Chapter 47
Chapter 47
ta ya kara sanyi sai bin d'akin da ido take alaman d'akin yayi mata kyau dan sai ince zan iya kira shigowan ta d'akin mu tun kamin ayi mana wannan ginin. A bakin gado nace ta zauna ni kuma ina shiga bayi nayi wanka tare da dauro alwala na fito na fara shirin bacci,duk tana zaune a inda na bar ta"tashi kema ki watsa ruwa zaki fi jin dad'in baccin" nace mata ina saka kayan bacci na ba musu ta mike ta shiga kamin ta fito na fitar mata da rigan bacci sannan na haye gado na kwanta,ko da ta fito ta mayar da kayan jikin ta nace ta canza tare da nuna mata kayan da na fitar mata. Ba zan iya cewa nayi bacci ko banyi ba a wannan daren saboda zanyi kaman bacci ya fige ni kuma duk juyi da Hajara tayi ina ji,ni dai gani nan har aka kira sallahn farko na tashi nayi alwala na fara nafila har aka kira na sallahn asuba mukayi tun da sanyin safiya mutane suka fara hidiman gaban su gidan ya d'auki hayaniya na ana shirin biki a gidan da gaske. Breakfast da aka kawo mana ban iya cin komai illah tea dana sha kawai nayi wanka muka koma can b'angaren Maman Dije a lokacin 'yan uwan sun fara cika gidan na kusa da nesa 'Yan mata da muke mates duk wajan mu suka zo suka dasa sabon hira sunayi suna ta tsokananta amma na kasa kula kowa cikin su sai yake da nake binsu dashi. Kusan 12 rana sai ga masu decor sun zo wai daga gidan su Ango aka turo su suyi decoration na wajan da za'ayi wushe-wushe. Duk yanda nayi gudun kitso bai yiwu ba dan Maa ce da kanta ta turo wata mata tace in zauna a min kitso,dole na na zauna aka yaryad'a min kitson KELEYASKU. Ba karamin kara fito dani kitson yayi ba, da yake step 2 akayi min wasu ta baya wasu Kuma ta gaba,na gaban nan ya sauk'o min har kan kirjina na baya kuma har gadon bayana kowa na wajan sai santi kitson suke,bayan sallah la'asar wasu masu make-up kusan su 4 wai suma daga can aka turo su harda photographer da masu video coverage kan kace kabo duk sun fara abinda ya kawo su,kamin ayi sallahn magriba naga 'yan mata sunyi wanka kowacce ta fito cikin ankon ta na atamfa mai tabarma da Maryam ta jagoranta sukayi. Nima ina yin sallah aka tilasta ni nayi wanka ina fitowa masu make-up din suka rufu kaina kowacce tana baza fasaharta,cikin lokaci kankani na fito kaman wata tauraruwa ni kaina kasa daina kallon kaina nayi ta cikin mirror. Maryam ce ta d'auko min akwati da kayan da zan saka suke ciki,ashe kowanne sun manna sunan event din da zan saka a jiki,ban tab'a gani ba duk da boxes d'ina a d'akina suke ko dan basa gaba nane oho. Wani atampa ce da ban san sunan ta ba amma kana gani kasan kud'in ta ba na wasa bane anyi mishi d'inkin GUMJE KANURI daya sha aikin stones kaman ba gobe sai Kuma laffaya wacce zata shiga da kayan shima duk ya Sha adon stones sai Kuma jewelry na d'anyen gold. Ba zan iya misalta muku irin kyan da nayi ba ku dai kawai ku hasaso da kan ku. Fito dani waje akayi nan bakin gate din mu inda yasha decorations dada fararen fitulu kaman rana, su Maryam na min jagora Aunty Fatima na bin mu da turarrn wuta har zuwa inda aka tanada wai wajan zaman mu ni da shi suka zaunar dani wai ana jiran zuwan ango. Ni dariyar suma nake a zuciya ta da suke saka ran wannan d'an rainin hankalin ne zai zo nan lalle suna da babban aiki. Kaman daga sama naji gud'a da kid'an GANGA KURA ana shelan isowan ango da jama'arsa, tun daga nesa na hango shi cikin wasu dankareriyar shadda wanda yayi shige da kayan jikina wato sky blue. Tun kamin ya karaso naji zuciya ta nata bugawa kaman ya fito Dan na San halin shi ban san yau Kuma da me yazo ba. [6/16, 9:16 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *28&29* Duk kamshin turaren wuta da yake wajan dana sauran mutane sai da wannan mayen kamshin nashi ya cika wajan,Kara sadda kaina kasa nayi ban kara gigin d'agawa ba tunda na d'aga na farko zuciya ta kuwa kaman zai faso kirji na ya fito haka nake ji tsabar bugu da yake. Ba komai ya saka ni shiga wannan halin ba sai dan sanin halin sa na wulakanci da disgi, ina gudun kada ya gwada su a nan a gaban kowa ba abinda na tsana a rayuwata kaman mutum ya wulakanta ni ko ya disgani a bayyanar jama'a. Ina cikin zancen zuci naji alamun mutum a kaina d'aga ido da zanyi na ga shine ya rankwafo da kan sa daidai fuska na yana sake min wannan shu'umin murmushi nasa yana kallon na, ni d'in ma shi nake kallo ya bala'in kara had'uwa cikin light blue shadda shi ga hula da ya saka itama light blue ce ba zan iya kwatanta muku yanda yayi kyau ba just imagined him. Na shagala da kallon shi naji yana dariya kasa-kasa yace " please da baki wahalar da kan ki wajan wannan abubuwa da kika shafa ba domin kara miki muni sukayi" ya karasa da kara sautin dariyar shi sannan ya zauna a gefe na inda aka tanada domin zaman shi. Hawaye naji sun cika min ido amma ban bar su sun zubo ba, I knew it na san dole ne ya shimfid'a min wulakanci son ran shi wai kara min muni sukayi ko ina ruwan shi da kwalliya ta. Kuma abin takaicin salon da yayi amfani dashi ya min maganan zaka d'auka hiran soyayya muke sai wani narke ido yake dan haka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99