Chapter 58
Chapter 58
mata kenan daren da za'a Kai ta gidan ta cewa kada ta kuskura ta zauna shiru duk dabarun da zatayi tayi ta rinka turo mana gida mu rinka shan maikon tare, in ma bata turo ba na san tana kan tarawa ne kema na san ki adana balle kuma kin samu makudan kud'i a bikin nan d'an gutsoro min rabo kamin 'yar albarka ta aiko mana" ya karasa yana washe baki. Takaici ne ya kawowa Inna har wuya ya hana ta magana tir da mai irin halin sa irin nasihar da yayiwa 'yarsa da zata shiga gidan miji kenan, wai har sai yaushe zai canza sai yaushe ne zai gane gaskiya? " Abin haushi ma kin ga banida number sirkin nawa ai da kai tsaye zan Kira shi muyi magana ta fah....." Cikin sauri Inna ta katse shi tana " haba Mallam yin hakan ba girman mu bane zai iya raina mu ka bari tunda dai ka fad'awa ita Zareefan zata aiko su ne da zaran ta samu" "Ji wani zance wai ba girman mu bane, yo wani girma talaka yake da ita in banda abinki menene a ciki dan Mai kud'i ya raina talaka." " Babu komai ba komai bane Amma ka bari in an kwana 2 da kaina zan karb'o maka numbern nashi a wajan ta kaga daga nan zaka iya magana dashi kai tsaye a duk lokacin da kake so" tana gama dad'in haka ta mike zuwa cikin bedroom dinta ta d'auko mishi bunch na dubu daya wato dubu dari kenan ta kawo mishi. "Ka rike wannan zuwa wani lokacin ko?" " Ai shiyasa nake son ki ke d'in ta daban ce" yace yana ta washe baki ya mike ya fice daga parlour ba tare da ya jira amsar ta ba. Dabas Inna ta koma ta zauna tana nazari inko hakane tana da aiki babba a gaban ta ba zata tab'a bari ya zubar min da kima a gidan miji ba dole ta mike tsaye akan shi sannan ta dage da addu'a Allah ya shirye shi ya gane gaskiya. *********************** Tundaga wannan rana ban kara ganin kowa a gidan da sunan ziyara ba daga ni sai shi, duk aikin da yace inyi kullum da sassafe nake yi kamin ya fito na tsabtace ko ina na saka turaren wuta abincin sa kuwa bana fashi ina ajiye mishi a kan table in koma d'aki in kulle kaina duk da akwai lokacin da ya same ni yace in daina ajiye mishi wannan jagwalgwalo na dan yafi karfin ci kullum masu aiki yake bawa, ban kula shi ba na cigaba da ajiyewa dan jiki na ya bani shi yake cinyewa ya fake da masu aiki, d'akin shi ne dai ban kara gigin lekawa ba balle ince zan share. Duk wannan kokarin da nake bai hanawa in 'yan rashin mutuncin nashi suka motsa ya sauke su a kaina, ina dai daurewa bana nuna mishi rauni na sai na koma daki nake cin kuka na in more duk rayuwar gidan ya ishe ni. Yau tunda na farka nake ta murna saboda a yau za'ayi yinin bakwai kuma a gidan nan za'a yi shi kaman yanda al'ada yake, babban farinciki na harda Inna za'a zo shima iyayen shi zasu zo a hadu gaba daya asan juna a kara karfafa zumunci. Irin gyaran da nayiwa gidan yau na musamman ne tun 7:30 na shirya cikin wata hadaddiyar shadda ta blue dinkin doguwar riga yasha zubi har kasa, duk da ban iya wani d'aurin kirki ba na kokarta nayi yanda zan iya kuma cikin ikon Allah yayi kyau sosai sai na kara zama Amarya sak, duk d'auki ya hana ni sukuni sai kallon time nake ina jin lokaci baya tafiya, ina zaune ina ta kallon agogo naji an murd'a handle din kofan parlour cike da murna da d'auki na mike na tafi da gudu dan in rungume duk wacce ta fara zuwa, da gudu na kwasa nayi kofan sai dai kamin in karasa naja wani wawan briki na tsaya a tsoroce tare da mayar da kai na kasa. Shiru banji yayi min magana ba Kuma banji alamun ya tafi ba, ina ta ayyanawa a rai na kila ya tafi ne in ba tafiya yayi ba me zai tsayar dashi anan? Hakan da na saka a raina yasa na dago da kaina karaf ido na a cikin nashi yana min wani kallo da ni dai ban san fassaran shi ba, mayar da kai nayi na shiga gulman shi a zuciya ta mutum sai shegen fadin ran tsiya da iyayi.... "Meye na gaya miki last time akan gidan nan?" Muryan shi ya katse min gulman shi da nake. "Kace in rika share gidan nan kullum...." "And then?" Ya katse ni tun kamin in karasa. "Ina yi kuma harda girki" daki na fa?" Ya kara katse ni. Harga Allah bai zata da gangan na zubar da ruwa ya fad'i ba a wancan ranan Kuma yaji dad'in gyaran da nayi mishi shiyasa ya biyo ni, ni kuma a tunani na ya sani shiyasa naki shiga d'akin kada ya kama ni na San halin shi na cin zali. "Kayi hakuri zan rinka gyarawa " na bashi amsa cikin sanyin murya. "Better " yace tare da juyawa ya fita nabi shi da ido har ya b'ace min dan yayi min masifan kyau cikin riga armless da wando 3 quater duka farare ne tass anr rubuta Gucci da manyan harufa da bakin fenti a gaban rigan mutum yana ganin well builded body shi a zahiri ga gashi kwance luf a fatan jikin shi kaman wani balarabe. Kofan na rufe na dawo na zauna jiki na duk a mace me yasa kwanan man nake jin wannan yanayin in muna zaune waje daya kuma duk abinda yake yanzu birge ni yake ba kaman da danake jin haushin shi ba. 9:00 am dot Yasmeen da kannen ta 2 suka zo cikin farinciki na taro su bamu zauna a babban parlour ba naja zuwa nawa muka zauna naja karamin kanin ta da ba zai wuce 7 years ba ina tambayan shi ya sunan shi? Dan Allah ya daura min son k'ananan yara ko dan babu a d'akin mu ne oho. "Muhsin " ya amsa min da karamin muryan shi mai dad'i, murmushi nayi nace " sunan ka mai dad'i". "Aunty Amarya kin gan mu da sassafe ko, wlh muhsin ne ya takura mana tunda ya farka daga bacci yana ta kuka shi lalle sai an kawo shi nan shine fa da ya ishi Momy da fitina tace muzo kamin ta karaso" Yasmeen ta katse ni da murmushi a fuskar ta.. "Ni ai Muhsin ya burge ni ina zaune ni kad'ai kaman mayya gashi na samu abokanen hira, kema kince zaki dawo ban Kara ganin kafar ki ba tun ranan da kika fice daga gidan nan" na bata amsa ina dan dariya. "Cab ai Momy ce ta hani ni zuwa wai zan zo in takura ku" ta karasa itama tana dariyan. Kawar da wannan maganan nayi na kawo wata hirar daban nake tambayar ta ya matakin karatun ta yake, ta amsa min da zata rubuta jamb tayi joining next year, naga ashe matakin mu daya da ita a karatu. ***************** Tun goma da rabi na safe gidan mu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99