Chapter 8
Chapter 8
sauri na fito ina goge gumin jikina,kallon tausayi tabi ni dashi ta san Allah bai bata haihuwa dayawa ba amma alhamdullilahi tana alfahari dani domin jumm'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake gane ta. Na zata zatayi min fad'a ko ta ce wani abu akai amma naji tayi shiru bata ce komai ba sai tagumi data zuba tana yawan ajiyan zuciya,da taga zaman ba zaiyi mata ba ta mik'e ta saka hijabi tare da yi min gargad'in kada in fita koda k'ofar d'aki ne kuma kar in kula kowa duk abinda zasu ce min. Bata jira amsa ta ba ta fita daga gidan zuwa gidan su wato gidan kakanni na da muke makotaka dasu,da sallama ta shiga. Kakata Ya Jalo da suke kira da Maa tana soya gyad'a na sayarwa ta amsa tana mata sannu da zuwa,bata gama suyar ba ta sauke gyad'an ta taso sanin cewa in taga kafar Inna ta a gida da dalili ne ya kawo ta duk da kasancewar muna makota basu bata daman zuwa gida any how ba. "Bintu komai da kike gani na duniya mai wucewa ne sannan kowa yayi hakuri zai ga riba a gaba dan haka bana son kina sawa kan ki damuwa ko kad'an ki cigaba da hakuri wata rana sai labari" cewar kaka ta kenan ganin damuwa karara a fuskan Inna ta,dama haka take mata kullum koda tazo da damuwar ta bata bari ta fad'a sai dai tayi mata nasiha tare da kwantar mata da hankali ta koma gida. "Nagode Maa Allah ya kara girma amma ba matsalan gida ne ya kawo ni ba akan Zareefa ne...." nan ta kwashe labarin Abdulbasit tun farko har zuwa yau da yazo ya tafi. Shiru kaka tayi tana tunani kaman na second 20 can ta d'ago ta ce," a yanda na fahimci maganan nan yaron nan bashi da aibu da gasken sa taimakon yake yi in da bashi da gaskiya a yanda kika ce yana da kud'i nan ba zai tsaya yi miki wannan dogon bayanin ba balle ya gaya miki asalin sa,in kuma da yana da niyyan cutar da ita da tuni ya cutar da ita dan haka ki kwantar da hankalin ki Allah ne ya dubi zuciyar ki ya kawo wanda zai taimake ku ke da 'yar ki cikin ruwan sanyi". Cike da gamsuwa maganan mahaifiyarta ta ciro kud'in ta bawa Maa dubu uku a ciki amma taki karb'a ta ce," ki bar shi ki had'a dana wajan naki ki saka Zareefa makarantan gaba kaman yanda kika ce". "Maa akwai saura ai zasu isa ki karb'i wannan d'in ki saka albarka" cewar Inna kenan. Dubu 1 kawai ta zara a ciki ta mayar mata da sauran tare da cewa," Allah ya sanya albarka". Sun d'an tab'a hira kad'an sannan tayi mata sallama zuciyar ta fari kal ta dawo gida. D'ari biyar ta cire ta bani a cikin kud'in tace inje in sayo naman miya harda kayan miya,cike da murna na fita a guje yau za'a dafa shinkafa a gidan mu kuma harda nama abinda ada sai sallah yake faruwa. Ina dawowa Inna ta fito ta hura wuta ta fara girki nan da nan ko k'amshin miyan ta ya cika gidan, Inna Asabe ce ta fara mita," oh in da ranka zaka sha kallo yanzu fisabillilahi wannan abinci da aka samu ta haramtaccen hanya shi za'a girkawa 'ya'yan mu su shi?" Ta karasa maganan tana kallon gwaggo Aisha ko zata ce wani abu. "Hmmm ni yara na ba zasu ci ba dama kowa ya san ni ba irin ku bace ina da abinda zasu ci nan wata ko 3 ne koda ace bana sana'a dan haka ku kuka sani" Gwaggo Aisha ta fad'i haka tana yiwa karamar 'yar ta da muke sa'anni da juna kitso wato Jameela. "Ke kuwa daga magana sai ki wani dawo kaina kina wani cika baki,meye naki bamu sani ba wallahi mun san inda Hajara take zuwa tallah da abinda yake tafiya wallahi duk mun sani, a toh kada a cika mana baki kuma ba'a karya kusa da gida" Inna Asabe take mayarwa Gwaggo Aisha magana cikin fushi dan taji haushin maganan da ta yab'a mata. Nan fa fad'a ya kaure ba abinda kake ji sai ifacce-ifaccen su suna zagin juna tare da tonon asiri kala-kala, sai Maman Dije ce da ta gaji da hayaniyar tasu tazo ta shiga tsakanin su sukayi shiru. Inna ta dai tana gefe tana aikin ta ko inda suke bata kalla balle tayi gigin raba su domin ta sha gwadawa a baya sai fad'an ya dawo kan ta data fahimce su sai ta kama kanta ta koma gefe ta zama 'yar kallo. Ana kiran sallah magariba Inna ta gama girkin ta duk da taji sun ce ba zasu ci ba amma haka ta nemo kwanukan kowa ta zuzzuba musu ta bani na kaiwa ko wacce d'akin ta suka bini da zagi da tsinuwa kuma wai inzo in d'auke tsiyar mu amma nayi musu kunnen uwar shegu domin Inna taja kunne na kan ina ajiye musu in juya in basa ci su bawa almajirai amma ni kar in d'auko. Sai bayan sallah isha'i Baban mu ya shigo dama ko girkin Inna tane baya shigowa d'akin mu bare yaci abincin mu dan haka Inna tana jin muryan shi tace in d'auki abincin shi in kai mishi. "Na'am" na cewa Inna ba tare da na shirya ba jin tace wai in kaiwa Baba abinci,sai naji abin wani banbara kwai. "Ki kaiwa babanku abincin shi nace" ta kara maimaita min,amsawa nayi na d'auki tiren abincin da Inna ta d'aura kwanon tuwo daban miya ma daba sai kofin silver mai murfi da ta zuba ruwan randa mai sanyi. A tsorace na nufi d'akin nashi ina jan k'afa dan na san karamin aikin shine ya koro ni da abincin,ba yanda na iya haka na karasa bakin k'ofan d'akin cikin rawan murya nayi sallama,da yake tsanan da yake min bana wasa bane nan da nan ya gane murya ta cikin tsawa ya ce," uwar me kike nema a nan?" "Inna tace ta ce in kawo abinci" na bashi amsa cike da fargaba. "Ita Bintu dan yau ta haukace shine zata aiko ki kawo min jagwalgwalo,kafin in kirga uku ki bar nan ko kuma in na tashi wallahi...." Ai ban bari ya karasa ba na jiyo cikin sauri Allah ya taimake ni babu kowa a tsakar gidan dan haka babu wanda ya ganni na shige d'akin mu. Inna murmushi tayi ganin na dawo da abincin ta ce," koro ki yayi ko?" Gyad'a mata kai kawai nayi bata kara cewa komai ba ta sauke min tiren akaina ta zuba mana namu muka fara ci abin mu. Saida naji ciki na barazan fashewa sannan na hakura da tura shinkafa da jan miyan da nake na kwashe kwanukan na fitar sai ga sauran yaran ma suna fitowa da nasu kwanukan suna ta tsid'e hannu su da iyayen su suka ce ba zasu ci ba. Ina dariya na koma d'aki nake bawa Inna ta labari ta kwab'e ni kan bata son surutu in nemi waje in kwanta,ba musu kuwa na kwanta kan shimfid'a ta cikin abinda bai kai minti biyar ba bacci yayi gaba dani. Da washe gari da sassafe Innata da ta tashi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99