Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

kasa zama sai neman hanyar da zata dakatar dasu take amma kasan zuciyar ta kuwa gargad'i take mata na kar ta tsauwala har ta tonawa kanta asiri cikin mutane, da wannan shawaran ta nemi waje ta zauna sai karkad'a kafa take tana sharce gumi,Hajara tana ankare da ita amma taki tanka mata. Ni kuwa tunda naji Baba yace ginin zamani za'a yiwa gidan mu na kasa ko daga yatsa na sannan kuma na tabbatar da zancen bawan Allah nan na jiya gaskiya ne kenan in ba haka ba ina Baba yaga kud'in ginin zamani, "Ya Allah ka dube ni ka fidda ni cikin wannan fitinan" nace cikin raina. Basuyi wani nisa ba suka fara tono tsirkullen Gwaggo Aisha, cikin mamaki suka tsaya cirko-cirko suna kare musu kallo an rasa mai magana cikin su. "Mu cigaba da aikin mu mana" cewar d'aya daga cikin su. "Kaman yaya mu cigaba bayan wannan abubuwa da muka tono,kamata yayi a sanarwa mai gidan sai ya san matakin da zai d'auka" nan duk sukayi na'am da shawaran nan suka tura karamin cikin su kiran Baba. "Innalillahi wa inna ilahi rajiun" shine Kalmar da Inna ta samu daman maimaitawa fitowar ta kenan daga bayan gida taga sun tara tsirkullen a gefe suna ta tattaunawa akai. Kasa wucewa tayi tana mamakin me ya kawo layu da guraye kofan kitchen d'in ta, fargaba fal a zuciyar ta na kada ace itace ta binne su,har Baba iso wajan tana tsaye sai ambaton sunan Allah take. "Wannan ai ba wani abin tada hankali bane, ta yiwu tun na kakanin mune sune zasu iya ajiye irin wayan nan abubuwan su jima haka kasa haka" cewar Baba kenan cikin rashin d'aukan abin da muhimanci. "A'a wayanan tsurkullen basu dad'e a kasa ba ta, da gani kwananan aka binne su" cewar d'aya daga cikin su. "Matsalaha daya ne shine a k'ona su kurmus in ma mai shi da wata manufa ya binne toh zai zo da sauki" Inna da jikin ta yayi sanyi sosai barin ma irin kallon tuhuma da taga Baba na aiko mata da shi yasa duk taji ba dad'i, tana jin anyi maganan konawa yasa cikin sauri ta wuce d'aki ta d'auko ashana a cikin drowern d'aki inda take ajiyewa in ta sayo kwali. Kamin ta fito har sun tara su a gefe sun zuba kalanzir suna neman ashana, Baban mu ta mikawa ta koma gefe ta tsaya babu b'ata lokaci wanda ya karba ya ketta ashana bayan yayi addu'oi nan da nan kuwa wuta ya kama ya fara ci bakin hayaki na tashi a jiki kaman ana kona taya. A d'akin Gwaggo Aisha kuwa tunda aka cinnawa layun nata wuta ta fara ganin d'akin na juya mata ga wani zafi-zafi da take ji a jikin ta kaman ana hura mata wuta, tun tana iya daurewa har abin yafi karfin ta ta fara ihu tana birgima a tsakiyar d'aki. Sharewa nayi kaman banji ba dan nima ina fama da nawa matsololin inda zan samu daman ihun nima da nayi ko zanji sauki cikin raina. Tsaki naja ina mikewa tsaye da d'an sauran kuzarin daya rage min na fita saboda yanda naji ihun yaki tsayawa kuma kana ji kasan wanda yake yana cikin mamuyacin hali. Kus-kus na tarar masu aikin nayi ban kula su ba nayi wucewa ta zuwa d'akin Gwaggo Aisha da zan iya kirga shiga ta ciki tunda aka haife ni. Da gudu na karasa nima ina kokarin rike ta kaman yanda naga Inna da Hajara sukayi Inna sai tofa mata addu'oi take, ban tsaya b'ata lokaci ba nima na fara taya ta muka cigaba da tofa mata har ta daina birgima sai jikin ta da yake rawa sosai, tuni Baban mu ya fice abin shi zuwa d'akin shi ya bar mu da ita. Mun Kai good 30 mins muna yi mata sannan ta dawo hayyacin ta sai ajiyan zuciya take a kai- akai hawaye na bin gefen fuskan ta amma koda wasa bata bud'e ido ba, ganin taji sauki yasa Inna mikewa tacewa Hajara ta lullub'a mata abin rufuwa da alamu ta samu bacci, amsawa tayi da toh tare da mana godiya muka fito zuwa d'akin mu Inna bata zauna ba ta d'auki dubu d'aya ta bawa Ibrahim kan ya sayo mana abin karyawa a waje. Tunda ta bada sakon ta dawo d'aki ta zauna shiru na san shirun nata baya rasa nasaba da abinda ya faru a safiyar yau, ba Inna da take shekaru ba ko ni nan na fahimci abinda ya faru da Kuma musababbin ta. Allah sarki Inna ta kamin ka samu mai irin zuciyar ta a wannan zamnin sai an tona, tsab ta gane komai amma taje tayi mata addu'a, da wata ce sai dai ta mutu ko nice nan Yasin ko kurar da ya debo ki ba zan kallah balle har in nema miki waraka barin ki zanyi ki girbi abinda kika shuka. Shi kuwa Baban mu akwai shi da kyaluwa ba kasafai kake gane mishi ba in ba harkan kud'i bane, ko ya fahinmci abinda ya faru ko bai fahimta ba oho. ************* A b'angaren Zafar kuma yau cikin farinciki ya tashi ko ba komai ya ragewa kan shi tention da kuma fad'an Abban shi, ba komai yake kara mishi nishad'i ba kaman in ya tuno da hiran shi da Abban shi jiya a kaina. Murmushi ya kara saki lokacin da ya tuna Abba shi yace" ina matukar alfahari da kai ka birge ni sosai da ka tashi neman aure baka nema cikin 'ya'yan masu kud'i ba ka nema a irin gidan da nake son in samu sirka, Naji dad'i da baka bi halin mahaifiyar ka ba na wajan kin talaka, da mai kud'i da talaka duka Allah ne yayi mu saboda hikimomin shi ba yayi hakan bane dan baya son su ba. Ina son ka auna da kanka ka gani a nan ne zaka gane hikiman ubangiji da nake fad'a maka, misali ace duniyan gaba d'aya babu talaka ya kake ganin zai kasance ko kuma ace duka talakawa ne babu mai kud'i, ka fahimta?" Ya tambaya yana kallon yanda ya natsu yana sauraron shi. Gyad'a kai Zafar yayi a hankali kan shi a kasa da sai yanzu da Abba ya fad'a mishi ya gane dole talaka yana bukatan mai kud'i haka Kuma mai kud'i yana bukatan talaka a rayuwar shi. Muryan Abba yaji ya cigaba da magana " babu wanda yafi wani sai wanda ya mutu ya samu aljanna, kana nan duniya kana taka mutum saboda kai kana da shi shi kuma talaka baka sani ba kila a wajan Allah yafi ka daraja, dan haka ka cigaba da rike mutane da kyakkyawan zuciya zaka ga amfanin haka duniya da kiyama". Shi dai Zafar duk mamaki ya hana shi sakat yaushe rabon da su zauna da Abban shi har suyi magana mai tsayi cikin lumana haka, tun kafin zuwan sa abroad karatu, tunda ya dawo da sabbin halayen sa na shan minti kuwa suka daina shan inuwa d'aya tare. "Kana da kud'i a account d'inka?" Ya karajin muryan Abba ya katse mishi zancen zuci yake. "Eh akwai Abba ba za'a rasa ba" ya amsa a sanyaye kaman mutumin kirki. "Ok bari zuwa anjima ko gobe zanyi maka transfer ko kad'an ne kada

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99