Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Ba Sonta Nake Ba Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

zuba santi,sai da nayi nak sannan na tattara sauran na kai kitchen ban gan shi a parlorn ba ban kuma bi ta kan shi ba nazo na cigaba da charting na. ****************** Washe garin ranan da suka dawo daga wajan boka Gwaggo Aisha tasa Hajara wanka da sassafe ta shirya wai ta taho gida na su fara aiwatar da kudurin su tunda wuri, bata musa mata ba ta shirya tsab tayi kwalliyar ta cikin doguwar rigar ta na atampa daya amshe ta sosai,tana bari tayi breakfast kamin ta fita amma ta hana ta tace in azo nan gidana taci. Haka ta fito wajan 8 da wani abu ba tayi nisa da gidan namu ba ta samu kwata ta jefa maganin a ciki tayi wucewar ta, bata son zuwa gidan da sassafe haka ta san duk yanda akayi kila ko farkawa daga bacci bamuyi ba, tunda ta shigo anguwan da nake ta fara jan kafa dan bata san kowa a anguwan ba da ta shiga ta dan ja lokaci har sai Zafar din ya fita kamin ta shigo. Dole haka ta karaso kofar gidan tayi knocking mai gadi yazo ya bud'e mata kofan ta shigo daga ciki sannan ta gaishe shi cikin girmamawa da yake ya dan manyan ta, amsa mata yayi cikin kulawa kasancewar yaji dad'in yanda ta gaida shin. "Dan Allah Baba masu gidan sun tashi kuwa?" Ta tambaya shi lokacin yana shirin komawa dakin shi. "Gaskiya bana jin sun tashi dan sai kusan goma sannan muke kin motsin farkawan su" ya amsa mata. " Toh dan Allah zan zauna a nan kamin su farka" tace tana nuna mishi wasu kujerun roba da suke can gefe cikin furanni. "Toh toh shikenan ki zauna sai sun fito" yace yana shigewa dakin shi, karasawa tayi ga kujerun ta zauna tana ajiyar zuciya samun relief ta ciro wayar ta daga cikin jaka ta fara game dan ya rage mata zaman kad'aici, ya ko taimaka matan dan bata san lokacin da taja a wajan zaune ba hankalin ta duk yana kan wayan taji saukan ruwa kaman daga sama a jiki ta, a firgice ta mike tana " innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" a masifance ta juyo da niyyan ciwa wanda yayi mata wannan danyen aikin mutunci sai dai tana jiyowa idanun su suka sarke dana juna shima ya taho da niyyan bata hakuri saboda sam bai kula cewa da mutum a zaune a wajan ba domin kullum yazo haka zaiyi aikin shi ya koma ba tare da yaga wani na gidan ba gwara shi Zafar din sukan had'u wasu lokutan. Da kyar ya samu bakin bata hakuri cikin sanyin muryan shi da ya zame masa jiki, sai a lokacin Hajaran ta dawo hayyacin ta ta janye idon ta akan shi a kunyace tare da ce mishi babu komai. Ajiye tiwon hannun shi da yake bawa flowers ruwa dashi yayi cikin sauri ya koma can inda ya ajiye kayan shi wajan Baba mai gadi ya d'auko wani babban handkie ya dawo duk tana tsaye tana bin shi da ido yazo ya goge mata ruwan da ya jika kujera da take kai sannan ya dube ta wannan karon fuskar shi d'auke da murmushi yace " ki zauna Hajiya kiyi hakuri wallahi ban lura da mutum a wajan bane d z an kullum Ina zuwa aiki ban tab'a cin karo da wani a nan zaune ba shiyasa". Zama tayi a hankali itama fuskar ta d'auke da murmushin tace " kada ka damu na san ba da gangan kayi ba, nima na zauna a nan ne kamin masu gidan su farka daga bacci, ba matsala ka cigaba da aikin ka nagode". " Toh Hajiya nima nagode" yace yana komawa kan aikin shi sai dai tunda ya fara hankalin shi gaba daya yana kan ta haka itama ta kasa natsuwa hankalin ta kacokan yana kan shi sai kallon shi take ta kasan ido dan ba laifi shima kyakkyawa ne gashi da hasken sa dan yafi ta haske sosai. Suna had'a ido sai su sakarwa juna murmushi a haka har ya kammala aikin shi ya dawo wajan ta yana ko ya taya ta zama ne tunda har yanzu da sauran lokaci, bata musa ba ta bashi dama ya zauna sai gashi suna hira kaman sun dad'e da sanin juna kamin Zafar ya fita har sunyi exchange na phone number tsakanin su. Zafar ya fito zuwa gaishe da iyayen shi kaman yanda ya saba ya shiga mota ya wuce su sun ga fitowan shi Amma shi sam hankalin shi bai Kai kan su ba yaja motan shi ya fita bayan mai gadi ya bud'e mishi gate. Koda Zafar ya fita sai da suka kara kusan minti 20 tare kamin su rabu ta samu daman shigowa cikin gidan a lokacin ni kuma na gama breakfast nazo nayi kwanciya ta naji salkamar ta, cikin ihun murna na fito na rungume ta zan iya cewa bayan yinin bakwai da akayi sai yau wani nawa yazo min dan haka cike da farincikin na tarbe ta ina tambayan ta Inna ta da mutanen gida tace min duk suna lafiya. Bayan gama gaishe-gaishe na gabatar mata da sauran abincin da na rage ta fara ci muna hira cikin tsananin farincikin da kewar juna. Shi kuwa Zafar tunda ya tafi gidan su hankalin shi na kaina dan ya kasa sakin jiki suyi hira kaman yanda suka saba, bini-bini sai kallon agogo yake har Abban shi ya gano shi yace" ya kamata ka tashi ka koma gida son dan my daughter tana bukatan kulawar ka musamman a halin da take ciki yanzu". "Wani hali take ciki kuma?" Mom da tundazu taki saka baki a hiran nasu ta tambaya a d'an rikice. "Ke kuwa ai zaki fimu sanin halin da take ciki tunda ke macece, yau ta tashi bata da lafiya wai tana fama da jiri da ciwon kai kinga alamun ciki sun bayyana a tare da ita amma fa a nawa hasasshen kenan ko kunje asibiti?" Abba ya amsa mata da wadatattacen murmushi saman fuskar shi yana kallon Zafar daya duke kai shima yana murmushin tare da girgizawa Abba kan shi. "Ja'iri ji wani murmushi dan Allah Hajiya yaran yanzu da shegen son 'ya'ya suke" ya karasa yana dungure mishi Kai. Mom da tayi suman zaune ko jin abinda yake fad'a ba tayi ba har yayi musu sallama ya fita ya bar ta baki bud'e. Anan Kuma nida 'yar uwata sai hira muke zubawa yanda tun daga kofar shigowa zaka ji hayaniyar mu ba dan komai ba sai na labarin sabon saurayi da tayi na gidan mu take tana yayi mata amma tana gudun kada yaji ta tab'a aure da haihuwa ya guje ta... Ni kuwa ina kara karfafa mata giwan cewa babu wanda zai kalle ta yace ta tab'a aure balle har ace ta haihu, muna cikin haka Zafar ya dawo gidan jiki a sanyaye amma tunda ya fara jiyo murya ta cike da nishadi muna hira yasa ya shigo da karfin shi, sallama yayi ya tsaya daga bakin kofa fuskar shi d'auke da tsantsan farincikin samu na a haka da yayi, bude min hannuwa yayi alamun inzo gare shi har zan watsa masa harara na tuna cewa ashe fa in a gaban mutane ne drama muke

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99