Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

ya fad'a kan makeken gadon shi da a kalla zai lashe mutane 7 ba tare da wani takura ba, tunani kawai yake tayi dan komai na duniyan ya fice a ran sa bare zuwa bikin nan, bai dad'e da kwanciya ba d'ayan wayan shi ya fara ringing shima kaman ba zai d'aga amma ya daure ba tare da ya lura da sunan mai kiran ba ya amsa wayan, muryan ango Shamsuddeen yaji yana mishi magana. "Haba Zafar yanzu ka kyauta min kenan, har an fara shagalin biki na baka ciki?" "No Shams it's...., No just ba zan iya zuwa ba saboda wani dalili nd......" "Dan Allah mana kada kace haka please ko minti 2 ne Zafar we really need u here ,pls I'm begging..." "Stop that mana sai ka roke ni ne zan zo bikin ka, aiko saboda Sadiq zan zo ko yanzun ma wani issue ne yake son shige min gaba but gani ni nan zuwa tunda kace ko minti 2 then I will come sai dai ba zan dad'e ba" yana gama fad'in haka ya katse wayan tare da mikewa zuwa bathroom. Can b'angaren su Ango kuma sadiq yana kallon Shamsuddeen daya gama waya yace" ya zai zo d'in?" Gyad'a kai shamsuddeen yayi yana murmushi suka cigaba da shirin su. ******"""""******* Tunda nazo gidan bikin na daure zuciya ta ake ta hidima da ni sai kai komo muke, cikin wannan yanayin ban fasa trying number Yaya na ba sai dai amsar daya ce a kashe har a wayan Maryam na gwada wai ko daga layi na ne a natan ma switch off ake ta maimaita min, bayan munyi sallahn la'asar Maryam ta takura min muka tafi saloon inda akayi mana gyaran gashi lalle sannan aka mana kwalliyan mu. Muna dawowa daga saloon muka saka ankon mu na material Les dark blue da tie milk color sosai kayan suka zauna a jiki na, nayi wani kyau ina haske sai ka zata nice ma Amaryan , Maryam itama tayi kyau sosai abinta, Lokaci yanayi mutane suka fara tafiya ga motoci birjik sai wanda ka zaba zaka shiga wasu kuma a nasu suke tafiya, duk yanda Maryam tayi min nasiha kan in saki raina cikin jama'a in kwantar da hankalin na Yaya na yana lafiya amma na kasa. Ko da muka isa ma banyi wani abu ba na nemi waje na zauna kan wani table da babu kowa saboda ina bukatan kad'aici na fad'a duniyar tunani anya Yaya na lafiyan shi kuwa Allah yasa haka Allah ya kare min shi duk inda yake Ameen. Haka na cigaba da tunanin shi ina yi mishi addu'a Allah ya kare shi yasa yana cikin koshin lafiya tare da kokuwa da hawaye cikin ido na da suke ta bara zanan zasu fito ina maida su ciki. **************** A hankali yake takun sa cikin natsuwa da kasaita ya nufi wata bakar latest Honda wanda zai fita dashi, tsab yake kaman wani basarake yayi matukar kyau cikin half jamfa na wani arnanen voile milk color mai duhu wanda ya kara haska farar fatan sa, bai saka hula ba,gashin kan shi da sajen shi sun sha gyara sun kwanta lub sai sheki suke sai kamshin tsaddaun perfumes d'in shi yake, bai yiwa iyayen nashi sallama ba ya fad'a motan shi yaja ya tafi. Sowan abokan sa sosai ke tashi a lokacin da ya iso na murnan zuwan nashi dan wasu sun fidda ran cewa zai zo, bai biye musu ba hannu kawai ya d'aga musu ya wuce ya samu waje ya zauna yana auna maganan Abban shi wai shi zai had'a shi aure da 'yar kauye shida na birnin ma basa burge shi in aka aura mishi ita ko Ina zai kai ta, oho. Yana cikin zancen zuci yaji an dafa mishi kafad'a a dan razane ya d'ago yaga Sadiq ne tsaye a kan shi yana mishi murmushi yace " lafiya kake kuwa tun d'azu ina tsaye s kan ka ina maka magana baka ji ba har sai da na tab'a ka, kuma baka je kun gaisa da Shams din ba kazo ka zauna kai kad'ai". Zafar kallon shi kawai yayi ya d'auke kai ba tare da yace mishi ci kan ka ba kuma bashi da niyyan tankawan. A zuciye Sadiq ya mike zai bar wajan yana fad'in " d'an rainin hankali kada Allah yasa kayi maganan ai dama ka saba wulakanta mutane...". Caraf yaji Zafar ya riko hannun shi ta baya tare da dawo da shi baya fuska a had'e yace" seat" Ba musu Sadiq ya koma ya zauna yana mai nazarin yanayin Zafar d'in ,duk da bai cika faran-faram da mutane ba amma yaga tarin damuwa da tashin hankali a tare da shi kasancewar shine mafi kusanci dashi bayan iyayen shi. "Wats wrong u look so disturbed?" Sadiq ya tambaya cikin kulawa. Hannun shi duka 2 ya d'aura a goshi yana murzawa kaman ba zai amsa ba can kuma yace" ina cikin damuwa Sadiq kasan yau Abba ya dawo da naje...." "But naga kayi aski ai ko an bashi labarin kaje wani party ne?" Sadiq ya tambaya yana dariya. "Shut up just shut up it'ss not a joke ina gaya maka damuwa na nd u e making fun of me" Zafar ya katse shi a hasale. "I'm sorry sorry pls I don't mean it naga kawai shine matsalan ka da Abba most time" cikin rarrashi da kwanantar da murya Sadiq yake magana yaga da gaske abokin nashi ya fusata. "In wannan ne da sauki kaima kasan ba zai dame ni ba cos I'm used to it " sai da ya sarara yana had'iyen zuciya alaman abinda zai fad'a ya mishi zafi yace "can u imagine abba ya bani 3 days wai in kawo matar da zan aura ko ya had'a ni da 'yar kauye". Dariya Sadiq ya kwashe da shi harda rike ciki yace" kai nagodewa Abba yayi min maganin ka Wallahi ba ka raina 'yan matan Nigeria gaba d'aya ba, shikenan anyi maka mai kankat waya ga Zafar da village girl. Kasan me on ur wedding day ko kuma on ur dinner with d village girl nine zan....." A fusace Zafar ya mike ya koma wani table ya bar Sadiq na kwasan dariyan mugunta, yana zaune a wajan sai saka da warwara yake na yanda zai zillewa auren da Abba keso ya lik'a mishi idon shi ya sauk'a a kaina da nake zaune a gefe ni kad'ai kai na a sunkuye kan waya ta sai neman layin Yaya na nake da bata shiga. Ido ya zuba min ko kiftawa baya yi harda tagumi yayi kana ganin shi kasan yayi zurfi cikin nazari ni kuma ban san wainar da ake toyawa ba. Tab'a shi da akayi ya dawo dashi daga dogon tunani daya tafi ya juya yaga Sadiq ne, gira daya ya d'aga mishi yana murmushi yace " da alama dai Abba ba zai had'a ka da village girl ba". Cikin sauri shima ya amsa yana" yes I won't let dat happen Sadiq, look at dat girl Sadiq" yace tare da kallon inda nake zaune, bin wajan da kallo Sadiq yayi kamin yace" yes na ganta tun a can nake kallon yanda ka tsare 'yar mutane da ido, so finally Zafar got d love of his

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99