Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,295 words 0 views Progress saved
Download Book

zuba su anan nace" ya kara daka musu tsawa daya kara hargitsa su suka kama karkarwa amma babu wanda yayi yunkurin cirewa. Tau kake ji suka d'auke wani saurayi da bindiga babu wani nisa tsakanin shi da Gwaggo Aisha. Kaman kiftawan ido suka fara rige rigen cire kayan jikin su, aka kwashe duka aka zuba su cikin wani buhu sannan suka umarci driver da su shiga mota su koma cikin Maiduguri a haka. [1/26, 7:06 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹 🦚 *BA SONTA NAkE BA* 🦚 🦚🌹 🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹 _A story about love and sacrifice._ _Written by_ *UMMEE YUSUF* _(Maman Yusuf)_ *15* _*From The Fantastic Writer of*_ ```FARHAT``` ```KAMACE``` ```UKUBAR KISHIYATA``` ```UMMU~SALMA``` ```UWANI``` *_And now_* *_BA SONTA NAKE BA_* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *15* Shiru cikin motan kaman ba wani mai rai a ciki sai muryan mata da suke kuka kasa-kasa saboda kukanta su da akai babu mai kallon d'an uwan sa duk sun takure waje d'aya suna tunanin tayaya zasu shiga gari a haka? Ita kuma Gwaggo Aisha tana ganin kaman kaifin asirin Inna shi ya hana ta zuwa ga wannan mashahurin bokan har 'yan ta'addan suka samu daman yi mata aika-aika. A wani kauye driver ya tsaya Allah ya sa akwai wani tsumamun riga da ya maida duster yana goge-goge dashi a cikin motan, shi ya saka ya fita ya karasa cikin kauyen yayi musu bayanin halin da suke ciki, nan da nan mai garin yasa aka hado musu suturu na maza da mata ya kai musu dan ba karamin tausaya musu sukayi ba. Koda ya kai musu kayan kowa ya d'auka ya suturta jikin sa sannan suka mike hanya zuwa cikin gari. Azahar dai-dai suka shigo driver ya zubar da kowa nan cikin tasha ya kama gaban shi, Gwaggo Aisha da kyar taja kafafun ta da har yanzu rawa suke saboda firgita ta fito ta samu adaidaita sahu zuwa gida duk da ta san bata da ko sisi a hannu. A hanya ji take kaman kada taje gida ta wuce ko gidan 'yan uwan ta ko zata samu canza suturan dake jikin ta wai kada su Inna su raina ta, canza akalan tafiyan tayi daga gidan mu zuwa gidan kanwar ta. Da yake duk tafiyar su d'aya da kanwar nata da taji abinda ya faru da Gwaggo Aisha maimakon ta nutsar da ita ko ta d'aura ta kan hanya saima kara zuga ta da ta rinka yi harda cewa ta samu kudi ta kara komawa, kuma kar ta kuskura ta nuna gazawar ta har sai ta kawo karshen Inna ta. Da wayan nan kalaman nata ta kara karfafa mata guiwa, sai bayan sallahn magriba ta dawo gida hankalin ta kwance kaman babu abinda ya faru, anyi sa'a Jameela tana gida cikin murna ta tarbe ta kannuwan ta duk sun zaku da son jin daddadan labarin yanda sukayi da boka, Hajara tana yi mata sannu da zuwa ta fice ta bar musu d'akin tare da nema musu shiriya daga rabbi. "Umma wannan wani irin magana ne haka kike cewa ko kuma dai sabon rainin hankali da kika zo dashi kenan?" Muryan Jameela ke tashi daga cikin dakin nasu cikin tsawa kaman ba da mahaifiyar ta take magana ba. "Na lura tunda nace ki daina sana'a zanyi miki komai kika koyi wasa da kud'i saboda baki sha wahalan neman su ba, toh wallahi nima daga rana rin ta yau na daina baki kud'i na sai dai ki koma yin sanar ki dan ba zan iya ba" ta karashe tana harare-harare ita kad'ai. Gwaggo Aisha kin kula ta tayi ta shige can d'aki ta rabu da ita domin ta lura asirin ta take son tonawa gaban kishiyoyi wanda ba zata tab'a bata daman hakan ba duk da kwanan nan alamun karara sun fara bayyana cewa Jameela ta fara tab'a shaye-shaye. Hajara kam tana gefe tana sauraron su bata da daman saka. baki Gwaggo Aisha ta hau kan ta da bala'i, Jameela ta gama suratan ta tayi ficewar ta. Bata bawa kowa labarin abinda ya same su a hanya ba ta had'iye kayan ta amma ta kudiri aniyar neman kud'i tukuru domin ta samu tara kud'i ta koma wajan bokan ta. Ko sati bai kai ba muka ga ta fara sana'ar ta na abinci kaman yanda ta saba sai dai banbancin yanzu almajiri keyi mata tallah saboda bata da yara kanana yanzu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wata rana dad'i wata rana kuma akasin ta, sai dai mu kam babu abinda ya canza a soyayyar mu sai ma karuwa da yake a ko wani dakika cikin zukatan mu. Cikin ikon Allah yau muka gama waec d'in mu muka fito cikin farinciki muna taya juna murna tare da fatan Allah yasa mu fito da sakamako mai kyau, IV muka shiga rabawa kawayen mu na dinnern auren yayan Maryam Shamsuddeen wanda za'ayi sati mai zuwa. "Yaushe zaki zo gidan mu muje saloon tunda shine kad'ai ya rage mana cikin shirye-shiryen bikin?" Maryam ke tambaya ta bayan mun fito daga makaranta. "Toh uwar zumud'i in kin manta let me remind u auren fa saura sati". Nace ina aika mata da hararan wasa. Dariya tayi sosai sannan ta ce" nafi ki sanin cewa saura sati kuma ai ba cewa nayi muje yau ba ko?" "A toh ai na zata tsabar zumud'i yasa kin d'auka yau ne auren,ni ya kamata inyi wannan rawan kafar kin ga munyi waec d'in mu Allah yasa kada Baba yace sai anyi neco za'ayi bikin mu da Yaya na ayi mana yanzu wallahi in lokacin yin neco yayi sai ya rako ni muzo tare ina yi mishi 'yar...." Duka da Maryam ta d'ad'a min a baya shi ya hana ni karasa magana ta, ina sosa wajan nace" ke me yasa kin cika mugun ta ne?" "Ke ko kunya ba kya ji, bari in yi hanzarin zuwa gidan ku in fad'awa Inna tayi saurin aurar dake kada ....." "Da kin taimaka min kuwa dan Allah zo muje ki gaya mata yanzu " nace in riko hannun ta. Warce hannun ta tayi tana" Allah ya shirye ki Zareefa". Mukayi dariya dukan mu. A nan mukayi

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99