Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,293 words 0 views Progress saved
Download Book

sallama ta shiga motan su da driver yake jiran ta nima na shiga a daidaita da yake zuwa d'auko kuma ya kawo ni makaranta kullum kaman yanda Yaya na ya tsara. Tun daga wannan rana bamu kara had'uwa da Maryam ba suna can hidima tayi musu yawa amma kowacce rana sai munyi waya kuma tana neman inje in taya ta wasu abubuwa sai dai kwata-kwata bana cikin natsuwa kasancewar Yaya na yau kusan kwanan shi 5 kenan da yin tafiya amma shiru bai dawo ba kuma wayar shi bata shiga balle inji lafiyar shi. Wannan dalilin yasa bani da kwanciyar hankali sam shiyasa na kasa zuwa gidan su Maryam d'in, haka kawai kuma nake jin yawan fad'uwar gaba har na kasa daurewa na fad'awa Inna tace min inyi ta addu'a ba abinda zai faru. A haka na daure nake dan al'amura na har ta kai gobe ne dinner gidan su Maryam kuma tun safe ta matsa min da waya kan yau bata son wani excuse lalle inzo da safe dan akwai abubuwan da zamuyi, ba dan ina so ba na amsa mata da toh kawai na katse waya ta dan rashin jin labarin Yaya na ya sanya bana jin dad'in duniya sam. Da washe gari ma Inna ce ta matsa min akan in tafi tun safen tunda haka ta bukata ko akwai ayyuka da zan kama musu itama tana zuwa anjima kad'an,dole na na shirya nayi mata sallama na fita. *********************** Tun jiya yaje tsadadden saloon da yake zuwa aka aske mishi gashin da ya tara kuma akayiwa askin zamani, sanin cewa in Abba shi ya gani ba zaiyi mishi da sauki ba , ko da yaji Abban nashi ya dawo duk daukin son ganin shi da yake sai da ya d'auko natsuwa da jarumta sannan ya nufi part din iyayen nasa cikin fargaban kada yayi mishi maganan aure. A parlour ya tadda su zaune suna hira Abba na shan fruit salad da Momy ta had'a mishi da kan ta. Kusa da kafafun shi ya karasa ya zauna tare da d'aura kan sa akan cinyan Abba ya kwantar, cikin tsantsan kaunar tilon d'an nashi ya hannu yana shafa kan a hankali fuskar shi d'auke da murmushi yana matukar son d'an nashi sai dai wasu halayan da ya kwaso marasa kyau ya d'aurawa kan shi yasa basa shiri, ganin sa cikin shigar kamala kad'ai yau yasa shi farinciki. Babban burin shi yanzu shine yaga d'an nashi yayi aure ko zai natsu ya daina abinda baya so sannan shima girma ya fara zuwa mishi yana bukatan hutu yana son d'aura shi kan d'inbin dukiyar shi da shi kan shi bai san iyakar su ba. Cikin girmamawa yayiwa Abban nashi barka da zuwa shima ya amsa cikin kulawa, zama ya gyara ya d'auki spoon d'in da Abba shi ke shan fruit shima ya fara sha yana kai na farko baki ya lumshe ido yace" Mom ji yanda wannan fruits din yayi dad'i amma ni in nace ki min ba yayin dad'i haka". Mom tana dariya tace" kayi aure matar ka zata yi maka wanda yafi wannan dad'i". Ras yaji gaban shi ya fad'i meya kai shi fad'in haka gashi har an tabo zancen da baya so ayi ta agaban Abba, shima dariyan yayi da son kawar da zancen yace" yauwa Mom abokinaboki na shamsuddeen nan da kike ta yabon shi kullum gobe ne fa auren shi anjima kad'an ma zan je dinnern kuma dasu Sadiq....." "Aikin kenan zuwa dinnern wasu amma kai baka tab'a tunanin kaima kayi settling down, ko har yanzu kana tsamanin yaro kake komawa?" Abba ya katse musu zancen cikin daure fuska da zaka san ran shi a bace yake. "Anyway duk ma laifi na ne da na zuba maka ido ina kallon ka da sunan ina jiran ka kawo min matar da kake so da kan ka,but tunda baka fahimta ba let me make my self clear, kwana 3..... Wallahi kwana 3 kacal na baka in baka fito da wacce kake so ba kauye zan je in samo maka mata cikin 'ya'yan dangi, in kuma ka d'auka wasa nake maka ka jira kwana 3 ka gani" Abba yana gama maganan shi ya mike fuuu ya bar musu parlon. Cikin wata irin murya mai cike da tashin hankali ya rarrafo gaban Mom ya fara magana" Mom pls ki bashi hakuri wallahi ni banida wacce nake so a yanzu dan Allah ya kara min lokaci wallahi zan kawo ta har nan ku gan ta". "Wannan karon nima babu hannu na a ciki saboda ka kai Abban ka makura sannan ni kaina ina son ganin auren ka ko dan jikoki su cika mana gida, so count me out of this" itama tana gamawa tabi bayan mijin ta suka bar Zafar cikin fargaba da tashin hankali. [1/26, 7:06 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *16* Zafar ya kai kusan 30 mins a zaune wajan sai share gumi yake duk da sanyin A.c dake parlor amma bai hana shi jikewa da gumi ba, ta ina ma shi zai nemo mata cikin kwana 3 kacal, shi fa ya raina 'yan mata 9ija kuma koda yayi karatu abroad bai samu wacce ta kwanta mishi a rai har yace zai iya auren ta ba. Ringing d'in waya ne ya dawo da shi hayyacin sa amma ya kasa d'aga hannu ya d'auki wayan balle ya amsa,sai da akayi mishi 2 missed calls a na 3 ne ya d'auki wayan ya kai kunne yayi shiru. "Zafar kana ina ne baka karaso ba, tun d'azu Shamsuddeen ya dame ni da na kira ka wai har an kusan tafiya hall" muryan Sadiq yaji cikin wayan yana magana, bai iya bashi amsa ba ya cire wayan daga kunnen shi ya mike a hankali ya fara tafiya cikin kasaita daya zame mishi jiki. Part d'in shi ya shiga bai tsaya a parlour ba ya wuce bedroom

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99