Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,312 words 0 views Progress saved
Download Book

take ba kullum tana cikin d'akin ta dan matan duk sun had'e mata kai har yaran su duk raini suke mata sai wajan matan kanin Baban mu Maman Dije take samun sauki dan babu ruwanta da hargitsin gidan mu sai kishiyarta itama tana shiga cikin sauran matan Baban mu tana taya su wulakanta Inna ta. Haka na fito daga cikin makarantan ina kukana na karin takaicin ma 'yar silifas da nake lallab'awa kuma nake shan bulalan rashin sandal akai ina zuwa bakin gate ya tsinke, ban tsaya neman leda dan gyarawa ba na rike a hannu na nufi titi ido rufe na manta da akwai motoci kan titin burina kawai in ganni a gida. Karan takawan brick ne ya dawo dani hayyaci na, ganin mota ya nufo ni gadan-gadan yasa na rasa yanda zanyi saboda firgita nan na durkushe ina jiran ta Allah ta kasance min. Motan daya ja brick Allah ya taimake ni bai kad'e ni ba amma motan bayan shi sai da ya fasa mishi danger, shima na bayan shi ya buga mishi a takaice dai motoci kusan 5 sukayi hatsari duk a dalilina, kuma duk abinda ake ina nan durkushen ban mike ba. Wani wanda motan shi yafi na sauran bugawa ya fito a zuciye ya janyo ni yana bala'i yana zagina ya d'aga hannu zai yarfa min mari, ihu na yi na rufe fuska ta da d'ayan hannuna ina jiran saukan marin amma na ji shiru ina bud'e idona naga ashe mutane ne suka rike shi suna bashi hakuri, ina jin ya sake min hannu na kama hanyan gida da gudu dama tsakanin makarantan mu da gidan babu wani nisa sosai. Ban iya tsayawa a ko ina ba saboda zafin rana da yake kona min kafa ina shigowa Hajara na fita da katon tire da aka jera mata robobi da aka zuba garau-garau hamsin hamsin a ciki, ni dai ban san ya akayi ba kawai sai gani nayi munyi karo kayan kan ta sun zube kamin kice kwabo almajirai sun fara wawaso nima ganin haka na wawasushi roba 2 na kama ci dama na kwaso yunwa ta na fitan hankali. Ihu Hajara ta fasa tana "Wayyoo Gwaggo zo ki gani zo kiga abinda Zareefa tayi min" jin an ambaci suna na yasa matan gidan da yaran su lekowa dukan su, ni kuwa ko a jikina ina gefe sai zabga loma nake yau na samu shinkafa da wake daya ji mai da yaji har roba 2. Salati manyan suka fara suna bina da kallo yanda baki na yayi nasha-nasha da mai,Gwaggo Aisha da fitowar ta kenan tace" kan uba ke Hajara meke faruwa ya akayi kika min b'arin abinci haka?" "Wallahi Gwaggo kin gan ta nan Zareefa ce ina fita ta shigo a guje ta ture ni har nayi barin, kuma tun kamin almajirai su zo ita ta fara wawason min abinci" Hajara ta karasa tana harara ta yanda nake ta sud'e roba dan ban san ma sunayi ba sam. Wani maka da Gwaggo ta kai min a gadon baya ban san lokacin da na saki roban na gatsare tare da fasa ihun azaba ba, wuyan matattacen uniform d'ina ta kama ta jani zuwa ciki tana" lalle na yarda wannan 'ya ta gado mugunta, hasada da tsiya yo banda tsiya yanda kuke ke da uwar ki baku da allura a cikin d'akin shine ta koya miki yanda zaki na yi min barna kina jawo min asara?? Ke Bintu koki fito wallahi kabo na ba zaiyi ciwon kai ba duk inda zaki shiga ki fita sai kin bani kudina yanzu kuma wallahi ba sai anjima ba, ki fito na ce ". Kallon yanda wuyan uniform d'ina yake kara yagewa yasa nace" Gwaggo ki sake min uniform d'ina kinga kina kara......" Ban samu karasawa ba sakamakon buge min baki da tayi tana huci tace" inifon din banza inifon din wofi ke iskanci uwar taki take koya miki ko boko shegiya yarinya duk wani gantali kin iya wai an likawa boko da baida baki" "Ni ai abin nasu dariya yake sakani haka masu bokon suke ko akan su aka fara oho, dubi kiga ko takarda d'aya bata dashi balle fensir,ko da uwar me take rubutun?" Cewar Inna Asabe. Inna ta duk tana jinsu amma ko lekowa bata yi ba balle ta tanka musu, hayaniya sosai ya kaure a gidan mu harda mokota masu zugi sai yi suke harda masu cewa a gaban su ma abin ya faru, dole yasa Inna ta fitowa daga d'aki jin abin yaki ci yaki cinyewa. "Yauwa daddawa uwar zaman d'aki dole ai yau ki fito azo a biyani kud'ina naira dubu daya da dari biyu ciff wallahi ko biyar d'ina ba zaiyi ciwo ba". Dariya suka fara suna " keko Aisha ina wannan taga har dubu da dari biyu sai dai in 'yar zata sai da ta biya ki" ko kuma kije wajan tsohon soja" wani tsohon soja sai dai ayi sata" ire-iren kalamai da suke jifan Inna ta dashi kenan. Kaman yanda ta saba bata kula kowa ba ta koma cikin d'akin ta sai gata ta fito da dubu d'aya da dari biyu ciff da Gwaggo Aisha ta ambata ta mika mata babu kunya ta sake min riga ta karb'e kudin tana lissafi tana mamakin ina Inna ta ta samu wannan kud'i ita da burin ta yau sai ta wulakan tamu yanda taga dama amma cikin ikon Allah ta biya. Duk watsewa suka yi cike da mamaki wasu ko cewa suke dama bar raina mutum baka san sirrin sa ba. Ana cika min rigata na shigo d'aki ina kallon wuyan rigata na ce, "Inna dubi fa yanda ta maida min wuyan rigata gobe ya zanyi in tafi makaranta?" Inna da ta had'a rai sosai ta ce, "ba wuyan riga ya kamata kiyiwa kuka ba, gobe kika ce za'a rufe karb'an kud'in common entrance ko?" Gyad'a mata kai nayi ina cire kayana. "Toh kud'in da nayi wata 3 da wani abu ina tara miki na common entrance d'in su na bada a maimakon abincin mutane da kika zubda, gobe ma in kin taso daga makaranta kada ki rinka kula da gaban ki". Yawan comments yawan typing. [8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` *_And now_* *_💃🏻UWANI💃🏻 *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊 *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Addu'a Ga Wanda ka zage shi:* Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; اَللَّهُمَّ فَأَيـما مُؤْمِنٍ سَبَبْتُهُ فَاجْعَلْ ذَلِكَ لَهُ قُرْبَةً إِلَيْكَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ. Allahumma fa'ayyuma mu'minin sababtuhu, faj'al zalika lahu kurbatan ilayka yawmal qiyamati. Ya Allah! Duk wnai mumini da na zage shi, to ka sanya wannan ya zamanto sababi gare shi na samun kusanci zuwa gare Ka ranar kiyama. *~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* _Kasance mutum na farko da zai fara karanta

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99