface-iface wani babban abin takaici wai ita da Zareefa su sukayi mata addu'a har ta samu lafiya...." "Har ta samu kafan komawa wajan bokan ta zaki ce Batool, in ba dan Allah ya takaita wannan yaro Ibrahim ya ganta yazo ya fad'a ba, da shikenan auren nan ya fasu amma da yake bata da kunya bakin ta bai mutu ba ana magana tana mayarwa" fad'in Ya Maaji. "Ban ki ta naku ba nima ba wai kuma fad'an ne ban iya ba, amma abinda nake son in tuna muku duk wanda ya rike Allah in ba wani ikon sa ba babu abinda zai same ka, ku duba mana sau 2 tayi yunkurin cutar da mu Allah yana mayar mata da abin ta. Ban so kuka kula ta ba, jibi yanda asirin ta ya tonu cikin bainar jama'a wannan ma ya ishe ta ishara, mu kuma bama gajiya da d'aga hannayen mu sama insha Allah, Allah zai kare mu" Inna ta basu amsa cikin sanyin murya babu wacce ta kara cewa kala da alamu maganganun ta ya kashe musu jiki. "Innalillahi wa Inna ilahi raji'un" shi kawai nake ta maimaitawa tare da sulalewa na zauna dabas kan tiles na kitchen d'in, cikin tashin hankali amma ni kam Ibrahim bai kyauta min ba da yazo ya fad'a har aka dakatar da ita, ina ma tayi nasaran sake binnewa da shikenan na fita daga wannan cakwakiyar matsalan. "Gata da hassada da ya gama bin jinin jikin ta dubi yanda ta fito wai tana nuna adawar ta a zahiri kan kayan cin-cin da aka kawo" naji muryan Aunty Fatima tana magana cikin d'acin rai. Sai ana na fahimci ashe kayan da na gani kayan cin-cin ne kenan, shikenan yanzu da gaske ake aure za'a yi min, auren ma da wanda bai san daraja ta ba? Hawaye sai rige-rigen saukowa suke banyi yunkurin hana su ba na bar su suna kwarara domin yana rage min rad'ad'in dake cikin zuciya ta. Muryan Inna naji tana kwala min kira ba shiri na mike daga zaunen da nayi ina share hawaye na na fito duk suka bini da kallon tausayi . "Me kike yi a kitchen d'in tun d'azu" ta jeho min tambaya, "Ruwa na sha " na amsa mata cikin murya kuka, kan kace me kuma hawaye suka fara kwaranya. "Daga tambayan ki shine zaki fara min kuka? Bari in tashi inyi miki abinda zakiyi kukan da hujja" Inna ke fad'an haka tana shirin mikewa, da gudu nayi d'aki na maida kofa na rufe ina jin su Ya Maaji suna mata fad'an kada ta kuskura ta tab'a ni ta bar ni inyi kuka na, ban ji karshen maganan su nayi shirin kwanciya na kwanta abina. Da washe gari ga mamakina ashe duk basu tafi ba anan suka kwana sai ya Maaji da ta kwana gidan Maa, da rana ya fara yi sai ga gidan mu ya fara cika da 'yan uwa ashe wai yau ake cin-cin ni dai ganin sun fara yawa na wuce bangaren su Maman Dije saboda kowacce ta ganni sai ta kira ni da sunan amarya basu san hakan kona min rai yake ba shiyasa na gwammace in tattara in bar musu gidan su kara ta. Kamin in wuce naji sun fara sa-in-sa da 'yan uwan Baba da suka zo cewar su zasuyi, su Aunty Batool kuma suka ce anyi magana da professional bakers su zasuyi kasancewar komai ya zama na zamani ita kuma Gwaggo Hinde ta fara masifa wai ai zagin su akayi a fakaice meye basu iya ba da za'a ce zasu kira wasu suyi dama sun raina su. Wucewa ta nayi abina ban san ya suka kare ba, ina can b'angaren su Dije Ni kad'ai duk abin duniya ya ishe ni zuwan su Maryam da sauran 'yan class d'in mu yasa naji d'an dama-dama. Kusan azahar Dije ma ta iso da yaron ta da yayi wayo gidan ya gama kacamewa saboda surutun ta, hatta Hajara nan tazo tana d'an kqma jiki tana baya-baya saboda abinda ya faru jiya, sai da naja ta da wasa sannan ta saki jiki suka cigaba hayaniyar su Jameela ce dai ban san ina take ba domin yanzu abin nata kullum kara muni yake dan sai tafi sati bata gida kuma koda ta dawo to a buge take dawowa ta zama cikakkiyar 'yar kwaya. Muna nan a b'angaren Maman Dije Har dare a lokacin mafi yawancin 'yan matan sun wuce Dije ma ta tafi sai Maryam da Hajara ne kad'ai suke tare da ni amma itama Maryam d'in shirin tafiyan take wai sai gobe zata taho gaba d'aya ba zata koma ba sai an gama bikin. Har bakin gate muka raka ta nida Hajara inda driver gidan su yake jiran ta, ta shiga yaja suka tafi mu Kuma muka koma cikin gida, Hajara har tana shirin shiga kofan su na tsaida ta nace " Dan Allah Hajara muje mu kwana tare a d'aki na kin ga har yanzu da sauran mutane a b'angaren mu". "Kina ganin babu matsala?" Tambayan da ta jeho min kenan idon ta na cikowa da kwalla. "Wani matsala kuma ko kin manta ke'yar uwa tace" na bata amsa tare da jan hannun ta muka wuce, a parlorn muka tadda su Ya Maaji sun baje suna rarraba snacks da akayi da wayan da aka bayar akayi cikin different containers wai suna rarraba su. Za'a cire na gidan su Ango da wanda za'a rabawa baki sai kuma w so hg6xhanda za'a rage min "wai" atoh dole ince wai dan ni har yanzu na kasa gaskata aure na ake. Hajara duk ta kasa sakin jikin ta akan abinda ya faru jiya ga ya ma'aji sai binta da kallon banza take,ganin haka yasa na jata zuwa d'aki da yake mallaki na a yanzu, tunda muka shiga naga jikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99