Chapter 36
Chapter 36
babu abinda zai kawo shi gidan mu. Cikin fargaba na d'aga ido na dan tabbatarwa kai na cewa bashi bane, amma me ina dagowa idona sai cikin nashi da yake aiko min da munanan sakonni. D'auke nawa idon nayi cikin second d'aya ganin wanda ban tab'a zato balle tsamani ba a kofar gidan mu, na had'iye wani bushashan yawu da ya tsaya min a makoshi sai yanzu na lura da yanayin shigar sa tsayin sa fatan jikin sa komai daban dana Yaya na. Kara d'agowa nayi naga yana min wani kallo kaman yaga kashi , cike da jin haushin kaina kama hanya zan shiga gida garin murnanan zuwan Yaya bada kaina. Gaba na yasha yana wani kumbura fuska kaman ni na jawo shi gidan namu yace; "Nasan yanzu gurgun tunanin ki ya baki cewa wajan ki nazo ko? well I don't have much time but to say I have a contract with you" "Contract!?" Naji baki na ya furta cikin mamaki ba tare da na shirya ba, shi kuwa murmushin gefen baki yayi yana like father like daughter" shi a zaton sa duk son abin duniya yasa na amsa mishi lokaci d'aya bai san cewa mamaki ne ya kama ni ba. "Yeah contract marriage kuma if possible ba zai wuce 1 to 2 months ba zakiyi tafiyan ki nd zan iya baki daga 100 millions zuwa sama kuma kada ki d'auka wai zaman ma'auran gaske zamuyi, no zanyi haka ne kawai dan in fita daga mess d'in da Abba na yake son jefa ni ciki" a garance ya cigaba da tambaya ta nawa zai bani. Juyowa nayi ina fuskar shi da kyau duk da ina jin yanda zuciya ta take bugawa kaman ya fito saboda tsaban kwarjini da yayi min dan sosai yake cika min ido amma dole ne in nuna mishi mu mata daraja ne damu kud'i bai isa ya saye mu ba. "Hmmm ikon Allah , naji ni mai gurguwar tunani ce, kai kuma wannan tunanin naka me zan kira ta dashi miskini ko nakashasshe? "Anyway bari in fada maka ko duniya da abinda yake ciki zaka mallaka min toh ni Zareefa na fi karfin wannan kazami ko haramtaccen rayuwa da kazo min dashi sai dai ka kara gaba kila ka samu wata gantalalliya da zata amince maka amma ba ni ba" Ina gama maganata na rab'a ta gefen shi zan wuce zuwa cikin gida naji an finciko ni ta baya tare da d'aga hannu zai yarfa min mari kuma ya fasa ya dungule hannun ya kaiwa iska naushi yace; Damn u ! Who do u think u re ? Da har zaki bud'i baki ki fad'a min magana son ranki, I don't blame you baki san wanene ni ba da ko wuka aka d'aura miki a wuya u will not have d guts to do it. Kada gani na a kofar gidan ku yasa ki d'auki kan ki kaman wata mace u re nothing yes I mean nothing, ba duniya da abinda suke ciki zan bayar ba amma Baban ki yace min ko gobe inzo zai d'aura min aure dake nazo nan na fad'a miki ne cus na san ba lalle bane su fad'a miki irin auren da zakiyi but for now at least kin san irin auren da zakiyi, as for me I don't have time for cheap girls like u". Yana gama maganan shi fad'a motan shi yaja shi a d'ari ya fita daga layin mu tare da bad'e ni da kurar motan ya tafi abin shi. Ni kuwa ko kafata na kasa d'agawa a wajan ba wai maganganun shi ne suka b'ata min rai ba illa sunan Baban mu daya ambata a cikin maganan shi ya jefa ni cikin tashin hankali mara misaltuwa. Na san Baban mu tun ina k'arama akan kud'in Baban mu ba abinda ba zai aikata ba koda akan dubu d'ari ne zai amince balle yaji million d'ari, " Na shiga uku" nace hawaye na ambaliya a fuskata. Nafi minti 5 tsaye a wajan ina hawaye sannan na goge fuska ta da hijabi na,naja kafafu na da sukayi min nauyi zuwa cikin gida. Allah ya so ni babu kowa a tsakar gidan duk suna d'akunan su sai hayaniyar su daya cika ko Ina kai tsaye na wuce d'akin mu, da sallama na shiga d'akin ban tadda Inna ba ina zaton ta zaga bayi ne. Ban tsaya bata lokaci ba na haye gado na kwanta ko hijabin dake jikina ban cire ba gudun kada Inna tazo ta same ni cikin sabon tashin hankali dan ban san wani bayani zanyi mata ba. Tunani na zurfafa a ciki na yanda rayuwa take neman juya min baya ina 'yar k'arama ta koda yake Allah ba bawan sa da baya jarabta babba ko karami mace ko namiji, ni na san ina cikin jarrabawan ubangiji nane, yau na dawo daga asibiti wanda tashin hankali yaja min kwanciya can kuma gashi yanzu ga wata fitinan da kwanciya asibitin ma ba zai min maganin ta ba. Ina ji Inna ta shigo tana min magana nayi likimo kaman mai bacci saboda bana son ta tambaye ni waye yazo, jin wanene ko meya zo dashi babu abinda zai kara mata illah tashin hankali. Addu'oin bacci tayi ta shafa nima ta shafa min ta kwanta a gefe na taja mana bargo ba tafi 15 mins da kwanciya ba naji tayi bacci, a zuciya ta nace Allah sarki Inna ta dana fad'a miki halin da nake ciki yanzu na tabbata da baki samu daman runtsawa ba. Har karfe d'ayan dare tayi ido na babu alamun bacci, cikin tsand'a na sauka daga kan gadon na fita na d'auro alwala na fara kai kuka na ga Rabbil Izzatti shine kad'ai madogara na. **************** Zafar har ya isa gida zuciyar shi bai bar tafasa ba har kaman shi wannan yarinyan zata dubi cikin idon shi ta fad'a mishi abinda taga dama " bull shit" yace yana dukan stairin shi da karfi kaman shi ya mishi lafin. Yana zuwa gida kai tsaye part d'in iyayen shi ya wuce, a kofan parlour ya tsaya ya gyara fuskan shi kaman he is in good mood saboda baya so su fahimci halin da yake ciki. Da sallama ya shiga parlour suna zaune suna kallon wa'azi a Sunna TV da Sheikh Aminu Daurawa da yake , amsa mishi sukayi duka ya karaso ya zauna kan lallausan rug dake parlour ya gaishe su suka amsa mishi cikin kulawa daga nan yaja bakin shi yayi shiru shima ya maida hankalin shi kan wa'azin. Kusan mint 10 wa'azin ya kare dama yazo karshe , remote Abban shi ya d'auka ya rage volume d'in TV sannan ya kalli inda Zafar yake zaune yace; "Ina ta zuba ido ka kawo min wacce kake so kaman yanda mukayi magana tun kwanaki 3 da suka wuce amma na jika shiru, so yau ne deadline d'in kuma dole ne in cika alkawari na dana d'auka na samo maka mata a cikin 'ya'yan dangi". "Kayi min afuwa Abba yanzu haka abinda nazo fad'a maka kenan na tarar kuna kallon wa'azi shiyasa na jira ku gama sai muyi magana" ya amsa yana wani sussunne kai. "Okay sai yau kaga dama kazo min da zancen?? Hmm toh bakin alkalami ya bushe gobe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99