Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

daga cikin dalilan da Gwaggo Aisha take min zazzafan tsana. Inna kuwa tana fita a d'aki bata ko kalli inda Baba da Gwaggo Aisha suke ba ta fice zuwa gidan su, suma dai basu lura da ita ba duk hankalin su yana kan fad'an da suke. A tsakar gida ta samu Maa da kanwar ta wacce suke kira da Ya ma'aji suna hiran su na 'yan uwan taka gwanin sha'awa, da sallama ta shiga sai dai bata tsaya taji amsawar sun ba ta shige d'akin Maa. Da ido duk suka bita har ta shige cikin d'aki ba tare da ta tsaya wajan su ba kaman yanda ta saba ba ko kuma ince yanda ya kamata ba, Ya ma'aji ta dubi yayar ta tace" Yaya da alamau yarinyan nan tana cikin damuwa,dubi yanda ta shigo gidan nan hankali tashe, ni wallahi wannan kaddararren auren nata da kina jin shawara ta da tuni ta rabu da shi haba yarinya tana 'yar karamar ta amma kullum cikin tashi hankali take dubi yanda duk ta motsare,ga fitinan miji gana kishiyoyi da wanne zata ji" ta karasa da matukar fushi a fuskarta domin ita halin ta daban dasu Maa fad'a ne da ita sosai ga rashin hakuri. Murmushi mai sanyi Maa tayi mata tana girgiza kai tace "kai ma'aji akwai ki da daukan abu da zafi baki san halin yaran yanzu ba abu bai kai ya kawo ba zasu d'auke shi da zafi........". "A'a Yaya kada ki raina hankalin ta na tabbata ko ke da kika fimu sanyin hali aka ki gidan nan nata zasu kure ki,bari inje inji meya faru" tace tana mikewa tare da nufan d'akin da Inna take ciki. A kan carpet da yake shimfid'e a tsakar dakin ta samu Inna ta had'a kai da giwa tana kuka kasa kasa. Dafa ta Ya ma'aji tayi yasa ta d'ago da kai suka had'a ido tayi mata murmushi ita kuma kukan ta kara fashewa da shi cikin muryan kuka ta fara magana"Ya ma'aji ku ceci Zareefa dan Allah ku cece ta ni na yarda suyi min duk abinda suke so amma dan Allah su kyale ta tayi rayuwa mai yanci da farin ciki, yarinya ce k'arama bata san rayuwa ba dan Allah kada su jefa rayuwar ta cikin.........." "Ya isa haka ya isa, ki natsu ba abinda zai faru da Zareefa muna tare da ke kuma Allah yana tare da mu dan haka ki kwantar da hankalin ki, ki min bayanin me yake faruwa?. Ya ma'aji ta katse Inna da take magana cikin fitan hankali. "Wai aure zaiyi mata kuma ni baiyi shawara dani ba ban san waye zai bawa ba,kawai yau da safe ya shigo da masu gini wai zai canza ginin gidan zuwa na zamani kuma yana so ayi da wuri kuma a bangare na aka fara saboda auren wai ba zai wuce wata d'aya ba. ni abinda yake bani tsoro na san halin shi in game da kud'i ne komai zai iya yi......." "Ba 'yar sa bace ko saida ta zaiyi ina ruwanki " suka ji muryan Maa a bakin k'ofa wacce da alamu ta dad'e tsaye a wajan,duk kallon ta suka tsaya yi har ta shigo ta samu waje ta zauna tana fuskantar Inna. "Kin bani mamaki Bintu da har zaki tada hanklin ki kiyi abinda baki tab'a yi ba wato kawo karan miji, yanzu da kika kwashi kafa kika zo min gida menene a zuciyar ki ko so kike ni in kira shi ince bashi da daman zabawa 'yarsa mijin aurex ko kin manta addinin musulunci ne ya koyar da hakan...." "Maa na sani wallahi na sani amma kema kin san halin shi zai iya yin komai akan kud'i, sannan ya kamata ya shawarce ni ya fad'a min abinda yake faruwa ba wai inji maganan ta sama ba" Inna ke fad'an haka cikin wani irin murya mai nuna tsananin halin da take ciki. "Menene halin sa Bint? koma wani irin hali ne dashi ba zai tab'a cutar da Yar cikin sa kuma maganan shawara da kike so yayi dake, wani shawarwan zaiyi bayan ke kan ki a karkashin sa kike. Tashi ki koma d'akin ki ki cigaba da ibadan ki cikin kwanciyar hankali kaman yanda kika saba sannan kija yarinyan nan a jikin ki,ki kwantar mata da hankali kiyi mata tuni da duk wanda yayiwa iyayen sa biyayya to tabbas zai ga alkhairi a cikin rayuwar sa, kada ki kuma yin abinda zai tashi hankalin ta, duk halin da zata shiga in fana ganin ki a kusa da ita zata ji sanyi, Sannan ke kuma ki bita da addu'oin zaman lafiya da farinciki Mai daurewa ya tabbata a gidan ta, insha Allah sai ts samu fiye da yanda muke hasashe". Inna share hawayen ta take wasu na zubowa bata son musu da mahaifiyar ta amma ta san halin Baban mu sai shi, mikewa tayi da niyyan komawa Ya Maaji da bata da hakuri ga zafin zuciya ta bud'i baki da nufin zatace wani abu Maa tayi saurin dakatar da ita ta hanyan daga mata hannnu, kawar da kai gefe tayi tana cize lebe na haushin an hana ta magana. "Ya Maaji na tafi ki gaida su Bayuram,Maa na gode Allah ya saka da alkhairi ya baki nisan kwana insha Allah zanyi kaman yanda kika ce" Inna ke fad'an haka tana gyara hijhabi dake jikinta. Ya Maaji da duk takaici ya hana ta saka baki cikin maganan nasu da taga Inna ta juya zata tafi tayi yunkurin magana nan ma Maa bata bata dama ba ta kara daga mata hannu alaman tayi shiru. Shirun tayi tana kallon Inna har ta fice sannan ta dawo da hankalin ta kan 'yar uwar ta tace " haba yaya yanzu sanyin halin naki ya kai kija baki kiyi shiru a cuci 'yar jikar ki guda d'aya tilo, ni dai wallahi tafiya ta zanyi ba zan zauna bakinciki ya kashe ni ba" Hijabinta ta shura tayi hanyan waje, Maa tana ta kwala mata kira bata yarda ta juyo ba balle ta amsa, Dan murmushi Maa tayi tana girgiza kai tare da mata addu'a Allah ya rage mata wannan zafin zuciyan. Lokacin da ta dawo bacci ya d'an sace ni ban san ma ta dawo ba sai cikin bacci naji kaman kuka harda shashheka, a hankali na bud'e ido na dan tabbatarwa, bayan ta na gani tana ta kuka tsakanin da Allah wanda tun tasowa ta banga ko kwatanci sa tayi ba. Tausayi da kaunar tane naji yana bin ko ina a cikin jinin jikina saboda na san duk a kaina ta tada hanklin ta kan auren da taji Baba yace zai min, banida zab'i dole in kwantar da hankali in nuna mata babu komai ta wajena ko zata samu natsuwa, wannan dalilin yasa naki fad'a mata tun farko kenan amma ba yanda zanyi dole ne ta sani. D'an motsi nayi yanda zata ji, aiko nan da nan ta shiga share hawayen sannan ta d'an juyo sai taga ido na a rufe, bakin gado tazo ta zauna tana shafa min gashin kaina, jin ta daina kuka yasa na bud'e ido na kaman yanzu ne na tashi daga baccin. Murmushi ta sakar min tace " bacci kika koma kenan?" Gyad'a kai na nayi nima ina maida mata

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99